Lamentações 4
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Zinariya ta rasa kyanta,
hasken zinariya ya dushe!
An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu
masu daraja a kan tituna.
2Dubi samarin Sihiyona masu daraja,
waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya,
yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa,
aikin maginin tukwane!
3Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha,
amma mutanena sun zama marasa zuciya
kamar jiminai a cikin jeji.
4Domin ƙishirwa
harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu;
yaran suna roƙo a ba su burodi,
amma ba wanda ya ba su.
5Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗi
yanzu su ne masu bara a tituna.
Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyau
yanzu suna kwance a kan tarin toka.
6Horon mutanena
ya fi na Sodom girma,
wadda aka hallaka farat ɗaya
ba wani hannu da ya juya ya taimake ta.
7’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske
sun kuma fi madara fari,
jikunansu sun fi murjani ja,
kyansu kamar shuɗin yakutu.
8Amma yanzu sun fi dare duhu;
ba a iya gane su a tituna.
Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu;
sun bushe kamar itace.
9Gara waɗanda aka kashe su da takobi
da waɗanda suke mutuwa da yunwa;
sun rame domin rashin abinci a gona.
10Da hannuwansu mata masu tausayi
sun dafa yaransu,
suka zama masu abinci
sa’ad da aka hallaka mutanena.
11Ubangiji ya saki fushinsa;
ya zuba zafin fushinsa.
Ya hura wuta a Sihiyona
ta kuma cinye harsashin gininta.
12Sarakunan duniya ba su gaskata ba,
haka ma mutanen duniya,
cewa magabta da maƙiya
za su iya shiga ƙofofin Urushalima.
13Amma ya faru domin zunuban annabawanta
da muguntar firistocinta,
waɗanda suka zub
da jinin masu adalci a cikinsu.
14Yanzu suna yawo barkatai a tituna
kamar makafi.
Sun ƙazantu da jini
yadda ba wanda zai kuskura ya taɓa rigunansu.
15“Ku tafi! Ba ku da tsabta!” Haka mutane suke ihu suke ce musu.
“Ku tashi daga nan! Ku tashi daga nan! Kada ku taɓa mu!”
Sa’ad da suka gudu suna yawo,
mutanen waɗansu ƙasashe suka ce,
“Ba za su ci gaba da zama a nan ba.”
16Ubangiji kansa ya warwatsa su;
ya daina duban su.
Ba a ba firistoci girma,
ba su ba dattawa gata.
17Idanunmu sun gaji,
suna ta dubawa ko taimako zai zo;
mu sa ido ko za mu ga
ƙasar da za tă iya taimakon mu.
18Ana bin sawunmu,
ba za mu iya tafiya kan tituna ba.
Ƙarshenmu ya kusa, kwanakinmu sun ƙare,
gama ƙarshenmu ya zo.
19Masu fafarar mu sun fi gaggafa
mai firiya a sararin sama sauri;
sun fafare mu a kan duwatsu
suna fakon mu a jeji.
20Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu,
ya fāɗi cikin tarkonsu.
Muna tunani cewa za mu iya rayuwa
cikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa.
21Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom,
ke mai zama a ƙasar Uz.
Amma ke ma za a ba ki kwaf;
za ki bugu ki zama tsirara.
22Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare;
ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba.
Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki
yă tona tsiraicinki.

Você sabia?
A Agonia da Cidade Caída
- O poeta considera o sofrimento prolongado de Jerusalém pior do que o destino de Sodoma. Enquanto Sodoma foi destruída em um instante por fogo divino, os habitantes de Jerusalém suportaram o tormento lento e doloroso do cerco e da fome.Fontes: o próprio texto bíblico · Sodom
- Antes de sua queda, Jerusalém era amplamente vista como uma cidade montanhosa impenetrável. O texto observa que os reis estrangeiros e as nações vizinhas nunca imaginaram que um inimigo pudesse romper seus portões fortificados.Fontes: o próprio texto bíblico · Jerusalem
- O capítulo se encerra com uma mensagem dirigida a Edom, que habitava na terra de Uz, advertindo que o juízo logo a alcançaria. A terra de Uz é mencionada em apenas três livros bíblicos: Jó, Jeremias e Lamentações.Fontes: o próprio texto bíblico · Uz · Edom
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Zion · Hoje: Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 2, 11, 22
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 12
- Edom · 30.746, 35.604 · versículos 21, 22
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org