Jeremias 49
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Saƙo game da Ammon
1Game da Ammonawa.
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Isra’ila ba shi da ’ya’ya maza ne?
Ba shi da magāda ne?
To, me ya sa Molek ya mallaki Gad?
Me ya sa mutanensa suka zama a garuruwansa?
2Amma kwanaki suna zuwa,”
in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan yi kirarin yaƙi
a kan Rabba ta Ammonawa;
zai zama tarin juji,
za a sa wuta a ƙauyukan da suke kewayenta.
Sa’an nan Isra’ila zai kori
waɗanda suka kore shi,”
in ji Ubangiji.
3“Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai!
Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba!
Ku sa tufafin makoki;
ku ruga nan da can a cikin katanga,
gama Molek zai tafi bauta,
tare da firistocinsa da kuma fadawansa.
4Me ya sa kuke taƙama da kwarurukanku,
taƙama da kwarurukanku masu amfani?
Ya ke diya marar aminci,
kin dogara a wadatarki kika kuma ce,
‘Wa zai iya fāɗa mini?’
5Zan kawo razana a kanki
daga waɗanda suke kewaye da ke,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Za a kore kowannenku,
babu wani da zai tattara masu gudun hijira.
6“Duk da haka, daga baya, zan maido da wadatar Ammonawa,”
in ji Ubangiji.
Saƙo game da Edom
7Game da Edom.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Babu sauran hikima a Teman ne?
Shawara ta ɓace daga masu basira ne?
Hikimarsu ta ruɓe ne?
8Ku juya ku gudu, ku ɓuya a cikin kogwanni masu zurfi,
ku da kuke zama a Dedan,
gama zan kawo masifa a kan Isuwa
a lokacin da zan hukunta shi.
9In masu tsinkar ’ya’yan inabi suka zo maka,
ba za su rage ’ya’yan inabi kaɗan ba?
In ɓarayi suka zo da dare,
ba za su sata abin da kawai suke bukata ba?
10Amma zan washe Isuwa sarai;
zan bubbuɗe wuraren ɓuyarsa,
don kada yă ɓoye kansa.
’Ya’yansa, danginsa da maƙwabtansa za su hallaka,
ba kuwa zai ƙara kasancewa ba.
11Ka bar marayunka; zan tsare ransu.
Gwaurayenka kuma za su dogara a gare ni.”
12Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In waɗanda ba su dace su sha kwaf ɗin ba suka sha shi, me ya sa za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, sai ka sha shi. 13Na rantse da kaina,” in ji Ubangiji, “cewa Bozra za tă zama kufai da kuma abin tsoro, abin dariya da abin la’ana; kuma dukan garuruwanta za su kasance kufai har abada.”
14Na ji saƙo daga Ubangiji cewa;
an aiki jakada zuwa ga al’ummai ya ce,
“Ku tattara kanku don ku fāɗa mata!
Ku tashi don yaƙi!”
15“Yanzu zan mai da kai ƙanƙani a cikin al’ummai
abin reni a cikin mutane.
16Tsoron da ka sa ake ji
da kuma girman kan zuciyarka ya ruɗe ka,
kai da kake zama a kogon dutse,
kai da kake kan tudu.
Ko da yake ka gina wa kanka sheƙa can bisa kamar na gaggafa,
daga can zan sauko da kai ƙasa,”
in ji Ubangiji.
17“Edom za tă zama abin tsoro;
dukan wanda ya wuce zai giggice ya yi tsaki
saboda dukan mikinta.
18Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra,
tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,”
in ji Ubangiji,
“haka ba wanda zai zauna a can;
ba wani da zai zauna a cikinta.
19“Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun
zuwa wurin kiwo mai kyau,
zan kori Edom daga ƙasarta nan da nan.
Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa don wannan?
Wane ne yake kama da ni kuma wa zai kalubalance ni?
Kuma wane makiyayi ne zai yi gāba da ni?”
20Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Edom,
abin da ya nufa wa waɗanda suke zama a Teman.
Za a ja ƙanana na garken tumaki a tafi;
zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su.
21Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza;
za a kuma ji muryar kukansu a Jan Teku.
22Duba! Gaggafa tana firiya tana kuma saukowa,
tana buɗe fikafikanta a bisa Bozra.
A wannan rana zukatan jarumawan Edom
za su zama kamar macen da take naƙuda.
Saƙo game da Damaskus
23Game da Damaskus.
“Hamat da Arfad sun giggice,
gama sun ji mummunar labari.
Suna damuwa,
sun damu kamar tekun da baya hutu.
24Damaskus ta karai
ta juya don ta gudu
tsoro kuma ya kama ta;
wahala da zafi sun kama ta,
zafi kamar na mace mai naƙuda.
25Me ya sa ba a tafi aka bar sanannen birnin nan ba,
birnin da nake jin daɗi?
26Tabbatacce, samarinta za su fāɗi a tituna;
dukan sojojinta za su yi shiru a wannan rana,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
27“Zan cinna wa katangar Damaskus wuta;
za tă ci kagaran Ben-Hadad.”
Saƙo game da Kedar da Hazor
28Game da Kedar da mulkokin Hazor, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fāɗa wa.
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Tashi, ku fāɗa wa Kedar
ku kuma hallaka mutanen Gabas.
29Za a ƙwace tentunansu da garkunansu;
za a tafi da mafakanta
tare da dukan kayayyakinsu da raƙumansu.
Mutane za su yi musu ihu,
‘Razana ko’ina!’
30“Ku yi maza ku gudu!
Ku zauna a kogo masu zurfi, ku da kuke zama a Hazor,”
in ji Ubangiji.
“Nebukadnezzar sarkin Babilon ya shirya muku maƙarƙashiya;
ya ƙulla maƙarƙashiya a kanku.
31“Ku tashi ku kuma fāɗa wa al’umma da sauƙi
wadda take zama da ƙarfin hali,”
in ji Ubangiji,
“al’ummar da ba ta da ƙofofi ko ƙyamare;
mutanenta suna zama su kaɗai.
32Za a washe raƙumansu,
garkunansu mai girma za su zama ganima.
Zan watsar da waɗanda suke a wurare masu nesa a ko’ina
zan kuma kawo musu masifa a kowane gefe,”
in ji Ubangiji.
33“Hazor za tă zama mazaunin diloli,
kufai har abada.
Ba wanda zai zauna a can;
ba wanda zai zauna a cikinta.”
Saƙo game da Elam
34Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Elam, a farkon mulkin Zedekiya sarkin Yahuda.
35Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Ga shi, zan karye ƙarfin Elam,
zaunannen ƙarfinsu.
36Zan kawo a kan Elam a kusurwoyi huɗu
daga kusurwoyi huɗu na duniya;
zan watsar da su zuwa kusurwoyi huɗu,
kuma ba al’ummar
da masu gudun hijirar Elam ba za su kai ba.
37Zan ragargaza Elam a gaban maƙiyansu,
a gaban waɗanda suke neman ransu;
zan kawo masifa a kansu,
da zafin fushina,”
in ji Ubangiji.
“Zan runtume su da takobi
sai na kawo ƙarshensu.
38Zan sa kursiyina a Elam
in kuma hallaka sarkinta da fadawanta,”
in ji Ubangiji.
39“Duk da haka zan maido da wadatar Elam
a kwanaki masu zuwa,”
in ji Ubangiji.

Você sabia?
Julgamentos sobre as Nações Vizinhas
- Jeremias repreende os amonitas por ocuparem o território a leste do rio Jordão que havia sido concedido à tribo de Gade. Sua principal cidade, Rabá, é advertida sobre a destruição e o exílio de sua divindade Milcom e de seus líderes.Fontes: o próprio texto bíblico · Gad · Rabbah
- A profecia contra Edom reflete sua geografia montanhosa e escarpada, onde os habitantes erguiam fortalezas nas fendas das rochas. Ela também menciona Temã, um distrito ao sul famoso pela reputada sabedoria de seu povo.Fontes: o próprio texto bíblico · Edom · Teman
- Quedar refere-se a tribos árabes nômades que viviam em tendas e se deslocavam pelo deserto com seus camelos e rebanhos. O capítulo prediz o saque e a derrota dessas tribos pelo rei babilônio Nabucodonosor.Fontes: o próprio texto bíblico · Kedar · Nebuchadnezzar
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Ammon · 31.955, 35.934 · versículos 1, 2, 3, 4, 6
- Rabbah · Hoje: Amman · 31.955, 35.934 · versículos 2, 3
- Edom · 30.746, 35.604 · versículos 7, 8, 10, 14, 15, 17, 18, 19, 20, 21, 22
- Jordan · Hoje: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículo 19
- Red Sea · Hoje: Gulf of Aqaba · 28.750, 34.750 · versículo 21
- Damascus · 33.511, 36.306 · versículos 23, 24, 27
- Hamath · Hoje: Hama · 35.136, 36.750 · versículo 23
- Babylon · 32.543, 44.422 · versículos 28, 30, 31
- East · Hoje: region around Amman · 31.955, 35.934 · versículo 28
- Kedar · 29.811, 39.868 · versículo 28
- Elam · 32.189, 48.258 · versículos 34, 35, 36, 37, 38, 39
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org