Jeremias 23
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Reshen adalci
1“Kaiton makiyayan da suka hallakar suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji. 2Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana ce wa makiyayan da suke lura da mutanena, “Domin kun watsar da garkena kuka kuma kore su ba ku kuma lura da su ba, zan kawo hukunci a kanku saboda muguntar da kuka yi,” in ji Ubangiji. 3“Ni kaina zan tattara raguwar garkena daga ƙasashen da na kore su zuwa zan kuma dawo da su ga makiyayansu, inda za su yi ta haihuwa su riɓaɓɓanya. 4Zan sa makiyaya a kansu waɗanda za su lura da su, ba za su ƙara jin tsoro ko razana ba, ba kuwa waninsu da zai ɓace,” in ji Ubangiji.
5“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan tā da wa Dawuda Reshen adalci,
Sarki wanda zai yi mulki da hikima
ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar.
6A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda
Isra’ila kuma zai zauna lafiya.
Sunan da za a kira shi ke nan,
Ubangiji Adalcinmu.
7“Saboda haka fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da mutanen ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da Isra’ila daga Masar ba,’ 8amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da zuriyar Isra’ila daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashen da ya yashe su.’ Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu.”
Annabawa masu ƙarya
9Game da annabawa kuwa,
Zuciyata ta karai;
dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa.
Na zama kamar wanda ya bugu,
kamar mutumin da ruwan inabi ya sha kansa,
saboda Ubangiji
da kuma maganarsa mai tsarki.
10Ƙasar ta cika da mazinata;
saboda la’ana ƙasar ta zama kango
makiyaya a hamada ta bushe.
Annabawa suna bin mugayen muradu
suna kuma amfani da ƙarfinsu a hanyar marar kyau.
11“Annabi da firist dukansu biyu marasa sanin Allah ne;
har ma a cikin haikalina na tarar da muguntarsu,”
in ji Ubangiji.
12“Saboda haka hanyarsu za tă yi santsi;
za a jefar da su cikin duhu
a can kuwa za su fāɗi.
Zan kawo musu masifa
a shekarar da za a hukunta su,”
in ji Ubangiji.
13“A cikin annabawan Samariya
na ga wannan abin banƙyama.
Suna annabci ta wurin Ba’al
suna ɓad da mutanena Isra’ila.
14A cikin annabawan Urushalima kuma
na ga wani abin bantsoro.
Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya.
Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta,
domin kada wani ya juya daga muguntarsa.
Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni;
mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”
15Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa,
“Zan sa su ci abinci mai ɗaci
su kuma sha ruwa mai dafi,
domin daga annabawan Urushalima
rashin sani Allah ya bazu ko’ina a ƙasar.”
16Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Kada ku saurari abin da annabawan suke muku annabci;
suna cika ku da sa zuciyar ƙarya.
Suna maganar wahayi daga tunaninsu,
ba daga bakin Ubangiji ba.
17Suna cin gaba da ce wa waɗanda suka rena ni,
‘ Ubangiji ya ce za ku zauna lafiya.’
Ga duka waɗanda suke bin taurin zukatansu kuwa
sukan ce, ‘Babu lahanin da zai same ku.’
18Amma wane ne a cikinsu ya taɓa tsaya a majalisar Ubangiji
yă ga ko ya ji maganarsa?
Wa ya saurari ya kuma ji maganarsa?
19Ga shi, hadarin Ubangiji
zai taso cikin hasala
guguwa tana kaɗawa
a kan kawunan mugaye.
20Fushin Ubangiji ba zai kau ba
sai ya aikata
nufin zuciyarsa.
A kwanakin masu zuwa
za ku gane sarai.
21Ban aiki waɗannan annabawa ba,
duk da haka sun tafi da saƙonsu;
ban yi musu magana ba,
duk da haka sun yi annabci.
22Amma da a ce sun tsaya a majalisata,
da sun yi shelar maganata ga mutanena
sun kuma juyar da su daga mugayen hanyoyinsu
da kuma daga mugayen ayyukansu.
23“Ni ɗin Allah na kusa ne kawai,”
in ji Ubangiji,
“ba Allah na nesa ba?
24Akwai wanda zai iya ɓuya a lungu har da ba zan iya ganinsa ba?”
In ji Ubangiji
“Ban cika sama da ƙasa ba?”
In ji Ubangiji.
25“Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’ 26Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu? 27Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada. 28Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji. 29“Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse?
30“Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna. 31I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘ Ubangiji ne ya furta.’ 32Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.
33“Sa’ad da waɗannan mutane, ko annabi ko firist, ya tambaye ka, ‘Mece ce maganar Ubangiji?’ Ka ce musu, ‘Wace magana? Zan yashe ku, in ji Ubangiji.’ 34In annabi ko firist ko da wani dabam ya ce, ‘Wannan ne abin da Ubangiji yake cewa,’ zan hukunta wannan mutum da kuma gidansa. 35Ga abin da kowannenku yana cin gaba da ce wa abokinsa ko danginsa, ‘Mece ce amsar Ubangiji?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ 36Amma kada ku ƙara ambatar ‘maganar Ubangiji’ domin kowace maganar mutum kan zama maganarsa. Ta haka kukan lalace maganar Allah mai rai, Ubangiji Maɗaukaki, Allahnmu. 37Ga abin da za ku ci gaba da faɗa wa annabi, ‘Mece ce amsar Ubangiji gare ka?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ 38Ko da yake kuna cewa, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ga abin da Ubangiji yana cewa kuna amfani da kalmomi, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ko da yake na ce muku kada ku ce, ‘Wannan ce maganar Ubangiji.’ 39Saboda haka, tabbatacce zan manta da ku in kuma jefar da ku daga gabana tare da birnin da na ba ku da kuma kakanninku. 40Zan kawo muku madawwamiyar kunya, kunya ta har abada wadda ba za a taɓa manta ba.”

Você sabia?
Pastores, o Renovo Justo e a Verdadeira Profecia
- No mundo antigo, os governantes eram frequentemente descritos como pastores. Jeremias contrasta os líderes corruptos de Judá, que dispersaram seu povo, com a promessa de um Renovo justo da linhagem de Davi, que reinaria com sabedoria, executaria a justiça e reuniria o rebanho disperso.Fontes: o próprio texto bíblico
- O capítulo contrasta a capital do norte, Samaria, cujos profetas invocavam a divindade fenícia Baal, com os profetas de Jerusalém. Jeremias retrata as falhas morais e as falsas promessas de paz em Jerusalém como tão graves quanto a proverbial maldade de Sodoma e Gomorra.Fontes: o próprio texto bíblico
- Jeremias emprega imagens vívidas para distinguir a genuína revelação divina dos sonhos inventados. A autêntica palavra de Deus é comparada ao trigo nutritivo, ao fogo consumidor e a um martelo que despedaça a rocha, enquanto as falsas profecias são rejeitadas como simples palha.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículo 7
- Samaria · 32.276, 35.195 · versículo 13
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 14, 15, 16
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org