Isaías 8
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Assuriya kayan aikin Ubangiji
1Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz. 2Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.”
3Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz. 4Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”
5Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,
6“Domin wannan jama’a ta ƙi
natsattsen ruwan rafin Shilowa
suka yi ta farin ciki a kan Rezin
ɗan Remaliya,
7saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu
rigyawar ruwan Kogi,
wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa.
Zai cika dukan gaɓoɓinsa,
yă kuma malala har zuwa bakin kogi.
8Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta,
yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa.
Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka,
Ya Immanuwel!”
9Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro!
Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe.
Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro!
10Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba;
ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba,
gama Allah yana tare da mu.
Ji tsoron Allah
11Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce,
12“Kada ka kira wani abu makirci
game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci;
kada ji tsoron abin da suke tsoro,
kada kuma ka firgita game da shi.
13Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki,
shi ne wanda za ka ji tsoro,
shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa,
14zai kuwa kasance a wuri mai tsarki;
amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama
dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe
dutse kuma da zai sa su fāɗi.
Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama
tarko da raga.
15Yawancinsu za su yi tuntuɓe;
za su fāɗi a kuwa ragargaza su,
za a sa musu tarko a kuma kama su.”
16Ɗaura shaidar nan ta gargadi
ka kuma yimƙe umarnin Allah a cikin almajiraina.
17Zan saurari Ubangiji,
wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yaƙub.
Zan dogara gare shi.
18Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona.
19Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai? 20Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani. 21Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu. 22Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.

Você sabia?
A Inundação Iminente e o Sinal Confiável
- O nome Maer-Salal-Hás-Baz significa "o despojo se apressa; a presa se precipita". Isaías recebeu a ordem de registrar esse nome publicamente diante de testemunhas de confiança — o sacerdote Urias e Zacarias — e depois dá-lo ao seu filho recém-nascido, simbolizando o saque iminente de Damasco e Samaria pelo rei da Assíria.Fontes: o próprio texto bíblico · Maher-shalal-hash-baz · Urijah
- A passagem contrasta as águas de Siloé, que correm suavemente em Jerusalém, com as fortes correntes do rio Eufrates. Como o povo rejeitou a confiança tranquila, a imagem retrata o rei invasor da Assíria varrendo a terra como uma inundação avassaladora que chega até o pescoço.Fontes: o próprio texto bíblico · Shiloah · River · Assyria
- Isaías apresenta a si mesmo e a seus filhos como sinais e símbolos vivos concedidos pelo Senhor a Israel. Em um momento de crise nacional, ele adverte o povo a não consultar necromantes e adivinhos que murmuram, insistindo que devem recorrer a Deus e ao Seu testemunho.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Assyria · 36.359, 43.153 · versículos 4, 7
- Damascus · 33.511, 36.306 · versículo 4
- Samaria · 32.276, 35.195 · versículo 4
- Shiloah · Hoje: Pool of Siloam · 31.771, 35.235 · versículo 6
- Euphrates · Hoje: Euphrates River · 31.004, 47.442 · versículo 7
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 14
- Mount Zion · 31.772, 35.229 · versículo 18
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org