Nations Bible

Isaías 66

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

Hukunci da kuma bege

1Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Sama kursiyina ce,

duniya kuma matashin sawuna.

Ina gidan da za ku gina mini?

Ina wurin hutuna zai kasance?

2Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa,

ta haka suka kasance?”

In ji Ubangiji.

“Wannan mutum ne nake jin daɗi,

shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba,

yana kuma rawar jiki ga maganata.

3Amma duk ya miƙa hadayar bijimi

yana kama da wanda ya kashe mutum,

kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago,

kamar wanda ya karye wuyan kare;

duk wanda ya miƙa hadaya ta gari

yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade,

kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni,

kamar wanda yake bauta gunki ne.

Sun zaɓi hanyoyinsu,

rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;

4saboda haka ni ma zan aukar musu da masifa mai zafi

in kuma kawo musu abin da suke tsoro.

Gama sa’ad da na yi kira, ba wanda ya amsa,

sa’ad da na yi magana, ba wanda ya saurara,

Sun aikata mugunta a idona

suka kuma zaɓa abin da ba na jin daɗi.”

5Ku ji maganar Ubangiji,

ku da kuke rawar jiki ga maganarsa,

“’Yan’uwanku da suke ƙinku,

suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce,

‘Bari a ɗaukaka Ubangiji,

don mu ga farin cikinku!’

Duk da haka za su sha kunya.

6Ku ji wannan hayaniya daga birni,

ku ji surutu daga haikali!

Amon Ubangiji ne

yana sāka wa abokan gābansa abin da ya dace da su.

7“Kafin naƙuda ya fara mata,

ta haihu;

kafin zafi ya zo mata,

ta haifi ɗa.

8Wa ya taɓa jin irin wannan abu?

Wa ya taɓa gani irin abubuwan nan?

Za a iya ƙirƙiro ƙasa a rana ɗaya

ko a haifi al’umma farat ɗaya?

Duk da haka da zarar Sihiyona ta fara naƙuda

sai ta haifi ’ya’yanta.

9Zan kai mace har haihuwa

in kuma sa ta kāsa haihu?” In ji Ubangiji.

“Zan rufe mahaihuwa

sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?” In ji Allahnku.

10“Ku yi farin ciki tare da Urushalima ku kuma yi murna saboda ita,

dukanku waɗanda kuke ƙaunarta;

ku yi farin ciki matuƙa tare da ita,

dukanku waɗanda kuke makoki a kanta.

11Gama za ku tsotsa ku kuma ƙoshi

da nonon ta’aziyyarta;

za ku sha sosai

ku kuma ji daɗin yalwarta.”

12Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa,

“Zan fadada salama gare ta kamar kogi,

wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu;

za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta

ku kuma yi wasa a gwiwoyinta.

13Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta

haka zan ta’azantar da ku;

za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”

14Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki

za ku kuma haɓaka kamar ciyawa;

za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa,

amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa.

15Ga shi, Ubangiji yana zuwa da wuta,

kuma kekunan yaƙinsa suna kama da guguwa;

zai sauko da fushinsa da zafi,

tsawatawarsa kuma da harsunan wuta.

16Gama da wuta da kuma takobi

Ubangiji zai yi hukunci a kan dukan mutane,

kuma yawanci za su kasance waɗanda Ubangiji zai kashe.

17“Waɗanda suka tsarkake suka kuma tsabtacce kansu don su je lambu, suna bin wannan da yake tsakiya waɗannan da suke cin naman aladu da ɓeraye da waɗansu abubuwan banƙyama, za su sadu da ƙarshensu tare,” in ji Ubangiji.

18“Ni kuwa, saboda ayyukansu da kuma tunaninsu, ina dab da zuwa in tattara dukan al’ummai da harsuna, za su kuma zo su ga ɗaukakata.

19“Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai. 20Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore. 21Zan kuwa zaɓa waɗansunsu kuma su zama firistoci da Lawiyawa,” in ji Ubangiji.

22“Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata. 23Daga wannan sabon wata zuwa wancan, kuma daga wannan Asabbaci zuwa wancan, dukan mutane za su zo su rusuna a gabana,” in ji Ubangiji. 24“Za su kuma fita su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa; tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, balle wutar da take ƙona su ta mutu, za su kuma zama abin ƙyama ga dukan mutane.”

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

A verdadeira adoração e a reunião das nações

  • Isaías abre este capítulo final declarando que o céu é o trono de Deus e a terra o estrado de Seus pés, de modo que nenhuma construção humana pode contê-Lo. Em vez disso, Deus valoriza os humildes e contritos de espírito que tremem diante de Sua palavra, em contraste com sacrifícios rituais feitos sem verdadeira devoção.Fontes: o próprio texto bíblico
  • A visão profética menciona mensageiros enviados a regiões distantes, incluindo Társis, os arqueiros de Lude, Tubal e Javã, a designação hebraica genérica para o mundo grego. Povos dessas terras remotas e ilhas distantes são retratados viajando a Jerusalém para contemplar a glória de Deus.Fontes: o próprio texto bíblico · Tarshish · Lud · Javan
  • A seção final descreve novos céus e uma nova terra duradouros, onde toda a humanidade vem adorar regularmente de sábado em sábado e de lua nova em lua nova. De maneira surpreendente, Deus anuncia que escolherá alguns dentre essas nações reunidas para servirem como sacerdotes e levitas.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 7, 10, 12, 13, 20
  • Zion · Hoje: Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 8
  • Javan · Hoje: Ionia · 38.200, 27.500 · versículo 19
  • Lud · Hoje: Lydia · 38.488, 28.040 · versículo 19
  • Meshech · Hoje: about 200 km around Gordion · 39.655, 31.994 · versículo 19
  • Tubal · Hoje: Tabal · 37.296, 36.254 · versículo 19

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.