Nations Bible

Ezequiel 41

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Sai mutumin ya kawo ni wuri mai tsarki da yake waje ya kuma auna madogaransa; fāɗin gefe-gefen kamu shida ne a kowane gefe. 2Faɗin ƙofar shiga kamu goma ne, fāɗin bangaye a kowane madogararta kamu biyar-biyar ne. Ya kuma auna wuri mai tsarkin da yake waje; tsawonsa kamu arba’in fāɗinsa kuma kamu ashirin.

3Sa’an nan ya shiga wuri mai tsarki da yake can ciki ya auna madogarar ƙofar shigar; fāɗin kowanne kamu biyu ne. Faɗin ƙofar shigan kamu shida ne, fāɗin bangayen a kowane gefenta kamu bakwai-bakwai ne. 4Ya kuma auna tsawon wuri mai tsarki da yake can ciki; tsawon kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin daga ƙurewa wuri mai tsarki da yake waje. Ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”

5Sa’an nan ya auna bangon haikalin; kaurinsa kamu shida ne, kuma kowane ɗakin da yake a gefe kewaye da haikalin fāɗinsa kamu huɗu ne. 6Ɗakunan da suke gefe masu hawa uku ne, wani bisa wani, guda talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da bangayen haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon haikalin. 7Faɗin ɗakunan da suke gefe kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. Ginin da aka yi kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, don haka ɗakunan suka yi ta ƙara fāɗi yayinda suka ƙara bisa. Akwai mataki daga ɗaki na ƙasa zuwa ɗaki na bisa ta hanya hawa ɗaki na tsakiya.

8Na ga cewa haikalin yana da ɗagaggen tushe kewaye da shi, wanda ya zama harsashin ɗakunan da suke gefe. Tsawonsa kara guda ne mai tsawon kamu shida. 9Kaurin bangon waje na ɗakunan da suke gefe kamu biyar ne. Faɗin filin da yake tsakanin ɗakunan da suke gefen haikalin 10da ɗakunan firistoci kamu ashirin ne kewaye da haikalin. 11Akwai ƙofofin shiga daga fili, ɗaya a arewa ɗaya kuma a kudu; fāɗin tushen da ya yi kusa da filin kamu biyar ne kewaye.

12Faɗin ginin da yake fuskantar filin haikali a wajen yamma kamu saba’in ne. Kaurin bangon ginin kamu biyar ne kewaye, tsawonsa kuma kamu tasa’in ne.

13Sa’an nan ya auna haikalin; tsawonsa kamu ɗari ne, tsawon filin haikalin da ginin tare da bangayensa su ma kamu ɗari ne. 14Faɗin filin haikalin a wajen gabas, haɗe da gaban haikalin, kamu ɗari ne.

15Sa’an nan ya auna tsawon ginin da yake fuskantar filin a bayan haikalin, haɗe da rumfunansa a kowane gefe, kamu ɗari.

Wuri mai tsarki da yake waje, wuri mai tsarki da yake can ciki da shirayin da yake fuskantar filin, 16da madogaran ƙofa da matsattsun tagogi da rumfuna kewaye da su ukun, har da kome da yake gaba haɗe da madogarar ƙofa, an rufe su da katako. An rufe bangon haikalin daga ƙasa har zuwa tagogi, tagogin kuwa an rufe su. 17A filin da yake bisan ƙofar shiga na waje zuwa wuri mai tsarki na can ciki da kuma a bangayen da aka daidaita tsakani kewaye da wuri mai tsarki na can ciki da kuma na can waje 18an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino. Zānen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu, 19fuskar ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe, ɗaya fuskar kamar ta zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zāna su dukan a jikin bangon haikalin kewaye. 20Daga ƙasa zuwa daurin ƙofa, an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a waje na wuri mai tsarki.

21Wuri mai tsarki da yake waje yana da madogarar ƙofa murabba’i, haka ma wadda take a gaban Wuri Mafi Tsarki. 22Akwai bagaden katako mai tsayi kamu uku, fāɗinsa kamu biyu da kuma tsawonsa kamu biyu; kusurwansa, tushensa da kuma gefe-gefensa duk katako ne. Sai mutumin ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da yake a gaban Ubangiji.” 23A wuri mai tsarki da yake waje da kuma Wuri Mafi Tsarki suna da ƙofa biyu a haɗe. 24Kowace ƙofa tana da murfi biyu masu buɗewa ciki da waje. 25A ƙofofin wuri mai tsarki da yake waje an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangayen, akwai kuma rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin. 26A bangayen da suke gefen shirayin akwai matsattsun tagogi da aka zāna siffar itatuwan dabino a kowane gefe. Gefe-gefen ɗakunan haikalin ma suna da rumfuna.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

O Interior do Templo Visionário

  • O santuário na visão de Ezequiel é dividido em duas seções principais: um santuário exterior medindo quarenta por vinte côvados e uma sala interior de vinte côvados quadrados, identificada como o Lugar Santíssimo.Fontes: o próprio texto bíblico · Most Holy Place
  • As paredes internas e as portas duplas eram revestidas de madeira e entalhadas com palmeiras e querubins alternados. Cada querubim foi retratado com dois rostos: o de um ser humano voltado para uma palmeira e o de um leão jovem voltado para a outra.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Três andares de câmaras laterais cercavam o templo, com trinta quartos em cada nível. As estruturas apoiavam-se em saliências externas para que os suportes não precisassem ser fixados diretamente na parede do próprio templo.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Most Holy Place · Hoje: on Mount Moriah · 31.778, 35.236 · versículo 4
  • Holy Place · Hoje: on Mount Moriah · 31.778, 35.236 · versículos 21, 23

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.