Ezequiel 36
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Annabci wa duwatsun Isra’ila
1“Ɗan mutum, ka yi annabci wa duwatsun Isra’ila ka ce, ‘Ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji. 2Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa abokin gāba yana magana game da ku cewa, “Yauwa! Tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu.” ’ 3Saboda haka ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin sun lalace ku suka kuma maishe ku kufai marar amfani a kowane gefe saboda ku zama mallakar sauran al’ummai da kuma abin magana da tsegumi ga mutane, 4saboda haka, ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana faɗa wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, wa kufai da garuruwan da suka zama kango waɗanda aka washe aka wulaƙanta suka zama ganimar sauran al’ummai da suke kewaye da ku, 5ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa cikin kishina mai ƙuna na yi magana gāba da sauran al’ummai, da kuma gāba da Edom, gama da farin ciki da reni a zukatansu suka mai da ƙasata mallakarsu don su washe wuraren kiwonta.’ 6Saboda haka ka yi annabci game da ƙasar Isra’ila ka kuma ce wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al’ummai. 7Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa na ɗaga hannuna sama na rantse cewa al’ummai da suke kewaye da ku za su sha ba’a.
8“ ‘Amma ku, ya duwatsun Isra’ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanena Isra’ila, gama ba da daɗewa ba za su komo gida. 9Na damu da ku kuma zan dube ku da tausayi; za ku nome ku kuma shuka, 10zan kuma riɓaɓɓanya mutane a kanku, dukan gidan Isra’ila ke nan. Za a zauna a birane a kuma sāke gina rusassun wurare. 11Zan sa mutane da dabbobi su yi yawa a kanku, za su kuma ba da ’ya’ya su kuma yi yawa. Zan zaunar da mutane a kanku kamar dā zan kuma sa ku wadaita fiye da dā. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. 12Zan sa mutanena Isra’ila su yi tafiya a kanku. Za su mallake ku, za ku kuma zama gādonsu; ba za ku ƙara sa su rasa ’ya’yansu ba.
13“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin mutane suna magana game da ku cewa, “Kun cinye mutane kuka kuma sa al’ummarku ta rasa ’ya’yanta,” 14saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ko ku sa al’ummarku ta rasa ’ya’ya ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 15Ba zan ƙara bari ku ji maganar banza ta al’ummai ba, ba kuwa za ku ƙara shan ba’ar mutane ko in sa al’ummarku ta fāɗi ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
An tabbatar da maidowar Isra’ila
16Maganar Ubangiji ta sāke zuwa mini cewa, 17“Ɗan mutum, sa’ad da mutanen Isra’ila suke zama a ƙasarsu, sun ƙazantar da ita ta wurin halinsu da kuma ayyukansu. Halinsu ya yi kamar rashin tsarkin mace a lokacin al’adarta a gabana. 18Saboda haka na husata da su domin sun yi kisankai a ƙasar kuma domin sun ƙazantar da ita da gumakansu. 19Na warwatsa su cikin al’ummai, suka kuwa warwatsu cikin dukan ƙasashe; na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu. 20Kuma ko’ina da suka tafi a cikin al’ummai sun ɓata sunana mai tsarki, gama an yi magana a kansu cewa, ‘Waɗannan mutanen Ubangiji ne, duk da haka dole su bar ƙasarsa.’ 21Na damu saboda sunana mai tsarki, wanda gidan Isra’ila ya ɓata a cikin al’ummai inda suka tafi.
22“Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba dominku ba ne, ya gidan Isra’ila da nake yin waɗannan abubuwa, amma saboda sunana ne mai tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al’ummai inda kuka tafi. 23Zan nuna tsarkin girman sunana, wanda aka ɓata a cikin al’umma, sunana da kuka ɓata a cikinsu. Sa’an nan al’ummai za su san cewa ni ne Ubangiji, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinku a idanunsu.
24“ ‘Gama zan fitar da ku daga al’ummai; zan tattara ku daga dukan ƙasashe in komo da ku zuwa ƙasarku. 25Zan yayyafa muku ruwa mai tsabta, zan kuwa tsarkake ku daga dukan ƙazantarku daga kuma dukan gumakanku. 26Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama. 27Zan kuma sa Ruhuna a cikinku in kuma motsa ku ku bi ƙa’idodina ku kuma kiyaye dokokina. 28Za ku zauna a ƙasar da na ba wa kakanninku; za ku zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku. 29Zan cece ku daga dukan rashin tsabtarku. Zan sa hatsi ya yi yalwa ba zan kawo yunwa a kanku ba. 30Zan ƙara ’ya’yan itatuwa da amfanin gona, saboda kada ku ƙara shan kunya a cikin al’ummai saboda yunwa. 31Sa’an nan za ku tuna mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda zunubanku da kuma ayyukanku na banƙyama. 32Ina so ku san cewa ba na yi wannan saboda ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku ji kunya ku kuma giggita saboda halinku, ya gidan Isra’ila!
33“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na tsarkake ku daga dukan zunubanku, zan sāke zaunar da ku a garuruwanku, a kuma sāke gina kufai. 34Ƙasar da take kango a dā za ku nome ta a maimakon zama kango a idon dukan masu ratsawa a cikinta. 35Za su ce, “Wannan ƙasar da take kango a dā ta zama kamar lambu Eden; biranen da dā suke kufai, kango da kuma aka lalata, yanzu suna da katanga ana kuma zama a ciki.” 36Sa’an nan al’ummai kewaye da ku da suka rage za su san cewa Ni Ubangiji na sāke gina abin da aka lalace na kuma sāke shuka abin da yake kango. Ni Ubangiji na faɗa, kuma zan aikata.’
37“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa har yanzu zan ji roƙon gidan Isra’ila in kuma yi musu wannan. Zan sa mutanensu su yi yawa kamar tumaki, 38yawansu ya yi kamar garken tumaki don hadaya a Urushalima a ƙayyadaddun lokuta bukukkuwarta. Haka biranen da suke kufai za su cika da ɗumbun mutane. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”

Você sabia?
A Renovação da Terra e do Coração
- Ezequiel é orientado a falar diretamente à paisagem física de Israel — seus montes, vales e colinas —, revertendo o desprezo das nações vizinhas. A região vizinha de Edom havia avançado com desprezo para se apossar das pastagens desoladas durante o exílio.Fontes: o próprio texto bíblico · Edom
- O capítulo apresenta a promessa de transformação espiritual interior, na qual Deus promete purificar o povo com água limpa, trocar o coração de pedra por um coração de carne e colocar Seu Espírito dentro deles.Fontes: o próprio texto bíblico
- A restauração agrícola da terra arruinada é comparada à fertilidade do jardim do Éden, enquanto a multidão de pessoas que retorna às cidades reconstruídas é comparada aos numerosos rebanhos sacrificiais reunidos em Jerusalém durante as festas solenes.Fontes: o próprio texto bíblico · Eden · Jerusalem
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org