Nations Bible

Ezequiel 11

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

Hukuncin shugabannin Isra’ila

1Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni ƙofar gidan Ubangiji wadda take fuskantar gabas. Can a mashigi zuwa ƙofar akwai mutum ashirin da biyar, na kuma ga a cikinsu akwai Ya’azaniya ɗan Azzur da Felatiya ɗan Benahiya, shugabannin jama’a. 2Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta suna kuma ba da muguwa shawara a cikin wannan birni. 3Suna cewa, ‘Lokaci bai yi kusa da za a gina gidaje ba? Wannan birni yana tukunyar dahuwa, mu ne kuwa naman.’ 4Saboda haka yi annabci a kansu; yi annabci, ɗan mutum.”

5Sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya kuma faɗa mini in ce, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, haka kuke cewa, ya gidan Isra’ila, amma na san abin da yake a zuciyarku. 6Kun kashe mutane da yawa a wannan birni kuka kuma cika titunanta da gawawwaki.

7“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa gawawwakin da kuka zubar a can su ne naman, wannan birni kuwa ita ce tukunya, amma zan kore ku daga cikinta. 8Kuna jin tsoron takobi, kuma takobi ne zan kawo muku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 9Zan kore ku daga birnin in miƙa ku a hannuwan baƙi in kuma azabtar da ku. 10Za ku mutu ta wurin takobi, zan kuma hukunta ku a iyakokin Isra’ila. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. 11Wannan birni ba za tă zama muku tukunya ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinta ba; zan hukunta ku a iyakokin Isra’ila. 12Za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji, gama ba ku bi ƙa’idodina ba balle ku kiyaye dokokina, amma kuka bi hanyoyin al’ummai kewaye da ku.”

13Yanzu yayinda nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benahiya ya mutu. Sai na fāɗi rubda ciki na kuma yi kuka da babbar murya na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Za ka hallaka raguwar Isra’ila ƙaƙaf ne?”

14Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 15“Ɗan mutum, ’yan’uwanka, ’yan’uwanka waɗanda suke danginka na cikinka da kuma dukan gidan Isra’ila su ne waɗanda mutanen Urushalima suka ce, ‘Su ne da nisa daga Ubangiji; an ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu.’

Alkawarin komowar Isra’ila

16“Saboda haka ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ko da yake na kore su zuwa cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama wuri mai tsarki a gare su a ƙasashen da suka tafi.’

17“Saboda haka, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan tattaro ku daga al’ummai in kuma dawo da ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku, zan kuwa sāke mayar muku da ƙasar Isra’ila.’

18“Za su dawo gare ta su kawar da dukan mugayen siffofi da gumaka masu banƙyama. 19Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama. 20Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu. 21Amma game da waɗanda zukatansu suka karkata ga bin mugayen siffofi da gumakan banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

22Sa’an nan kerubobi, tare da da’irori kusa da su, suka buɗe fikafikansu, ɗaukakar Allah kuwa tana a bisansu. 23Ɗaukakar Ubangiji ta haura daga cikin birnin ta sauka a bisa dutse gabas da shi. 24Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma kawo ni ga masu zaman bauta a ƙasar Babilon cikin wahayin da Ruhun Allah ya bayar.

Sa’an nan wahayin da na gani ya rabu da ni, 25na kuwa faɗa wa masu zaman bautan dukan abin da Ubangiji ya nuna mini.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Julgamento de Jerusalém e esperança para os exilados

  • Na porta oriental do templo em Jerusalém, Ezequiel viu vinte e cinco líderes, incluindo Jazanias, filho de Azur, e Pelatias, filho de Benaia, dando maus conselhos e alegando que a cidade os protegeria como uma panela. Enquanto Ezequiel profetizava a mensagem de julgamento, Pelatias morreu repentinamente, levando o profeta a clamar com angústia pelo restante de Israel.Fontes: o próprio texto bíblico · Pelatiah · Jaazaniah · Azur
  • Enquanto os habitantes que permaneceram em Jerusalém afirmavam que a comunidade no exílio havia sido rejeitada e estava longe do SENHOR, Deus declarou que seria um santuário para os exilados entre as nações. Ele prometeu reuni-los, retirar o coração de pedra e dar-lhes um coração de carne obediente aos seus preceitos.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Ezequiel observou os querubins estenderem suas asas enquanto a glória do SENHOR se afastava do meio de Jerusalém e pairava sobre o monte a leste da cidade. A visão terminou quando o Espírito transportou o profeta de volta aos exilados na Caldeia, onde ele relatou tudo o que havia visto.Fontes: o próprio texto bíblico · Chaldea · Jerusalem

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • East Gate · Hoje: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 1
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 9, 15, 24
  • Chaldea · 30.962, 46.104 · versículo 24

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.