Deuteronômio 29
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Sabuntawar alkawari
1Waɗannan su ne sharuɗan alkawarin da Ubangiji ya umarci Musa yă yi da Isra’ilawa a Mowab, wato, ban da alkawarin da ya yi da su a Dutsen Horeb.
2Sai Musa ya tara dukan Isra’ila, ya ce musu,
Idanunku sun ga dukan abin da Ubangiji ya yi a Masar ga Fir’auna, ga kuma dukan shugabanninsa da kuma ga dukan ƙasarsa. 3Da idanunku kun ga waɗannan gwaje-gwaje, waɗannan alamu masu banmamaki, da al’ajabai masu girma. 4Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku hankalin ganewa, ko idanun da za su gani, ko kunnuwan da za su ji ba. 5Shekaru arba’in da na jagorance ku cikin hamada, tufafinku ba su yage ba, haka kuwa takalman da suke a ƙafafunku. 6Ba ku ci burodi ba, ba ku kuwa sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa jiri ba. Ya yi haka don ku san cewa shi ne Ubangiji Allahnku.
7Sa’ad da kuka kai wannan wuri, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan, suka fito don su yi yaƙi da mu, amma muka ci su da yaƙi. 8Muka ƙwace ƙasarsu, muka ba da ita gādo ga mutanen Ruben, mutanen Gad, da kuma rabin mutanen Manasse.
9Saboda haka sai ku kiyaye, ku bi sharuɗan wannan alkawari, don ku yi nasara a cikin kome da kuke yi. 10Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabanninku da manyan mutanenku, dattawanku da hafsoshinku, da kuma dukan sauran mutanen Isra’ila, 11tare da ’ya’yanku da matanku, da baƙin da suke zama sansanoninku, har ma da waɗanda suke muku faskare, da waɗanda suke ɗiba muku ruwa. 12Kuna tsaye a nan don ku yi alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji yake yi ta wurin rantsuwa da ku a wannan rana, 13don yă mai da ku jama’arsa yau, shi kuwa yă zama Allahnku kamar yadda ya yi muku alkawari, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub. 14Ina yin wannan alkawari da rantsuwar, ba da ku kaɗai da 15kuke tsattsaye a nan tare da mu a yau a gaban Ubangiji Allahnmu ba, amma har da waɗanda ba sa nan yau.
16Ku kanku kun san yadda muka yi zama a Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al’ummai muka wuce. 17A cikinsu, kun ga siffofi masu banƙyama da gumaka na itace da dutse, na azurfa da zinariya. 18Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, tă koma ga bauta wa gumakan waɗannan al’ummai. Kada a sami wani tushe mai ba da ’ya’ya masu dafi, masu ɗaci a cikinku.
19Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai. 20Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama. 21Ubangiji zai ware shi daga dukan kabilan Isra’ila don yă hukunta shi bisa ga dukan la’anonin alkawarin da aka rubuta a wannan Littafin Doka.
22Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato, ’ya’yan da za su gāje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji ya buge ta da su. 23Ƙasar gaba ɗaya za tă zama gishiri mai ƙuna marar amfani da kuma kibiritu, babu shuki, babu abin da yake tsirowa, babu itatuwan da suke girma a cikinta. Za tă zama kamar yadda aka hallaka Sodom da Gomorra, Adma da Zeboyim, waɗanda Ubangiji ya hallaka cikin zafin fushinsa. 24Dukan al’ummai za su yi tambaya su ce, “Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya jawo wannan fushi mai tsanani haka?”
25Amsar kuwa za tă zama, “Wannan ya zama haka domin wannan mutane, sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fitar da su daga Masar. 26Sun juya, suka bauta wa waɗansu alloli, suka rusuna musu, allolin da ba su sani ba, allolin da Ubangiji bai ba su ba. 27Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan wannan ƙasa, har ya kawo dukan la’anoni da aka rubuta a wannan littafi a kanta. 28Cikin zafin fushi da babbar hasala Ubangiji ya tumɓuke su daga ƙasarsu, ya watsar da su cikin wata ƙasa dabam, kamar yadda suke a yau.”
29Ubangiji Allahnmu bai bayyana abubuwa na yanzu da na nan gaba ba, amma ya umarce mu mu kiyaye kalmomin dokar da ya ba mu, mu da kuma ’ya’yanmu har abada.

Você sabia?
A Renovação da Aliança em Moabe
- A aliança na terra de Moabe é apresentada como um pacto adicional àquele estabelecido no monte Horebe. Para incentivar a fidelidade, Moisés relembrou os quarenta anos no deserto e as vitórias sobre o rei Seom de Hesbom e o rei Ogue de Basã.Fontes: o próprio texto bíblico · Horeb · Sihon · Og
- A reunião da aliança incluiu toda a comunidade, desde líderes tribais, anciãos e homens até mulheres, crianças e estrangeiros residentes que cortavam lenha e tiravam água. Moisés enfatizou que o juramento vinculava não apenas os presentes naquele dia, mas também as gerações futuras.Fontes: o próprio texto bíblico
- Moisés advertiu o povo contra o desvio para adorar ídolos feitos de madeira, pedra, prata e ouro. A quebra da aliança traria severo julgamento, deixando a terra devastada por enxofre e sal, como a destruição de Sodoma e Gomorra.Fontes: o próprio texto bíblico · Sodom
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Moab · Hoje: Moab 1 · 31.181, 35.701 · versículo 1
- Mount Horeb · Hoje: Jebel Musa · 28.540, 33.973 · versículo 1
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 2, 16, 25
- Bashan · 32.781, 35.935 · versículo 7
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org