Daniel 4
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Nebukadnezzar ya yi mafarkin itace
1Daga sarki Nebukadnezzar.
Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya.
Salama mai yawa ta tabbata a gare ku!
2Ina murna in shaida muku game da alamu da al’ajabai waɗanda Allah Mafi Ɗaukaka ya yi ta wurina.
3Alamunsa da girma suke,
ayyukansa da girma suke!
Mulkinsa mulki ne na har abada;
sarautarsa kuma za tă dawwama daga zamani zuwa zamani.
4Ni, Nebukadnezzar, ina zaune a gidana cikin fadata, ina jin daɗi ina bunkasa. 5Na yi mafarkin da ya ba ni tsoro. A sa’ad da nake kwance a gadona, siffofi da wahayoyi da suka bi ta cikin tunanina sun firgita ni. 6Don haka na ba da umarni a tattaro dukan masu hikima na Babilon su bayyana a gabana domin su fassara mini mafarkin. 7Sa’ad da masu sihiri, da masu dabo, da masanan taurari da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya fassarta mini mafarkin ba. 8A ƙarshe, sai Daniyel ya zo gabana na kuma faɗa masa mafarkin. (Ana ce da shi Belteshazar, wanda aka ba shi sunan allahna kuma ruhun alloli masu tsarki suna a bisansa.)
9Na ce, “Belteshazar, shugaban masu sihiri, na san ruhun alloli suna a kanka, babu wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga dai mafarkin da na yi, sai ka fassara mini. 10Waɗannan su ne wahayin da na gani a lokacin da nake kwance a gadona, na duba, a gabana kuwa ga wani itace a kafe a tsakiyar duniya, yana da tsawo ƙwarai. 11Itacen ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, har tsayinsa ya taɓa sarari sama; ana iya ganinsa a ko’ina a duniya. 12Ganyayensa suna da kyau, yana da ’ya’ya jingim, abinci kuma domin kowa da kowa. A ƙarƙashinsa namun jeji suke samun wurin hutawa, kuma tsuntsayen sama suna zaune a bisa rassansa; daga cikinsa kowace halitta take cin abinci.
13“A cikin wahayin da gani sa’ad da nake kwance a kan gadona, Na duba, a gabana kuwa ga wani ɗan saƙo, mai tsarki, yana saukowa daga sama. 14Sai ya yi kira da babbar murya ya ce, ‘A sare itacen a kuma yayyanka rassansa; a karkaɗe ganyensa a kuma warwatsar da ’ya’yansa. Bari dabbobi su tashi daga ƙarƙashinsa da kuma tsuntsayen da suke a rassansa. 15Amma a bar kututturen da kuma saiwoyinsa, a daure shi da ƙarfe da kuma tagulla, a bar shi a cikin ƙasa, a cikin ciyayin filaye.
“ ‘Bari yă jiƙu da raɓar, bari yă zauna cikin dabbobi tare da tsire-tsiren duniya. 16Bari a canja tunaninsa irin na mutane a ba shi tunani irin na dabbobi, har sau bakwai su wuce a kansa.
17“ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’
18“Wannan shi ne mafarkin da ni, Nebukadnezzar, na yi. Yanzu Belteshazar, sai ka faɗa mini abin da yake nufi, domin babu wani a cikin masu hikima a mulkina da ya iya fassara mini shi. Amma za ka iya, domin ruhun alloli masu tsarki yana a bisanka.”
Daniyel Ya Fassara Mafarkin
19Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.”
Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan! 20Itacen da ka gani; wanda ya yi girma da ƙarfe, da tsayinsa ya taɓa sararin sama, wanda ana ganinsa ko’ina a duniya, 21wanda ganyayensa masu kyau ne yana da ’ya’yan itace da yawa, wanda yake ba da abinci ga duka, yana ba da wurin hutu ga namun jeji, kuma rassansa suna ɗauke da sheƙar tsuntsayen sama. 22Ya sarki kai ne itacen nan! Ka yi girma da ƙarfi; girmanka kuma ta kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko’ina a duniya.
23“Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’
24“Ga fassarar, ya sarki, wannan ita ce doka wadda Mafi Ɗaukaka ya bayar a kan ranka yă daɗe, sarkina. 25Za a kore ka daga cikin mutane, za ka kuma zauna cikin namun jeji; za ka ci ciyawa kamar shanu, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cif sa’an nan za ka sani cewa Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama. 26Umarni na barin kututturen itacen da saiwoyinsa yana nufin cewa za a maido maka da mulkinka a lokacin da ka gane cewa Mai sama ne yake mulki. 27Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”
Mafarkin Ya Cika
28Duk wannan kuwa ya faru da sarki Nebukadnezzar. 29Bayan wata goma sha biyu, a sa’ad da sarki yake takawa a bisan saman ɗakin fadar Babilon, 30sai ya ce, “Ba wannan ita ce Babilon babba da na gina domin wurin zaman sarautar Babilon, da ikona kuma domin ɗaukakar darajata ba?”
31Tun kalmomin suna cikin bakinsa sai ya ji murya daga sama tana cewa, “Wannan shi ne abin da aka zartar a kanka, Sarki Nebukadnezzar. An karɓe ikon mulkinka. 32Za a kore ka daga cikin mutane za ka kuma yi rayuwa tare da namun jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cif, sa’an nan za ka gane Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.”
33Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.
34A ƙarshen waɗannan kwanaki, ni, Nebukadnezzar, na ɗaga idanuna sama, sai hankalina ya komo mini. Na kuwa yabi Maɗaukaki, na girmama shi, na ɗaukaka shi wanda yake rayayye har abada.
Mulkinsa dawwammamen mulki ne;
sarautarsa ta dawwama daga zamani zuwa zamani.
35Dukan mutanen duniya
ba a bakin kome suke ba.
Yakan yi abin da ya gamshe shi
da ikokin sama
da kuma na mutanen duniya.
Babu mai hana shi
ko yă ce masa; “Me ka yi?”
36A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. ’Yan majalisata da fadawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā. 37Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin sama, ina waƙa ina kuma darjanta shi, saboda dukan abin da ya yi mini, mai kyau ne kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Kuma duk masu tafiya da girman kai zai ƙasƙantar da su.

Você sabia?
O sonho e a humilhação do rei
- O capítulo 4 de Daniel está estruturado como um decreto imperial ou carta aberta dirigida pelo rei Nabucodonosor a todas as nações e línguas da terra. Nele, o próprio rei relata seu sonho perturbador, o período de loucura em que viveu entre os animais e seu louvor final ao Deus Altíssimo.Fontes: o próprio texto bíblico
- Nabucodonosor foi o rei mais poderoso do Império Babilônico, sediado na antiga cidade de Babilônia, às margens do rio Eufrates. A narrativa relata que sua humilhação repentina ocorreu logo após ele caminhar pelo terraço de seu palácio, vangloriando-se de ter edificado a grande Babilônia por sua própria força e majestade.Fontes: Nebuchadnezzar · Babylon · o próprio texto bíblico
- Na corte real, Daniel era chamado pelo nome caldeu Beltessazar, que significa 'Beltis proteja o rei'. Nabucodonosor recorreu a ele depois que os magos, encantadores e astrólogos babilônios se mostraram incapazes de interpretar a visão da grande árvore.Fontes: Daniel · o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org