Nations Bible

Atos 7

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

Jawabin Istifanus ga majalisa

1Sai babban firist ya tambaye shi ya ce, “Waɗannan zargen gaskiya ne?”

2Game da wannan ya amsa ya ce, “’Yan’uwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran. 3Allah ya ce, ‘Ka bar ƙasarka da kuma mutanenka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.’

4“Saboda haka ya bar ƙasar Kaldiyawa ya kuma yi zama a Haran. Bayan mutuwar mahaifinsa, Allah ya aika da shi wannan ƙasar da yanzu kuke zama. 5Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro. 6Allah ya yi magana da shi ta haka, ‘Shekara ɗari huɗu, zuriyarka za tă yi baƙunci a wata ƙasar da ba tasu ba, za su yi bauta su kuma sha wulaƙanci. 7Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘Kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’ 8Sa’an nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan.

9“Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi 10ya kuma cece shi daga dukan wahalolinsa. Ya ba wa Yusuf hikima ya kuma sa ya sami farin jini a wurin Fir’auna, sarkin Masar; saboda haka ya mai da shi mai mulki a kan Masar da kuma dukan fadarsa.

11“Sai yunwa ta auko wa dukan Masar da Kan’ana, ta kawo wahala mai tsanani, kakanninmu ba su iya samun abinci ba. 12Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa akwai hatsi a Masar, sai ya aiki kakanninmu ziyararsu ta farko. 13A ziyararsu ta biyu, Yusuf ya faɗa wa ’yan’uwansa wane ne shi, Fir’auna kuwa ya sami sani game da iyalin Yusuf. 14Bayan wannan, Yusuf ya aika a zo da mahaifinsa Yaƙub da dukan iyalinsa, gaba ɗaya dai mutum saba’in da biyar ne. 15Sai Yaƙub ya gangara zuwa Masar, inda shi da kuma kakanninmu suka mutu. 16Aka dawo da gawawwakinsu Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya daga wurin ’ya’yan Hamor da waɗansu kuɗi a Shekem.

17“Da lokaci ya yi kusa da Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim, sai yawan mutanenmu da suke a Masar ya ƙaru ƙwarai. 18Sa’an nan wani sarki, wanda bai san kome game da Yusuf ba, ya zama mai mulkin Masar. 19Ya kuwa wulaƙanta mutanenmu sosai, ya kuma gwada wa kakanni-kakanninmu azaba ta wurin tilasta su su zubar da sababbin jariransu, don su mutu.

20“A lokacin nan aka haifi Musa, shi kuwa ba kamar sauran jarirai ba ne. Wata uku aka yi renonsa a gidan mahaifinsa. 21Sa’ad da aka ajiye shi a waje, diyar Fir’auna ta ɗauke shi ta kuma rene shi kamar ɗanta. 22Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka.

23“Da Musa ya cika shekara arba’in da haihuwa, sai ya yanke shawara yă ziyarci ’yan’uwansa Isra’ilawa. 24Ya ga ɗayansu yana shan wulaƙanci a hannun wani mutumin Masar, sai ya je ya kāre shi, ya rama masa ta wurin kashe mutumin Masar ɗin. 25Musa ya yi tsammani mutanensa za su gane cewa, Allah yana amfani da shi don yă cece su, amma ba su gane ba. 26Kashegari, Musa ya sadu da Isra’ilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku ’yan’uwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’

27“Amma mutumin da yake wulaƙanta ɗayan, ya tura Musa a gefe ya ce, ‘Wa ya mai da kai mai mulki, da alƙali a kanmu? 28Kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan na jiya?’ 29Sa’ad da Musa ya ji haka, sai ya gudu zuwa ƙasar Midiyan, inda ya yi baƙunci, ya kuma haifi ’ya’ya biyu maza.

30“Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai. 31Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce, 32‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.

33“Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne. 34Tabbatacce na ga wulaƙancin da ake yi wa mutanena a Masar. Na ji nishinsu na kuma sauka domin in ’yantar da su. Yanzu ka zo, zan aike ka ka koma Masar.’

35“Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin mala’ikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yă zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu. 36Ya fitar da su daga Masar ya kuma yi ayyukan da abubuwan banmamaki a Masar, a Jan Teku, da kuma cikin hamada har shekara arba’in.

37“Wannan Musa ne ya ce Isra’ilawa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’ 38Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da mala’ikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don yă miƙa mana.

39“Amma kakanninmu suka ƙi yin masa biyayya. A maimakon haka, sai suka ƙi shi a cikin zuciyarsu kuwa suka koma Masar. 40Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba!’ 41A lokacin ne suka ƙera gunki mai siffar ɗan maraƙi. Suka kawo masa hadayu suka kuma yi bikin girmama abin da suka ƙera da hannuwansu. 42Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa,

“ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki

shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila?

43Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek,

da tauraron allahnku Refan,

gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.

Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.

44“Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani. 45Bayan sun gāji tabanakul nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga al’umman da Allah ya kora a idanunsu. Tabanakul ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda, 46wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yă yi wa Allah na Yaƙub wurin zama. 47Amma Solomon ne ya gina masa gida.

48“Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa,

49“ ‘Sama ne kursiyina,

duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata.

Wane irin gida za ka gina mini?

Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance?

In ji Ubangiji.

50Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’

51“Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki! 52An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi 53ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin mala’iku amma ba ku yi biyayya da ita ba.”

Jifan Istifanus

54Da membobin Sanhedrin suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu. 55Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah. 56Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”

57Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya. 58Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.

59Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” 60Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Estêvão reconta a história de Israel

  • Estêvão abre o discurso com Abraão ainda na Mesopotâmia, antes de se estabelecer em Harã, quando recebeu a ordem de deixar sua terra e seus parentes. Mesopotâmia — em hebraico Aram-naharaim, “Síria dos dois rios” — era o nome que gregos e romanos davam à região entre o Eufrates e o Tigre; no Antigo Testamento ela também se chama Padan-aram, “a planície de Arã”, e o norte desse planalto foi o lar antigo dos antepassados dos hebreus. O Easton's Bible Dictionary (1897) observa que esse primeiro chamado não aparece no Antigo Testamento, embora Gênesis 12 o deixe implícito, e que Abraão saiu de Ur, na Caldeia, e percorreu cerca de 300 milhas ao norte, até Harã.Fontes: o próprio texto bíblico · Mesopotamia · Abraham
  • Estêvão afirma que os ossos de Jacó e dos pais foram levados de volta a Siquém e depositados no túmulo que Abraão comprara aos filhos de Hamor. O Easton's Bible Dictionary (1897) identifica Hamor como um heveu cujo nome significa “jumento”, nota que em Atos 7:16 ele é chamado Emmor e diz que Jacó lhe comprou o terreno de Siquém em que José foi sepultado mais tarde. O verbete acrescenta que Siquém, filho de Hamor, fundou a cidade que recebeu o seu nome.Fontes: o próprio texto bíblico · Hamor
  • Estêvão localiza a sarça ardente no deserto, perto do monte Sinai, e diz que Moisés recebeu ali palavras vivas da parte do anjo que lhe falou no monte. O Easton's Bible Dictionary (1897) trata Sinai — nome ligado a Sin, um deus da lua — como o mesmo distrito montanhoso também chamado Horebe. Segundo o verbete, os hebreus chegaram a essa região no terceiro mês após o Êxodo, depois de uma viagem de cerca de 150 milhas desde o mar Vermelho, com todas as voltas do caminho, e ficaram acampados cerca de um ano.Fontes: o próprio texto bíblico · Mount Sinai

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Haran · Hoje: Harran · 36.864, 39.033 · versículos 2, 4
  • Mesopotamia · Hoje: Aram-naharaim · 36.864, 39.033 · versículo 2
  • Chaldea · 30.962, 46.104 · versículo 4
  • Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 9, 10, 11, 12, 14, 15, 17, 18, 34, 36, 39, 40
  • Canaan · 32.767, 35.333 · versículo 11
  • Shechem · Hoje: Tell Balatah · 32.214, 35.282 · versículo 16
  • Nile · Hoje: Nile River · 31.465, 30.367 · versículo 19
  • Midian · 28.495, 35.012 · versículo 29
  • Babylon · 32.543, 44.422 · versículo 43

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.