2 Samuel 23
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Kalmomin Dawuda na ƙarshe
1Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe.
“Abubuwan da Dawuda ɗan Yesse ya yi magana a kai,
abubuwan da mutumin da Mafi Ɗaukaka ya girmama.
Mutumin da Allah na Yaƙub ya zaɓa yă zama sarki,
wanda kuma yake mawaƙi waƙoƙin Isra’ila.
2“Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina;
maganarsa tana a harshena.
3Allah na Isra’ila ya yi magana,
Dutsen Isra’ila ya ce mini,
‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci,
sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,
4yana kama da hasken safiya
a safiya marar girgije,
kamar haske bayan ruwan sama
da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’
5“Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba?
Ashe, Allah bai yi madawwamiyar yarjejjeniya da ni
shiryayye da ɗaurarre a kowane sashi ba?
Ba zai kawo ga cikar cetona
yă kuma biya duk bukatuna ba?
6Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan
da ba a tattara da hannu.
7Duk wanda ya taɓa ƙaya
yakan yi amfani da wani ƙarfe ne ko sandar māshi;
akan ƙone su inda suke a zube.”
Jarumawan Dawuda
8Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda.
Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.
9Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu, 10amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.
11Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa. 12Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.
13A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim. 14Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem. 15Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!” 16Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji. 17Sai ya ce, “ Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba.
Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.
18Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan. 19Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.
20Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki. 21Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin. 22Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku. 23Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
24Cikin talatin ɗin kuwa akwai,
Asahel, ɗan’uwan Yowab,
Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,
25Shamma, mutumin Harod,
Elika, mutumin Harod,
26Helez, mutumin Falti,
Ira, ɗan Ikkesh mutumin Tekowa,
27Abiyezer, mutumin Anatot, da
Mebunnai, mutumin Husha,
28Zalmon, mutumin Aho,
da Maharai, mutumin Netofa,
29Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa,
Ittai, ɗan Ribai mutumin Gibeya a Benyamin,
30Benahiya, mutumin Firaton,
da Hiddai, daga rafuffukan Ga’ash,
31Abi-Albon, mutumin Arba, da
Azmawet, mutumin Bahurim,
32Eliyaba, mutumin Sha’albo,
’Ya’yan Yashen,
Yonatan, 33ɗan Shamma mutumin Harar,
da Ahiyam, ɗan Sharar mutumin Harod.
34Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka,
Eliyam, ɗan Ahitofel mutumin Gilo,
35Hezro, mutumin Karmel,
Fa’arai, mutumin Arbi,
36Igal, ɗan Natan mutumin Zoba,
ɗan Hagiri,
37Zelek, mutumin Ammon
Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai,
38Ira, mutumin Itra.
Gareb, mutumin Itra,
39da kuma Uriya, mutumin Hitti.
Você sabia?
As últimas palavras e os valentes de Davi
- O oráculo poético de Davi retrata o governante ideal como alguém que lidera com justiça e temor a Deus, comparando tal reinado à luz radiante de uma manhã sem nuvens e ao frescor da chuva que faz brotar a relva.Fontes: o próprio texto bíblico
- Enquanto Davi se abrigava na caverna de Adulão e as forças filisteias ocupavam o vale de Refaim e Belém, três guerreiros de elite romperam as linhas inimigas para buscar água do poço junto à porta de Belém. Comovido pelo perigo que enfrentaram, Davi recusou-se a bebê-la e a derramou como oferta ao Senhor, considerando-a como o sangue de homens que arriscaram a vida.Fontes: o próprio texto bíblico · Adullam · Bethlehem · Valley of Rephaim
- Entre os guerreiros de destaque da lista estava Benaías, filho de Joiada, de Cabzeel, célebre por abater dois valorosos guerreiros de Moabe, descer a uma cova em dia de neve para matar um leão e desarmar um gigante egípcio para feri-lo com a própria lança.Fontes: o próprio texto bíblico · Benaiah · Kabzeel
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Valley of Rephaim · 31.763, 35.219 · versículo 13
- Bethlehem · 31.704, 35.208 · versículos 14, 15, 16, 24
- Moab · Hoje: Moab 1 · 31.181, 35.701 · versículo 20
- Tekoa · Hoje: Khirbet Teku’a · 31.632, 35.210 · versículo 26
- Arabah · 30.417, 35.151 · versículo 31
- Maacah · 33.258, 35.581 · versículo 34
- Zobah · 33.935, 36.151 · versículo 36
- Ammon · 31.955, 35.934 · versículo 37
- Jattir · Hoje: Khirbet Attir · 31.352, 35.016 · versículo 38
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org