Nations Bible

2 Samuel 17

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Ahitofel ya ce wa Absalom, “Zan zaɓi mutum dubu goma sha biyu su fita a daren nan in fafari Dawuda. 2Zan fāɗa masa sa’ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya. Zan firgita shi, mutanen da suke tare da shi kuwa za su gudu. Sarki ne kaɗai zan kashe 3in dawo da dukan mutanen a gare ka. Mutuwar wanda kake nema zai zama dawowar duka; dukan mutanen ba za su cutu ba.”

4Wannan shawara ta gamshi Absalom da dukan dattawan Isra’ila.

5Amma Absalom ya ce, “A kira mini Hushai mutumin Arkitawan nan shi ma, mu ji abin da zai ce.” 6Da Hushai ya zo wurinsa, sai Absalom ya ce, “Ahitofel ya ba da wannan shawara. Mu yi abin da ya ce? In ba haka ba, sai ka ba mu ra’ayinka.”

7Hushai ya ce wa Absalom, “Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokaci kam, ba ta da kyau. 8Ka san mahaifinka da mutanensa mayaƙa ne, suna cikin fushi kamar mugun beyar da aka ƙwace mata ’ya’ya. Ban da haka ma, mahaifinka gogagge ne a yaƙi; ba zai kwana da rundunar ba. 9Kai, ko yanzu ma, ya riga ya ɓuya cikin kogo ko kuma a wani wuri. In har ya fara kai wa rundunarka hari duk wanda ya ji, zai ce, ‘An yi kaca-kaca da rundunar da suka bi Absalom.’ 10Kai, ko jarumi mai zuciya kamar na zaki ma, zai narke don tsoro, gama dukan Isra’ila sun sani mahaifinka mayaƙi ne, sun kuma san cewa waɗanda suke tare da shi jarumawa ne.

11“Saboda haka ina ba ka shawara, bari a tara maka dukan Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba da yawansu ya yi kamar yashin bakin teku, kai kanka ka jagorance su zuwa fagen fama. 12Sa’an nan za mu fāɗa masa duk inda yake, za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa. Da shi da mutanensa babu ko ɗaya da za a bari da rai. 13In ma ya janye zuwa cikin birni, sai dukan Isra’ila su kawo igiyoyi wa wannan birni, su ja shi zuwa kwari yă wargaje, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”

14Absalom da dukan mutanen Isra’ila suka ce, “Shawarar Hushai mutumin Arkitawa ta fi ta Ahitofel kyau.” Gama Ubangiji ya ƙudura yă wofinta kyakkyawar shawarar Ahitofel, don yă jawo wa Absalom masifa.

15Hushai ya ce wa Zadok da Abiyatar, firistoci, “Ahitofel ya ba wa Absalom da dattawan Isra’ila shawara su yi kaza da kaza, amma na ba su shawara su yi haka, su yi haka. 16Yanzu sai ku aika wa Dawuda saƙo nan da nan ku ce masa, ‘Kada ka kwana a mashigai cikin hamada; ka tabbata ka haye ba faci, in ba haka ba sarki da dukan mutanensa za su hallaka.’ ”

17Yonatan da Ahimawaz suna zaune a En Rogel. Wata baranya ce za tă je ta faɗa musu, su kuma su tafi su gaya wa Sarki Dawuda don suna tsoro kada a ga suna shiga birnin. 18Amma wani saurayi ya gan su, ya gaya wa Absalom. Sai dukansu biyu suka tashi da sauri suka shiga gidan wani mutum a Bahurim. Yana da rijiya a cikin gida, sai suka shiga cikinta. 19Matarsa mutumin kuwa ta kawo tabarma ta shimfiɗa a bakin rijiyar, sai ta kawo hatsi ta baza a kanta. Ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.

20Da mutanen Absalom suka zo wurin matan a gidan, suka ce, “Ina Yonatan da Ahimawaz?”

Matar ta ce, “Tuni, sun haye rafi.” Sai mutanen suka yi ta nemansu amma ba su ga kowa, sai suka koma Urushalima.

21Bayan mutanen suka tafi, sai su biyun suka fito daga rijiyar suka je suka gaya wa Sarki Dawuda. Suka ce masa, “Maza ka ƙetare kogi; Ahitofel ya ba wa Absalom shawara a yi maka kaza da kaza.” 22Saboda haka Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka tashi suka ƙetare Urdun. Kafin wayewar gari, babu wanda ya rage da bai haye ba.

23Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya hau jakinsa ya koma gidansa a garinsu. Ya kintsa gidansa sa’an nan ya rataye kansa. Ta haka ya mutu, aka kuma binne shi a kabarin mahaifinsa.

24Dawuda kuwa ya tafi Mahanayim. Absalom kuma ya ƙetare Urdun tare da dukan mutanen Isra’ila. 25Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab. 26Isra’ilawa da Absalom suka kafa sansani a ƙasar Gileyad.

27Sa’ad da Dawuda ya zo Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabba ta Ammonawa, da Makir ɗan Ammiyel daga Lo Debar, da Barzillai mutumin Gileyad daga Rogelim 28suka kawo wa Dawuda da mutanensa tabarmai, da kwanoni, da kayayyakin da aka yi da yumɓu. Suka kuma kawo alkama da sha’ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa, 29da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu wa Dawuda da mutanensa su ci. Gama sun ce, “Mutanen suna jin yunwa, sun kuma gaji, ga ƙishirwa a hamada.”

Você sabia?

Conselhos Conflitantes e a Fuga de Davi

  • Husai aconselhou intencionalmente Absalão a adiar o ataque e reunir todo o Israel "desde Dã até Berseba", uma expressão tradicional que designava toda a extensão da terra. Esse atraso estratégico frustrou o plano de Aitofel de um ataque imediato e deu ao rei Davi tempo suficiente para conduzir seu povo através do rio Jordão.Fontes: o próprio texto bíblico · Hushai · Beersheba
  • Para transmitir informações a Davi, os jovens sacerdotes Aimaás e Jônatas posicionaram-se na fonte de En-Rogel, fora de Jerusalém. Quando os espias de Absalão os avistaram, os mensageiros esconderam-se dentro de um poço num pátio em Baurim, onde uma moradora os ocultou sob uma cobertura estendida com grãos espalhados.Fontes: o próprio texto bíblico · Ahimaaz · Jonathan · Bahurim
  • Após atravessar o Jordão, Davi encontrou refúgio em Maanaim, uma cidade fortificada a leste do rio. Ali, líderes locais proeminentes abasteceram o exausto grupo real com camas, vasilhas e alimentos como lentilhas, grãos tostados, mel e queijo.Fontes: o próprio texto bíblico · Mahanaim

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Dan · Hoje: Tel Dan · 33.249, 35.652 · versículo 11
  • Jordan · Hoje: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículos 16, 21, 22, 24
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 20
  • Gilead · Hoje: Gilead 1 · 32.187, 35.692 · versículos 26, 27
  • Ammon · 31.955, 35.934 · versículo 27
  • Rabbah · Hoje: Amman · 31.955, 35.934 · versículo 27

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.