Nations Bible

2 Crônicas 32

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

Sennakerib ya yi wa Urushalima barazana

1Bayan dukan abin da Hezekiya ya yi cikin aminci, sai Sennakerib sarkin Assuriya ya zo ya yaƙi Yahuda. Ya yi kwanto wa biranen katanga, yana zato zai ci su da yaƙi wa kansa. 2Sa’ad da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo yana kuma niyya yă yaƙi Urushalima, 3sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi. 4Sai babban taro suka haɗu suka datse dukan maɓulɓulai da rafuffukan da suke gudu cikin ƙasar. Suka ce “Me zai sa sarakunan Assuriya su zo su sami ruwa barkatai?” 5Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.

6Ya naɗa manyan hafsoshi a kan mutane, ya tattara su a gabansa a fili a ƙofar birni, ya kuma ƙarfafa su da waɗannan kalmomi. 7“Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Assuriya, da mayaƙan nan masu yawa da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su. 8Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.

9Daga baya, sa’ad da Sennakerib sarkin Assuriya da dukan mayaƙansa suke kwanto wa Lakish, sai ya aiki hafsoshinsa da wannan saƙo wa Hezekiya sarkin Yahuda da kuma wa dukan mutanen Yahuda waɗanda suke can cewa,

10“Ga abin da Sennakerib sarkin Assuriya ya ce ga me kake dogara, har da ka dāge cikin Urushalima da aka yi mata kwanto? 11Ai, Hezekiya, ruɗinku yake yi, don yă sa ku mutu da yunwa da ƙishirwa sa’ad da yake ce muku, ‘ Ubangiji Allahnmu zai cece mu daga hannun sarkin Assuriya.’ 12Hezekiya kansa bai rushe waɗannan masujadan kan tudu da bagadai, yana ce wa Yahuda da Urushalima, ‘Dole ku yi sujada a gaban bagade guda ku kuma ƙone hadayu a kansa ba’?

13“Ba ku san abin da ni da kuma kakannina suka yi wa dukan mutanen sauran ƙasashe ba? Allolin ƙasashen nan sun taɓa iya ceton ƙasarsu daga hannuna ne? 14Wanne a cikin dukan allolin waɗannan ƙasashe da kakannina suka hallaka ya taɓa iya ceton mutanensa daga gare ni? To, yaya Allahnku zai iya cetonku daga hannuna? 15Yanzu fa, kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku yă kuma ɓad da ku haka. Kada ku gaskata shi, gama babu allahn wata ƙasa ko masarautar da ya taɓa iya ceton mutanensa daga hannuna ko kuwa hannun kakannina. Balle har Allahnku yă cece ku daga hannuna!”

16Hafsoshin Sennakerib suka ci gaba da maganar banza wa Ubangiji Allah da kuma a kan bawansa Hezekiya. 17Sarki ya kuma rubuta wasiƙu yana zagin Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana faɗin wannan a kansa, “Kamar yadda sauran allolin mutanen sauran ƙasashe ba su iya kuɓutar da mutane daga hannuna ba, haka Allahn Hezekiya ba zai kuɓutar da mutanensa daga hannuna ba.” 18Sa’an nan suka yi magana da ƙarfi cikin Yahudanci wa mutanen Urushalima waɗanda suke kan katanga, don su firgita su, su kuma sa su ji tsoro don su iya cin birnin. 19Suka yi magana game da Allah na Urushalima yadda suka yi game da allolin sauran mutanen duniya, aikin hannuwan mutane.

20Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz suka yi kuka cikin addu’a ga sama game da wannan. 21Sai Ubangiji ya aiki mala’ika, wanda ya karkashe dukan jarumawa da shugabanni da kuma hafsoshi a sansanin sarkin Assuriyawa. Saboda haka sai sarkin Assuriya ya janye zuwa ƙasarsa da kunya. Da ya shiga haikalin Allahnsa, sai waɗansu a cikin ’ya’yansa maza suka yanka shi da takobi.

22Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mutanen Urushalima daga hannun Sennakerib sarkin Assuriya da kuma daga hannun dukan sauran. Ya magance su a kowane gefe. 23Yawanci mutane suka kawo hadayun ƙonawa zuwa Urushalima wa Ubangiji da kuma kyautai masu daraja wa Hezekiya sarkin Yahuda. Daga lokacin zuwa gaba dukan ƙasashe suka girmama shi.

Girmankai, nasara da kuma mutuwar Hezekiya

24A kwanakin nan Hezekiya ya yi ciwo, ya yi kusan mutuwa. Sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wanda ya amsa masa ya kuma ba shi alama. 25Amma zuciyar Hezekiya ta yi girman kai, bai kuwa yi amfani da alherin da aka nuna masa ba, saboda haka fushin Ubangiji ya sauko a kansa da kuma a kan Yahuda da Urushalima. 26Sai Hezekiya ya tuba daga girma kan zuciyarsa, haka ma mutanen Urushalima; saboda haka fushin Ubangiji bai zo a kansu a kwanakin Hezekiya ba.

27Hezekiya mai arziki da girma ne ƙwarai, ya kuma yi baitulmali domin azurfa da zinariyarsa da kuma domin duwatsu masu daraja, kayan yaji, garkuwoyi da kuma domin dukan kayayyaki masu daraja nasa. 28Ya kuma yi gine-gine domin ajiyar hatsi, sabon ruwa inabi da mai; ya kuma yi wuraren ajiyar kowane irin shanu dabam-dabam, da kuma turke domin tumaki. 29Ya gina ƙauyuka ya kuma samo shanu da garkuna masu yawa, gama Allah ya ba shi arziki mai yawa sosai.

30Hezekiya ne ya datse ruwan bisa na maɓulɓular Gihon, ya sa ruwan ya gangara zuwa gefe yamma na Birnin Dawuda. Ya yi nasara a kome da ya yi. 31Amma da masu mulkin Babilon suka aika da jakadu su tambaye shi game alamar da ta faru a ƙasar, Allah ya rabu da shi don yă gwada shi don yă kuma san kome da yake cikin zuciyarsa.

32Sauran ayyukan mulkin Hezekiya da kuma kyawawa ayyukansa, suna a rubuce a cikin wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila. 33Hezekiya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a kan tudu inda makabartan zuriyar Dawuda suke. Dukan Yahuda da kuma mutanen Urushalima suka girmama shi sa’ad da ya mutu. Sai Manasse ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

A invasão de Senaqueribe e o livramento

  • Diante da ameaça do cerco assírio, Ezequias e seus líderes taparam todas as fontes naturais fora de Jerusalém para privar os invasores de água. O rei também canalizou as águas da fonte superior de Giom diretamente para o lado ocidental da Cidade de Davi, assegurando o abastecimento interno da cidade.Fontes: o próprio texto bíblico · Gihon
  • Enquanto Senaqueribe sitiava a fortaleza judaica de Laquis, ele enviou emissários a Jerusalém para desmoralizar os defensores. Os mensageiros assírios gritaram em alta voz em hebraico para o povo que vigiava sobre as muralhas da cidade, tentando aterrorizá-los para que se rendessem.Fontes: o próprio texto bíblico · Lachish · Sennacherib
  • Em resposta às ameaças assírias, o rei Ezequias e o profeta Isaías, filho de Amoz, uniram-se em oração ao céu por livramento. O relato bíblico registra que outros detalhes do reinado e da devoção de Ezequias foram preservados na visão de Isaías, nos anais reais.Fontes: o próprio texto bíblico · Isaiah · Amoz

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Assyria · 36.359, 43.153 · versículos 1, 4, 7, 9, 10, 11, 13, 21, 22
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 2, 9, 10, 12, 18, 19, 22, 23, 25, 26, 33
  • City of David · 31.774, 35.236 · versículos 5, 30
  • Lachish · Hoje: Tell ed Duweir · 31.565, 34.849 · versículo 9
  • Gihon · Hoje: Gihon Spring · 31.773, 35.236 · versículo 30
  • Babylon · 32.543, 44.422 · versículo 31

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.