1 Crônicas 24
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Sassan firistoci
1Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza.
’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar. 2Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci. 3Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima. 4Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar. 5Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.
6Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
7Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib,
na biyu a kan Yedahiya,
8na uku a kan Harim,
na huɗu a kan Seyorim,
9na biyar a kan Malkiya,
na shida a kan Miyamin,
10na bakwai a kan Hakkoz,
na takwas a kan Abiya,
11na tara a kan Yeshuwa,
na goma a kan Shekaniya,
12na goma sha ɗaya a kan Eliyashib,
na goma sha biyu a kan Yakim,
13na goma sha uku a kan Huffa,
na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,
14na goma sha biyar a kan Bilga,
na goma sha shida a kan Immer,
15na goma sha shida a kan Hezir,
na goma sha takwas a kan Haffizzez,
16na goma sha tara a kan Fetahahiya,
na ashirin a kan Ezekiyel,
17na ashirin da ɗaya wa Yakin,
na ashirin da biyu a kan Gamul,
18na ashirin da uku wa Delahiya
da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya.
19Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.
Sauran Lawiyawa
20Game da sauran zuriyar Lawi kuwa,
Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel;
daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.
21Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.
22Daga mutanen Izhar, Shelomot;
daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.
23’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
24Ɗan Uzziyel shi ne, Mika;
daga ’ya’yan Mika maza, Shamir.
25Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya;
daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.
26’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi.
Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.
27’Ya’yan Merari su ne,
daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.
28Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza.
29Daga Kish, ɗan Kish shi ne,
Yerameyel.
30Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot.
31Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.

Você sabia?
Organização dos sacerdotes e levitas
- Como os dois filhos mais velhos de Arão, Nadabe e Abiú, morreram sem filhos após oferecerem fogo estranho, apenas as linhagens de Eleazar e Itamar continuaram o sacerdócio. O rei Davi organizou esses descendentes em vinte e quatro turnos de serviço, sendo dezesseis de Eleazar e oito de Itamar.Fontes: o próprio texto bíblico · Eleazar · Ithamar · Nadab
- Para garantir a imparcialidade entre as duas linhagens, a ordem das escalas foi determinada por sorteio diante do rei Davi, de Zadoque e de Aimeleque. O escriba Semaías, um levita, registrou formalmente o nome de cada família à medida que o lote era sorteado.Fontes: o próprio texto bíblico · Zadok · Ahimelech
- Os demais clãs levitas, incluindo os descendentes de Coate e Merari, também foram organizados e designados para suas funções mediante sorteio. O processo tratou com igualdade tanto os chefes de famílias quanto seus irmãos mais jovens.Fontes: o próprio texto bíblico · Merari
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Holy Place · Hoje: on Mount Moriah · 31.778, 35.236 · versículo 5
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org