Nations Bible

1 Crônicas 16

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

Yin hidima a gaban akwatin alkawari

1Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah. 2Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji. 3Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.

4Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila. 5Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna, 6Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.

Zaburar Dawuda ta godiya

7A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.

8Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa;

ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.

9Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;

ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.

10Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki

bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.

11Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;

ku nemi fuskarsa kullum.

12Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata,

mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,

13Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa,

Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.

14Shi ne Ubangiji Allahnmu;

hukuntansa suna a cikin dukan duniya.

15Yakan tuna da alkawarinsa har abada,

maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,

16alkawarin da ya yi wa Ibrahim

rantsuwar da ya yi ga Ishaku.

17Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida,

ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.

18“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana

kamar rabon da za ka gāda.”

19Sa’ad da suke kima,

kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,

20suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma,

daga wannan mulki zuwa wancan.

21Bai bar wani ya zalunce su ba;

saboda su ya tsawata wa sarakuna.

22“Kada ku taɓa shafaffuna;

kada ku yi wa annabawana lahani.”

23Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka;

ku yi shelar cetonsa kowace rana.

24Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,

ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.

25Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo;

dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

26Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,

amma Ubangiji ya yi sammai.

27Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;

ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.

28Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai,

ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,

29ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa.

Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa;

ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.

30Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka!

Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.

31Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;

bari su ce a cikin al’ummai, “ Ubangiji yana mulki!”

32Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri;

bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!

33Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,

za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji,

gama ya zo don yă hukunta duniya.

34Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;

ƙaunarsa madawwamiya ce.

35Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;

tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai,

don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki,

don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”

36Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,

daga madawwami zuwa madawwami.

Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”

37Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana. 38Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.

39Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon 40don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila. 41Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” 42Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.

43Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Adoração e ações de graças diante da arca

  • Enquanto a arca da aliança foi colocada em uma tenda em Jerusalém sob o ministério diário de Asafe e seus companheiros levitas, o tabernáculo e o altar de holocaustos permaneceram no lugar alto em Gibeom, onde o sacerdote Zadoque, Hemã e Jedutum mantinham os sacrifícios matutinos e vespertinos segundo a lei.Fontes: o próprio texto bíblico · Gibeon · Heman · Jeduthun (Ethan)
  • Davi instituiu uma ordem formal de músicos levitas com harpas, liras, címbalos e trombetas, nomeando Asafe como músico principal. Mais tarde, a tradição bíblica atribui vários salmos (Salmos 50 e 73–83) a Asafe e o reconhece como músico e vidente.Fontes: o próprio texto bíblico · Asaph (Levite)
  • Após os sacrifícios e bênçãos pela chegada da arca, Davi ofereceu uma refeição comemorativa para toda a congregação, distribuindo um pão, um bolo de tâmaras e um bolo de passas para cada homem e mulher presente.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Canaan · 32.767, 35.333 · versículos 18, 19
  • Gibeon · Hoje: El Jib · 31.847, 35.183 · versículo 39

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.