Romanos 7
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1'Yan'uwa, ko baku sani ba (domin ina magana da wadanda suka san shari'a), cewar shari'a na mulkin mutum muddin ransa? 2Domin ta wurin shari'a matar aure a daure take muddin mijinta nada rai, amma idan mijinta ya mutu, ta kubuta daga shari'ar aure. 3To don haka idan, mijinta na da rai, sai ta tafi ta zauna da wani mutumin, za'a kirata mazinaciya. Amma idan mijin ya mutu, ''yantarciya ce daga shari'a, domin kada ta kasance mazinaciya idan ta auri wani mutum. 4Domin wannan, 'yan'uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari'a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah 'ya'ya. 5Domin sa'adda muke cikin jiki, ana motsa dabi'armu ta zunubi dake cikin jikunan mu ta wurin shari'a domin mu haifi 'ya'ya zuwa mutuwa. 6Amma yanzu an kubutar damu daga shari'a, mun mutu daga abin da ya daure mu, domin mu yi bauta cikin sabuntuwar Ruhu, ba cikin tsohon rubutun shari'a ba. 7To me zamu ce kenan? ita shari'ar kanta zunubi ce? ba zai taba faruwa ba. Duk da haka. Idan ba ta wurin shari'a ba, ba zan taba sanin zunubi ba, in ba ta wurin shari'a ba. Ba zan taba kyashin abin wani ba, har sai da shari'a tace, “Kada kayi kyashi.” 8Amma zunubi, sai ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya jawo dukkan sha'awa dake cikina. Domin in da babu shari'a, zunubi matacce ne. 9Ada na rayu sau daya ba tare da shari'a ba, amma da dokar ta zo, sai zunubi ya farfado, ni kuma na mutu. 10Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya. 11Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni. 12Domin haka, shari'ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau. 13To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi. 14Domin mun san shari'a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi. 15Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa. 16Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari'a kenan, cewar shari'a nada kyau. 17Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina. 18Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa. 19Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa. 20To idan na yi abin da ba ni so in aikata, wato kenan ba ni bane ke aikatawa, amma zunubin da ke zaune a cikina. 21Don haka, sai na iske, akwai ka'ida a cikina dake son aikata abu mai kyau, amma kuma ainihin mugunta na tare dani. 22Domin a cikina ina murna da shari'ar Allah. 23Amma ina ganin wasu ka'idoji daban a gabobin jikina, su na yaki da wannan sabuwar ka'idar da ke cikin tunanina, suna kuma sanya ni bauta ta wurin ka'idar zunubi wadda ke cikin gabobin jikina. 24Ni wahalallen mutum ne! wa zai kubutar dani daga wannan jiki na mutuwa? 25Amma godiya ga Allah ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Domin haka ni kaina a wannan hannu bisa ga tunani na ina bautawa shari'ar Allah. Duk da haka, ta wani gefen ina bautawa ka'idar zunubi da ke tare da jikina.
¿Sabías que…?
La autoridad de la ley y el conflicto interior
- Este capítulo afirma que la ley tiene autoridad sobre una persona solo mientras esa persona vive. Lo explica con el matrimonio: la mujer está ligada por la ley a su esposo mientras él vive, pero si él muere, es liberada de la ley del matrimonio y no es llamada adúltera aunque se case con otro hombre. El autor dice entonces que sus hermanos también murieron a la ley por medio del cuerpo de Cristo, para pertenecer a aquel que fue resucitado de entre los muertos, dar fruto para Dios y servir en el nuevo camino del Espíritu, y no en el antiguo camino del código escrito.Fuentes: el propio texto bíblico
- Cuando el autor pregunta si la ley es pecado, responde: "¡Ciertamente no!" Dice que no habría sido consciente de la codicia si la ley no hubiera dicho: "No codiciarás", y que el pecado, apoderándose de la oportunidad por medio del mandamiento, produjo en él toda clase de deseo codicioso. Llama a la ley santa, y al mandamiento santo, justo y bueno, mientras afirma que el pecado produjo muerte en él por medio de lo que era bueno, para que el pecado quedara expuesto como pecado y llegara a ser totalmente pecaminoso.Fuentes: el propio texto bíblico
- El autor dice que la ley es espiritual, pero que él no es espiritual, vendido como esclavo al pecado: no hace el bien que quiere y sigue haciendo el mal que odia. En su ser interior se deleita en la ley de Dios, pero otra ley que obra en su cuerpo hace guerra contra la ley de su mente y lo mantiene cautivo de la ley del pecado que habita en él. Pregunta quién lo rescatará de este cuerpo de muerte, da gracias a Dios por medio de Jesucristo nuestro Señor, y concluye que con la mente sirve a la ley de Dios, pero con la carne sirve a la ley del pecado.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org