Nations Bible

Romanos 4

Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

1Me kenan zamu ce game da Ibrahim, kakanmu a jiki, me ya samu? 2Domin idan Ibrahim ya sami kubutarwa ta wurin ayuka, ai da ya sami dalilin fahariya, amma ba a gaban Allah ba. 3Kuma fa me nassi ke fadi? “Ibrahim ya bada gaskiya ga Allah, sai aka lisafta ta adalci gare shi.” 4Yanzu fa shi dake yin ayyuka, ladansa ba a lisafta shi alheri ba ne, amma abun da ke nasa. 5Amma kuma shi da bai da ayyuka kuma maimakon haka ya gaskanta ga wanda ke kubutar da masu zunubai, bangaskiyarsa an lisafta ta a misalin adalci. 6Dauda ya yi furcin albarka bisa mutumin da Allah ya lisafta mai adalci da rashin ayyuka. 7Sai ya ce, “Masu albarka ne wadanda aka yafe laifofinsu, kuma wadanda zunubansu a rufe suke. 8Mai albarka ne mutumin da ko kadan Ubangiji ba zaya lisafta zunubin sa ba.” 9To albarkar da aka fadi ko a bisansu wadanda aka yi wa kaciya ne kadai, ko kuwa a bisan su ma marasa kaciya? Domin mun yi furcin, “Bangaskiyar Ibrahim an lisafta ta adalci ce agare shi.” 10Yaya aka lisafta ta? Bayan Ibrahim ya yi kaciya, ko kuwa a rashin kaciya? Ba a cikin kaciya ba, amma a rashin kaciya. 11Ibrahim ya amshi alamar kaciya. Wannan shi ne hatimin adalcin bangaskiyar da ya ke da ita tun cikin rashin kaciyarsa. Albarkacin wannan alama ce, ta sa shi ya zama uban dukkan wadanda suka badagaskiya, ko da shike ba su da kaciya. Wato ma'ana, adalci za a lisafta masu. 12Wannan kuma yana da ma'anar cewa Ibrahim ya zama uban kaciya ga wadanda suka fito ba domin masu kaciya kadai ba, amma kuma domin wadanda ke biyo matakin ubanmu Ibrahim. Kuma wannan itace bangaskiyar da ya ke da ita a rashin kaciya. 13Domin ba ta wurin shari'a aka bada alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa ba, wannan alkawarin da ya ce zasu gaji duniya. Maimako, a ta wurin adalcin bangaskiya ne. 14Domin idan su da ke na shari'a magada ne, bangaskiya bata da komai, kuma alkawarin an wofintar da shi kenan. 15Domin shari'a ta kan jawo fushi, amma ta wurin rashin shari'a, babu karya umarni. 16Saboda wannan dalili haka ta faru ta wurin bangaskiya, domin ya zama bisa ga alheri. Kamar haka, alkawarin ya tabbata ga dukkan zuriya. Kuma wannan zuriya ba zata kunshi wadanda suke da sanin shari'a ba kadai, har ma da wadanda ke daga bangaskiyar Ibrahim. Saboda shi ne uban dukkan kowa, 17kamar yadda aka rubuta, “Na maishe ka uba ga kasashe masu yawa.” Ibrahim na gaban aminin sa, wato, Allah, mai bada rai ga mattatu kuma ya kan kira abubuwan da basu da rai su kuma kasance. 18Duk da halin da ke a bayyane, Ibrahim ya gaskata ga Allah kai tsaye game da abubuwan da ke nan gaba. Sai ya zama uba ga kasashe masu yawa, kamar yadda aka ambata, “... Haka zuriyarka zata kasance.” 19Ba ya karaya a bangaskiya ba. Ibrahim ya yarda da cewa jikinsa ya rigaya ya tsufa (shekarun sa na misalin dari). Ya kuma yarda da cewa mahaifar Saratu bata iya bada 'ya'ya ba. 20Amma domin alkawarin Allah, Ibrahim bai ji nauyin rashin bangaskiya ba. Maimakon haka, ya sami karfafawa a bangaskiyarsa sai ya daukaka Allah. 21Ya na da cikakkiyar gamsuwa cewa idan Allah ya yi alkawari, shi mai iya kammalawa ne. 22Haka nan ne kuma aka lisafta masa wannan a matsayin adalci. 23To ba'a rubuta kawai damin amfaninsa kadai ba, da aka lisafta dominsa. 24A rubuce yake domin mu, domin wadanda za'a lisafta su, mu da muka bada gaskiya gare shi wanda ya tada Yesu Ubangijinmu daga matattu. 25Wannan shi ne wanda aka bashe shi domin zunubanmu kuma an tada shi saboda fasar mu.

¿Sabías que…?

La fe de Abraham acreditada como justicia

  • El Diccionario Bíblico de Easton (1897) explica el nombre Abraham como "padre de una multitud". Este capítulo cita la promesa "Te he hecho padre de muchas naciones" y lo llama padre de todos los que creen, estén circuncidados o no.Fuentes: Abraham · el propio texto bíblico
  • Este capítulo subraya que la fe de Abraham le fue acreditada como justicia antes de ser circuncidado, y no después. La circuncisión se describe como señal y sello de esa justicia, así que él es padre tanto de los creyentes incircuncisos como de los circuncidados que siguen la misma fe.Fuentes: el propio texto bíblico
  • El Diccionario Bíblico de Easton (1897) explica el nombre Sara como "princesa" y dice que se lo dieron cuando se anunció que ella sería la madre del hijo prometido. Este capítulo recuerda a Abraham, de unos cien años, creyendo la promesa de Dios aunque el vientre de Sara estaba sin vida.Fuentes: Sarah · el propio texto bíblico

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.