Nations Bible

Romanos 14

Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

1Ku karbi duk wanda yake da rarraunar bangaskiya, ba tare da sukar ra'ayinsa ba. 2Wani yana da bangaskiyar yaci komai, wani wanda yake da rauni yakanci ganye ne kawai. 3Kada wanda yake cin komai ya raina wanda baya cin kowanne abu. Kada kuma wanda baya cin kowanne abu ya shara'anta sauran da suke cin komai. Saboda Allah ya karbe shi. 4Kai wanene, kai wanene da kake ganin laifin bawan wani? Tsayawarsa ko faduwarsa ai hakin maigidansa ne, amma Ubangiji yana da ikon tsai da shi. 5Wani yakan daukaka wata rana fiye da sauran. Wani kuma yana daukan ranakun daidai. Kowa ya zauna a cikin hakakkewa akan ra'ayinsa. 6Shi wanda ya kula da wata rana, ya kula da ita don Ubangiji. Kuma wanda yaci, yaci ne domin Ubangiji, domin yana yi wa Allah godiya. Shi wanda bai ci ba, yaki ci ne domin Ubangiji. Shima yana yi wa Allah godiya. 7Domin babu wanda yake rayuwa don kansa a cikinmu, kuma babu mai mutuwa don kansa. 8Domin in muna raye, muna raye don Ubangiji. Kuma in mun mutu, mun mutu ne don Ubangiji. Ashe, ko muna raye, ko a mace mu na Ubangiji ne. 9Domin wannan dalilin Almasihu ya mutu ya kuma tashi, saboda ya zama Ubangiji ga matattu da rayayyu. 10Amma ku don me kuke shara'anta yan'uwanku? kai kuma don me kake raina dan'uwanka? Dukan mu zamu tsaya gaban kursiyin shari'ar Allah. 11Domin a rubuce yake, “ Na rantse, “inji Ubangiji”, kowacce gwiwa zata rusuna mani, kowanne harshe kuwa zai yabi Allah.” 12Domin kowannenmu zai fadi abin da shi yayi da bakinsa a gaban Allah. 13Saboda da haka kada muyi wa juna shari'a, amma maimakon haka ku dauki wannan kudduri, don kada kowa ya zama sanadin tuntunbe ko faduwa ga dan'uwansa. 14Na sani na kuma tabbata tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake mara tsarki ga asalinsa. Sai dai ga wanda ya dauke shi marar tsarki ne yake zama marar tsarki. 15Idan har abincinka na cutar da dan'uwanka, ba ka tafiya cikin kauna. Kada ka lalata wanda Yesu ya mutu domin sa da abincinka. 16Saboda haka, kada abubuwan da aka dauka kyawawa su zama abin zargi ga wadansu. 17Saboda mulkin Allah ba maganar ci da sha ba ne, amma game da adalci ne, salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki. 18Domin wanda yake bautar Almasihu a wannan hanya, karbabbe ne ga Allah, kuma jama'a sun yarda da shi. 19Don haka, mu nemi abubuwa na salama da abubuwan da zasu gina juna. 20Kada ku lalata aikin Allah don abinci. Komai yana da tsarki, amma kaiton mutumin da yake cin abin da zai sa shi ya fadi. 21Bashi da kyau a ci nama ko a sha ruwan inabi, ko duk abin da zai jawo faduwar dan'uwanka. 22Wannan bangaskiyar da kuke da ita, ku adana ta tsakaninku da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa bata da laifi akan abin da hankalinsa ya ga daidai ne. 23Duk wanda yayi shakka amma kuma yaci, ya sani yayi laifi kenan, domin ba tare da bangaskiya bane. Duk abin da ba na bangaskya bane zunubi ne.

¿Sabías que…?

La comida, los días y no juzgarse unos a otros

  • Este capítulo vincula la fe débil con decisiones concretas: una persona tiene fe para comer de todo, mientras otra, que es débil, come solo verduras, y una persona considera cierto día por encima de los demás, mientras otra estima iguales todos los días. Quien come de todo no debe menospreciar a quien no come, y quien no come no debe juzgar a quien come, porque Dios lo ha aceptado.Fuentes: el propio texto bíblico
  • Ya sea que alguien coma o se abstenga, u observe un día especial, el capítulo dice que cada uno lo hace para el Señor y da gracias a Dios. Nadie vive ni muere solo para sí: si vivimos, vivimos para el Señor, y si morimos, morimos para el Señor, pues Cristo murió y volvió a la vida para ser Señor tanto de los muertos como de los vivos.Fuentes: el propio texto bíblico
  • El capítulo afirma una convicción personal de que nada es impuro en sí mismo, pero que si alguien considera algo impuro, entonces para esa persona lo es. Es mejor no comer carne ni beber vino que hacer tropezar al hermano, porque el reino de Dios no es cuestión de comer y beber, sino de justicia, paz y alegría en el Espíritu Santo.Fuentes: el propio texto bíblico

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.