Romanos 12
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Ina rokon ku 'yan'uwa, saboda yawan jinkan nan na Allah, da ku mika jikunanku hadaya mai rai, mai tsarki kuma abar karba ga Allah. wannan itace hidimarku ta zahiri. 2Kada ku kamantu da wannan duniya, amma ku sami canzawa ta wurin sabunta tunaninku, kuyi haka don ku san abin da ke nagari, karbabbe, kuma cikakken nufin Allah. 3Don ina cewa, saboda alherin da aka bani, ka da waninku ya daukaka kansa fiye da inda Allah ya ajiye shi; a maimakon haka ku kasance da hikima, gwargwadon yadda Allah yaba kowa bangaskiya. 4Domin muna da gababuwa da yawa a jiki daya, amma ba dukansu ne ke yin aiki iri daya ba. 5haka yake a garemu, kamar yadda muke da yawa haka cikin jikin Almasihu, dukkanmu gabobin juna ne. 6Muna da baye-baye dabam-dabam bisa ga alherin da aka bayar a gare mu. Idan baiwar wani anabci ne, yayi shi bisa ga iyakar bangaskiyarsa. 7In wani yana da baiwar hidima, sai yayi hidimarsa. Idan baiwar wani koyarwa ce, yayi koyarwa. 8Idan baiwar wani karfafawa ce, yayi ta karfafawa; Idan baiwar wani bayarwa ce, yayi ta da hannu sake; Idan baiwar wani shugabanci ne, yayi shi da kula; Idan baiwar wani nuna jinkai ne, yayi shi da sakakkiyar zuciya. 9Ku nuna kauna ba tare da riya ba. Ku Ki duk abin da ke mugu ku aikata abin da ke nagari. 10Akan kaunar 'yan'uwa kuma, ku kaunaci juna yadda ya kamata; akan ban girma kuma, ku ba juna girma. 11Akan himma kuma, kada ku yi sanyi; akan ruhu kuma, ku sa kwazo; Game da Ubangiji kuma, ku yi masa hidima. 12Akan gabagadi kuma, ku yi shi da farin ciki; akan tashin hankali kuma, ku cika da hakuri; akan adu'a kuma, ku nace. 13Ku zama masu biyan bukatar tsarkaka, ku zama masu karbar baki a gidajenku. 14Ku albarkaci masu tsananta maku, kada ku la'anta kowa. 15Ku yi farinciki tare da masu farinciki; Ku yi hawaye tare da masu hawaye. 16Tunanin ku ya zama daya. Kada tunaninku ya zama na fahariya, amma ku yi abokantaka da matalauta. Kada wani a cikin ku ya kasance da tunanin yafi kowa. 17Kada ku rama mugunta da mugunta. Ku yi ayukan nagarta a gaban kowa. 18Ku yi duk abin da za ku iya yi domin ku yi zaman salama tare da kowa. 19'Yan'uwa, kada ku yi ramako, ku bar Allah ya rama maku. A rubuce yake, '' 'Ramako nawa ne; zan saka wa kowa,' in ji Ubangiji.'' 20''Amma idan makiyin ka na jin yunwa, ba shi abinci ya ci. Idan yana jin kishin ruwa, ba shi ruwan sha. Idan kun yi haka, garwashin wuta ne za ku saka akan duk makiyi.'' 21Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta ta wurin yin aikin nagarta.

¿Sabías que…?
Sacrificio vivo y un solo cuerpo
- Romanos 12 exhorta a los hermanos, a causa de la misericordia de Dios, a ofrecer sus cuerpos como sacrificios vivos, santos y agradables a Dios, y llama a esto su servicio espiritual de adoración. Esa imagen de un sacrificio que sigue vivo va junto al llamado a no conformarse a este mundo, sino a transformarse por la renovación de la mente, a fin de probar y aprobar cuál es la voluntad de Dios, buena, agradable y perfecta.Fuentes: el propio texto bíblico
- La comunidad se compara con un solo cuerpo de muchos miembros que no tienen todos la misma función: en Cristo los muchos son un solo cuerpo, y cada miembro pertenece a los demás. Los distintos dones se atribuyen a la gracia recibida —profecía, en proporción a la fe; servicio; enseñanza; aliento; dar con generosidad; dirigir con diligencia; y misericordia con alegría—, y a cada uno se le pide pensar con juicio sobrio, según la medida de fe que Dios le ha dado, y no más alto de lo que debe.Fuentes: el propio texto bíblico
- El capítulo prohíbe devolver mal por mal y vengarse, y dice a los amados que dejen lugar a la ira de Dios y, si es posible de su parte, vivan en paz con todos. Apela a lo que está escrito —que la venganza pertenece al Señor, quien retribuirá, y que al enemigo con hambre hay que darle de comer y al sediento de beber, lo cual amontonará brasas ardientes sobre su cabeza— y termina exhortando a no dejarse vencer por el mal, sino a vencer el mal con el bien.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org