Apocalipsis 5
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Sa'annan na ga a cikin hannun daman wanda ke zaune a kan kursiyin, na ga littafi wanda ke da rubutu ciki da waje, an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. 2Na kuma ga wani kakkarfan mala'ika na shela da murya mai karfi, “Wa ya isa ya bude littafin ya kuma bambare hatimin?” 3Ba wani a sama ko a kasa ko karkashin kasa da ya iya ya bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa. 4Na yi kuka mai zafi saboda ba wani da ya cancanta da zai bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa. 5Amma daya daga cikin dattawan nan ya ce mani, “Kada ka yi kuka. Duba! Zaki na kabilar Yahuza, Tushen Dauda, ya yi nasara. Ya cancanci bude littafin da kuma hatimansa bakwai.” 6Na ga Dan Rago yana tsaye tsakanin kursiyin da rayayyun halittun nan guda hudu a cikin dattawa. Yana kama da wanda aka kashe. Yana da kafonni bakwai da idanuwa bakwai; wadannan sune ruhohin Allah bakwai da aka aiko zuwa dukan duniya. 7Ya tafi ya karbi littafin daga hannun daman wanda ke zaune bisa kursiyin. 8Lokacin da Dan Ragon ya dauki littafin, rayayyun halittun nan hudu da dattawan nan ashirin da hudu suka fadi har kasa a gaban Dan ragon. Kowannen su na dauke da molo da tasar zinariya cike da kayan kamshi, wadanda kuwa sune addu'o'in masu ba da gaskiya. 9Suka raira sabuwar waka: “Ka cancanta ka dauki littafinka kuma bude hatimansa. Domin an yanka ka, da jininka ka saya wa Allah mutane daga kowacce kabila, harshe, jama'a da al'umma. 10Ka maishe su mulki da firistoci su bauta wa Allanmu, kuma za su yi mulki a duniya.” 11Da na duba sai na ji karar mala'iku masu yawa kewaye da kursiyin da rayayyun halitu da kuma dattawa. Jimillarsu ya kai dubbai goma, sau dubbai goma, da dubun dubbai. 12Suka tada murya da karfi suka ce, “Macancanci ne Dan Ragon da aka yanka ya karbi iko, wadata, hikima, karfi, girma, daukaka da yabo.” 13Na ji kowanne halittaccen abu da ke cikin sama da kasa da karkashin kasa da cikin teku - dukan abubuwan da ke cikinsu - na cewa, “Ga shi wanda ke zaune a kan kursiyin da kuma Dan Ragon, yabo, girma, daraja, da kuma ikon yin mulki, har abada abadin. 14Sai rayayyun halittun nan hudu suka ce, “Amin!” dattawan nan kuma suka fadi da fuskokinsu suka yi sujada.
¿Sabías que…?
El Cordero digno de abrir el rollo
- Uno de los ancianos dice al narrador, que lloraba, que no llore, porque el León de la tribu de Judá, la Raíz de David, ha triunfado para abrir el rollo y sus siete sellos. La entrada sobre David lo llama Amado y lo identifica como el octavo hijo y el menor de Isaí, ciudadano de Belén, que cuidaba las ovejas de su padre en las tierras altas de Judá.Fuentes: el propio texto bíblico · David
- Lo que se ve después no es un león, sino un Cordero que parecía haber sido muerto, de pie en el centro del trono, con siete cuernos y siete ojos. La visión misma dice que esos cuernos y ojos representan los siete Espíritus de Dios enviados por toda la tierra.Fuentes: el propio texto bíblico
- Cuando el Cordero toma el rollo, los cuatro seres vivientes y los veinticuatro ancianos se postran ante él; cada uno tiene un arpa, y ellos sostienen copas de oro llenas de incienso, que el pasaje identifica como las oraciones de los santos. El cántico nuevo dice que él fue muerto y que, con su sangre, compró para Dios a los que proceden de toda tribu, lengua, pueblo y nación.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org