Apocalipsis 17
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Daya daga cikin mala'ikun nan bakwai wanda ke rike da tasoshi bakwai ya zo ya ce mani, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwarnan da ke zaune a kan ruwaye masu yawa. 2Da ita ce sarakunan duniya suka yi fasikanci. Da ruwan inabinta na fasikanci marar dacewa ta sa mazaunan duniya suka bugu.” 3Sai mala'ikan ya dauke ni cikin Ruhu ya tafi da ni jeji, sai na ga mace zaune bisa jan dabba cike da sunayen sabo. Dabbar tana da kawuna bakwai da kahonni goma. 4Matar kuwa tana sanye da tufafi na shunayya da kuma jar garura, ta kuma ci ado da kayan zinariya da duwatsu masu tamani da lu'u-lu'ai. Tana rike da kokon zinariya a hannunta cike da abubuwan kyama da na kazantar fasikancinta marar dacewa. 5Bisa goshinta an rubuta wani suna mai boyayyar ma'ana: “Babila mai girma, uwar karuwai da na kazamtattun abubuwan duniya.” 6Sai na ga matar a buge da jinin masu ba da gaskiya da kuma jinin wadanda aka kashe su domin Yesu. Da na gan ta, na yi mamaki kwarai da gaske. 7Amma mala'ikan ya ce mani, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka ma'anar matar da kuma na dabbar da ke dauke da ita, dabban nan da ke da kawuna bakwai da kahonni goma. 8Dabban da ka gani da, yanzu ba ta, amma ta na kusan hawowa daga rami marar iyaka. Sa'annan za ta je hallaka. Wadanda ke zaune a duniya, wadanda ba a rubuta sunayensu cikin littafin rai ba tun kafuwar duniya - za su yi mamaki idan suka ga dabbar da da ta kasance, ba ta nan yanzu, amma ta kusa zuwa. 9Wannan al'amari na bukatar hikima. Kawunnan bakwai, tuddai ne bakwai da macen ke zaune a kai. 10Su kuma sarakuna ne bakwai. Sarakuna biyar sun fadi, daya na nan, amma dayan bai zo ba tukuna; sa'anda ya zo zai kasance na dan lokaci kadan. 11Dabban da ya kasance a da, amma yanzu ba shi, shi ma sarki ne na takwas; amma shi daya ne cikin sarakunan nan bakwai, kuma zai tafi hallaka. 12Kahonnin nan goma da ka gani sarakuna goma ne wadanda ba a nada su ba tukuna, amma za su karbi iko kamar na sarakai na sa'a daya tare da dabban. 13Ra'ayinsu daya ne, za su ba da sarautarsu da ikon su ga dabban. 14Za su yi yaki da Dan Rago. Dan Ragon zai ci nasara a kansu domin shi Ubangijin iyayengiji ne da Sarkin sarakuna - kuma tare da shi sune kirayayyun, zababbun, amintattun.” 15Mala'ikan ya ce mani, “Ruwayen da ka gani, inda karuwar ke zaune, jama'a ce, da taro masu dumbin yawa, da al'ummai da harsuna. 16Kahonnin nan goma da ka gani - su da dabban za su ki karuwar. Za su washe ta su tsiranceta, za su lankwame namanta, za su kone ta gaba daya da wuta. 17Gama Allah ya sa a zukantansu su yi nufinsa ta wurin amincewarsa, su sadaukar da ikonsu na yin mulki ga dabban har sai maganar Allah ta cika. 18Matar da ka gani ita ce babban birnin nan da ke mulki bisa sarakunan duniya.”
¿Sabías que…?
El misterio de Babilonia la Grande
- Un nombre misterioso está escrito en la frente de la mujer: Babilonia la Grande, madre de las prostitutas y de las abominaciones de la tierra. El ángel explica que la mujer es la gran ciudad que gobierna a los reyes de la tierra.Fuentes: el propio texto bíblico
- Una entrada sobre el lugar registra Babilonia como la forma griega de Babel, y la forma semítica Babilu con el significado de "La Puerta de Dios". También dice que, en las tablillas asirias, el nombre significa "la ciudad de la dispersión de las tribus". La misma entrada sitúa la ciudad junto al Éufrates, unas doscientas millas río arriba de la confluencia de ese río con el Tigris.Fuentes: Babylon
- El ángel interpreta imágenes de la visión. Las aguas donde está sentada la prostituta son pueblos, multitudes, naciones y lenguas. Las siete cabezas son siete montes sobre los que se sienta la mujer; el pasaje también habla de siete reyes, y los diez cuernos son diez reyes que aún no han recibido un reino.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Babylon · Hoy: Rome · 41.892, 12.485 · versículo 5
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org