Nations Bible

Marcos 7

Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

1Farisawa suka taru wurin Yesu tare da wadansu marubuta wadda suka zo daga Urushalima. 2Sun ga cewa wasu daga cikin almajiransa sun ci gurasa da hannuwa marasa tsabta, wato, basu wanke hannu ba, 3(Domin Farisawa da dukan Yahudawa ba su cin abinci sai dole sun wanke hannu da kyau domin suna kiyaye al'adun dattawa. 4Idan Farisawa suka dawo daga kasuwa, wajibi ne su yi wanka kamin su ci abinci. Akwai sauran al'adun da suke kiyayewa, kamar wanke moda, tukwane, da wasu santula na dalma, har da dakin cin abinci.) 5Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, “Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?” 6Amma ya amsa masu cewa, “Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni. 7Sujadar wofi suke mani suna koyar da ka'idodi na mutane a matsayin rukunansu'”. 8Kun watsar da dokar Allah sai kuka rungumi al'adun mutane. 9Sai yace masu, kun yi nasara wurin kau da dokokin Allah domin ku kiyaye al'adun ku na mutane. 10Koda shike Musa ya rubuta cewa, “ka girmama Ubanka da Uwarka”, kuma, “duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take”. 11Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, “duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)”'. 12Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu. 13Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi.” 14Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, “ku kasa kunne gareni, kuma ku gane. 15Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi” 16Bari mai kunnen ji, ya ji. 17Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali. 18Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba, 19domin ba zai iya kai wa cikin zuciyarsa ba, sai dai ya shiga cikin sa ya kuma fita a matsayin bayan gari a salga”. Da wannan magana, Yesu ya mayar da dukan abinci ya zama da tsabta. 20Ya ce, abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi 21Domin daga cikin mutum, kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani, lalata, sata, kisa, 22zina, kwadayi, mugunta, hai'inci, mugun guri, kishi, zargi, girmankai, wawanci. 23Duk wadannan miyagun abubuwa suna fitowa ne daga cikin mutum, kuma suke gurbatar da shi.” 24Ya tashi daga nan ya tafi shiyyar Sur da Sida. Ya shiga wani gida don baya son wani ya sani cewa yana nan, amma bai iya boyuwa ba. 25Amma nan da nan wata mace, wadda diyarta ke da mugun ruhu-wannan mace kuwa ta ji game da Yesu sai ta zo ta durkusa a gabansa. 26Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta. 27Sai ya ce mata, “Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata a dauki abincin yaya a ba karnuka ba”. 28Sai ta amsa masa cewa, “I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan.” 29Ya ce mata, “domin kin fadi haka, kina iya ki tafi domin aljani ya fita daga diyarki.” 30Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta. 31Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis. 32Sun kawo masa wani kurma, kuma bebe ne shi, suna rokansa ya dora hanuwansa a bisansa. 33Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa. 34Ya dubi sama, ya ja numfashi ya ce masa, “Ifatha”, wato, “bude!” 35Nan da nan ya mayar masa da jinsa. abinda ya daure harshensa ya sake shi, sai ya fara magana da kyau. 36Ya umarce su da kada su gaya wa wani. Amma duk da umarnin da yake basu, suna ta shaida shi ko'ina. 37kuma suna ta mamaki cewa, “Yayi kowanne abu da kyau, har ya sa kurame suna jin magana, da kuma bebaye na magana.”

¿Sabías que…?

Pureza, tradición y el camino más allá de Galilea

  • Fariseos y escribas que habían venido de Jerusalén cuestionaron a Jesús porque algunos de sus discípulos comían con las manos sin lavar. Marcos explica que, al guardar la tradición de los ancianos, los fariseos y todos los judíos no comían hasta lavarse de manera ceremonial, y que también se lavaban al volver del mercado y lavaban vasos, jarros, calderos y lechos para comer. Una cronología fecha este discurso sobre mandamientos y tradición en el año 29 d. C.Fuentes: el propio texto bíblico · Commandments and Tradition Discourse
  • Jesús respondió citando a Isaías, hijo de Amoz, acerca de un pueblo que honra a Dios con los labios mientras el corazón está lejos de él, y que enseña preceptos humanos como doctrina. A la tradición de los ancianos contrapuso un mandamiento que atribuye a Moisés —honrar al padre y a la madre— y la práctica del corbán, que el texto explica como una ofrenda consagrada a Dios y por la cual, según él, la persona ya no podía hacer nada por su padre o su madre.Fuentes: el propio texto bíblico · Isaiah
  • En la región de Tiro, una mujer griega, de origen sirofenicio, rogó a Jesús que expulsara un espíritu impuro de su hija. Después pasó por Sidón hasta el mar de Galilea y entró en la Decápolis: Sidón, en el Mediterráneo, al norte de Tiro, era la ciudad fenicia más antigua y la ciudad madre de Tiro, mientras que la Decápolis —nombre que significa diez ciudades— estaba al este y al sureste del lago y estaba habitada sobre todo por griegos. Allí le trajeron un hombre sordo que apenas podía hablar, y Jesús dijo: “Efata”, que el relato explica como “Ábrete”.Fuentes: el propio texto bíblico · Sidon · Tyre · Decapolis

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 1
  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículo 24
  • Sidon · Hoy: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · versículos 24, 31
  • Tyre · 33.271, 35.196 · versículos 24, 31
  • Phoenicia · 33.271, 35.196 · versículo 26
  • Decapolis · 32.717, 35.800 · versículo 31
  • Sea of Galilee · 32.819, 35.590 · versículo 31

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.