Nations Bible

Lucas 4

Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

1Sai Yesu, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga kogin Urdun, sai Ruhu Mai Tsarki ya bishe shi zuwa cikin jeji 2kwana arba'in, shaidan kuma ya jarabce shi. A kwanakin nan, bai ci abinci ba, kuma yunwa ta kama shi bayan karshen lokacin. 3Shaidan ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci wannan dutse ya zama gurasa.” 4Yesu ya amsa masa, “A rubuce yake, 'Ba da gurasa kadai Mutum zai rayu ba.'” 5Sai shaidan ya kai shi zuwa wani tudu mai tsawo, ya kuma nuna masa dukan mulkokin duniyan nan a dan lokaci. 6Shaidan ya ce masa, “Zan ba ka iko ka yi mulkin dukan wadannan, da dukan daukakarsu. Zan yi haka domin an ba ni su duka in yi mulkinsu, kuma ina da yanci in ba dukan wanda na ga dama. 7Saboda da haka, idan ka rusuna ka yi mani sujada, dukansu za su zama naka.” 8Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake, 'Dole ne Ubangiji Allahnka za ka yi wa sujada, shi kadai kuma za ka bauta wa.” 9Sai shaidan ya kai Yesu Urushalima, ya tsayadda shi a bisan kololuwar haikali, kuma ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka jefas da kanka kasa daga nan. 10Domin a rubuce yake, 'Zai ba mala'ikunsa umarni su kiyaye ka, su kuma tsare ka,' 11kuma, 'Za su daga ka sama a hannunsu, don kada ka yi tuntube a kan dutse.” 12Yesu ya amsa masa cewa, “An fadi, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'” 13Da shaidan ya gama yi wa Yesu gwaji, sai ya kyale shi sai wani lokaci. 14Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin. 15Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa. 16Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi. 17An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta, 18“Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci, 19in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji.” 20Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa. 21Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.” 22Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, “Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?” 23Yesu ya ce masu, “Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'” 24Ya sake cewa, “Hakika na fada maku, annabi baya samun karbuwa a garinsa. 25Amma na gaya maku gaskiya akwai gwauraye da yawa cikin Isra'ila a zamanin Iliya, lokacin da an rufe sammai shekaru uku da rabi babu ruwa, lokacin da anyi gagarumar yunwa a duk fadin kasar. 26Amma ba a aiki Iliya zuwa wurin waninsu ba, sai wurin gwauruwa da ke a Zarifat can kusa da Sidon. 27Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai. 28Dukan mutanen da ke cikin majami'a suka fusata kwarai sa'adda suka ji wadannan zantattuka. 29Suka tashi suka tura shi zuwa wajen birnin, suka kai shi bakin dutsen da aka gina garinsu a kai dominsu jefar da shi kasa. 30Amma ya ratsa tsakaninsu ya yi gabansa. 31Sannan ya gangara zuwa Kafarnahum, wani birni a Galili. Wata Asabaci yana koya wa mutane a cikin majami'a. 32Sun yi mamaki kwarai da koyarwan sa, domin maganarsa na da iko. 33A wannan lokacin akwai wani mutum a cikin majami'a mai kazamin ruhu, sai ya yi kara da babbar murya, 34“Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!” 35Yesu ya tsauta wa aljanin yana cewa, “Yi shiru ka fita daga cikinsa!” Da aljanin ya jefar da mutumin kasa a tsakiyarsu, ya fita daga cikinsa ba tare da yi masa rauni ba. 36Dukan mutanen suka yi mamaki, kuma suna ta zancen wannan abu a tsakaninsu. Sun ce, “Wanda irin maganganu kenan? Ya umarce kazaman ruhohin da karfi da iko kuma sun fita.” 37Saboda da haka, an fara yada labarinsa zuwa dukan kewayen yankin. 38Sai Yesu ya bar majami'ar ya shiga gidan Siman. A wannan lokacin, surukar Siman tana fama da zazzabi mai zafi, sai suka roke shi dominta. 39Sai ya tsaya a kanta, ya tsautawa zazzabin, kuma ya rabu da ita. Nan take, ta tashi ta fara yi masu hidima. 40Da faduwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan wadanda suke ciwo da cuttuttuka dabam dabam. Ya dora masu hannuwansa ya warkar da su. 41Aljanu kuma sun fita daga wadasunsu da dama, suna kuka cewa, “Kai ne Dan Allah!” Yesu ya tsauta wa aljannun ya kuma hana su magana, domin sun sani cewa shine Almasihu. 42Da safiya ta yi, ya kebe kansa zuwa wani wurin da babu kowa. Jama'a da dama suna neman sa suka zo inda yake. Sun yi kokari su hana shi barin su. 43Amma ya ce masu, “Dole in yi bisharar Allah a wasu birane da dama, domin dalilin da aka aiko ni nan kenan.” 44Sai ya ci gaba da wa'azi cikin majami'u dukan fadin Yahudiya.

¿Sabías que…?

La Tentación y el Inicio del Ministerio de Jesús

  • En la sinagoga de Nazaret, la ciudad donde se había criado, a Jesús se le entregó el rollo del profeta Isaías. Tras desenrollarlo y leer el pasaje sobre dar buenas nuevas a los pobres y proclamar libertad a los cautivos, lo enrolló de nuevo, se lo devolvió al asistente y se sentó a enseñar.Fuentes: el propio texto bíblico · Isaiah · Nazareth
  • Para señalar la falta de fe de sus oyentes locales, Jesús recordó cómo Elías fue enviado a socorrer a una viuda en Sarepta de Sidón y no a viudas de Israel, y cómo Eliseo sanó a Naamán el sirio en lugar de a leprosos israelitas.Fuentes: el propio texto bíblico · Elijah · Elisha · Naaman
  • Tras ser rechazado y casi arrojado desde la cima de la colina de Nazaret, Jesús trasladó su actividad a Capernaúm, en Galilea, donde enseñaba con autoridad en día de reposo, expulsaba demonios y sanó a la suegra de Simón de una intensa fiebre.Fuentes: el propio texto bíblico · Capernaum · Galilee

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Jordan · Hoy: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículo 1
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 9
  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículos 14, 31
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · versículos 16, 34
  • Sidon · Hoy: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · versículo 26
  • Zarephath · Hoy: Sarepta · 33.464, 35.295 · versículo 26
  • Judea · Hoy: Judea 1 · 31.777, 35.234 · versículo 44

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.