Santiago 5
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Ku zo yanzu, ku da kuke masu arziki, ku yi ta kuka da kururuwa domin bakin ciki iri-iri da ke zuwa gare ku. 2Arzikin ku ya rube, tufafinku kuma duk cin asu ne. 3Zinariya da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsar su kuwa zai zama shaida a kanku. Zai cinye naman ku kamar wuta. Kun yi ajiyar dukiyarku domin ranakun karshe. 4Duba, hakin ma'aikata yana kuka - hakin da kuka hana wa wadanda suka girbe maku gonaki. Kuma kukan masu girbin ya tafi ya kai ga kunnuwan Ubangiji mai Runduna. 5Kun yi zama cikin annashuwa a duniya kuma kun tsunduma kanku. Kun sa zukatan ku sun yi kiba domin ranar yanka. 6Kun hukunta kuma kun kashe adalin mutum. Bai kuwa yi tsayayya da ku ba. 7Saboda haka ku yi hakuri, 'yan'uwa, har sai zuwan Ubangiji. Duba, yadda manomi ya kan jira kaka mai amfani daga gona. Da hakuri yake jiran ta har sai ta karbi ruwa na fari da na karshe. 8Ku, ma, ku yi hakuri. Ku karfafa zukatan ku, domin zuwan Ubangiji ya yi kusa. 9Kada ku yi gunaguni, 'Yan'uwana, game da juna, don kada a hukunta ku. Duba, mai shari'a na tsaye a bakin kofa. 10Dauki misali, 'yan'uwa, daga shan wuya da hakurin annabawa, wadanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji. 11Duba, mukan kira wadanda suka jimre masu albarka. Kun dai ji irin jimiri da Ayuba ya yi, kun kuma san nufin Ubangiji, yadda yake mai yawan tausayi da jinkai. 12Fiye da komai duka, 'yan'uwana, kada ku yi rantsuwa, ko da sama, ko da kasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. A maimakon haka bari “I” ya zama “I”, in kuwa kun ce “A'a”, ya zama “A'a”, don kada ku fada a cikin hukunci. 13Akwai wanda ke fama a tsakanin ku? Sai ya yi addu'a, akwai wanda yake murna? Sai ya raira wakar yabo. 14Akwai mara lafiya a tsakanin ku? Sai ya kira dattawan ikilisiya, sai su yi masa addu'a. Suna shafa masa mai a cikin sunan Ubangiji. 15Addu'ar bangaskiya zai warkar da mara lafiyan, Ubangiji zai tashe shi. Idan ma ya yi zunubi, Allah zai gafarta masa. 16Soboda haka, ku furta zunuban ku ga juna, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da karfin aiki kwarai da gaske. 17Iliya dan Adam ne kamar mu. Amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, ba kuma yi ruwa a kasar ba har shekara uku da wata shida. 18Sai Iliya ya sake yin addu'a. Sammai suka ba da ruwa, kasa kuma ta ba da amfanin ta. 19Ya ku 'yan'uwana, idan wanin ku ya baude wa gaskiya, wani kuma ya dawo da shi, 20wannan mutum ya sani cewa, duk wanda ya dawo da mai zunubi a hanya daga baudewar sa, zai cece shi daga mutuwa, kuma zai rufe dunbin zunubai.

¿Sabías que…?
Riqueza, paciencia y oración
- Santiago 5 recuerda la perseverancia de Job y el resultado que el Señor le dio. El Easton's Bible Dictionary (1897) lo describe como un patriarca árabe que vivía en la tierra de Uz y mantuvo su integridad en medio de pruebas repentinas. El artículo dice que Dios después le concedió una prosperidad aún mayor que antes, que vivió ciento cuarenta años después del período de prueba y que es un ejemplo de paciencia bajo una calamidad severa.Fuentes: el propio texto bíblico · Job
- Santiago dice que Elías era un hombre igual a nosotros. Oró con fervor para que no lloviera, y no llovió sobre la tierra durante tres años y medio; oró otra vez, los cielos dieron lluvia, y la tierra produjo sus cosechas. El Easton's Bible Dictionary (1897) lo llama el tisbita, el “Elias” del Nuevo Testamento, y señala que entregó un mensaje del Señor a Acab.Fuentes: el propio texto bíblico · Elijah
- Para animar a la paciencia hasta la venida del Señor, Santiago señala al agricultor que espera el fruto precioso de la tierra y las lluvias de otoño y de primavera, y dice que el Juez está de pie a la puerta. El mismo capítulo advierte que los salarios retenidos a los trabajadores que segaron los campos están clamando, y que el clamor de los segadores ha llegado a los oídos del Señor de los ejércitos.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org