Santiago 3
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Ba mutane dayawa za su zama masu koyarwa ba, 'yan'uwana. Mun san cewa za mu karbi hukunci mafi tsanani. 2Domin mukan yi tuntube ta hanyoyi dayawa. Duk wanda bai yi tuntube ta hanyar kalmomi ba, shi mutum ne ginanne sosai, wanda ke iya kame dukan jikinsa. 3Idan muka sa linzami a bakunan dawakai, domin su yi mana biyayya, za mu iya sarrafa jikunan su gaba daya. 4Ku lura kuma da jiragen ruwa, ko da yake suna da girma sosai kuma iska mai karfi tana kora su, da karamin karfe ne matukin yake juya su inda ya so. 5Haka kuma harshe dan karamin gaba ne a jiki, sai fahariyan manyan abubuwa. Ku lura yadda dan karamin wuta yake cinna wa babban jeji wuta. 6Harshe ma wuta ne, a cikin dukan gabobin mu, duniyar zunubai da aka sa cikin fannonin jikunan mu. Yana gurbata dukan jiki, ya kuma sa al'amurar rayuwa su kama da wuta. Shi kuwa gidan wuta ne yake zuga shi. 7Domin kowace irin dabbar jeji, tsunsu, da masu jan ciki, da hallittar teku, ana sarrafa su kuma dan Adam har ya sarrafa su ma. 8Amma game da harshe, babu wani a cikin 'yan Adam da ya iya sarrafa shi. Mugunta ne mara hanuwa, cike da dafi mai kisa. 9Da wannan harshe muke yabon Ubangiji da kuma Uba, da shi kuma muke la'antar mutane wandanda aka hallitta cikin kamanin Allah. 10Bakin da ake sa albarka, da shi kuma ake la'antarwa. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba. 11Mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba, ko zai iya? 12''Yan'uwana, itacen baure ba zai iya yin zaitun ba, zai iya? Ko kuwa gonar inabi ya yi baure? Haka kuma, ruwan zartsi ba zai iya bayar da ruwan dadi ba. 13Ina mai hikima da fahimta a cikin ku? Bari wannan mutumin, ta kyakkyawan zaman sa ya nuna aikin da halin tawali'u da hikima ke sawa. 14Amma in kuna da matsanancin kishi da kazamin buri a cikin zuciyar ku, kada ku yi fahariya da karya game da gaskiya. 15Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga sama ba ce, a maimakon haka, ta duniya ce, mara ruhaniya, ta aljanu. 16Domin duk inda kishi da kazamin buri suke, a nan ake samun hargitsi da kowanne irin aikin mugunta. 17Amma hikiman nan ta sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, kamila ce, mai saukin kai, mai tsananin jinkai, mai yawan alheri, mara gajiya, sahihiya kuma. 18Kuma 'ya'yan adalci wanda ake shukawa a cikin salama a tsakanin wadanda ke kulla zumunci.

¿Sabías que…?
La lengua y la sabiduría de lo alto
- El capítulo comienza exhortando a que no sean muchos los que se hagan maestros, porque quienes enseñan serán juzgados con mayor rigor. Añade que todos tropezamos de muchas maneras y que quien nunca falla en lo que dice sería una persona perfecta, capaz de controlar todo el cuerpo.Fuentes: el propio texto bíblico
- El capítulo compara la lengua con cosas pequeñas de gran efecto: los frenos en la boca de los caballos guían a todo el animal, y un timón muy pequeño conduce un barco grande impulsado por vientos fuertes. Una pequeña chispa, añade, incendia un gran bosque. La lengua es llamada una parte pequeña del cuerpo que se jacta de grandes cosas, un fuego que nadie puede domar, aunque las personas doman animales, aves, reptiles y criaturas del mar.Fuentes: el propio texto bíblico
- La misma boca, dice el capítulo, tanto bendice al Señor y Padre como maldice a personas hechas a semejanza de Dios, y dice que esto no debe ser. Pregunta si de un mismo manantial pueden brotar agua dulce y agua salada, si una higuera puede dar aceitunas o si una vid puede producir higos. La sabiduría de lo alto se describe como pura, pacífica, amable y llena de misericordia, mientras que los celos y la ambición egoísta se vinculan con el desorden y con una sabiduría llamada terrenal, no espiritual y demoníaca.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org