Efesios 3
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Saboda haka, ni Bulus, dan sarka sabili da Almasihu dominku al'ummai. 2Ina zaton kun ji a kan aiki mai girma na alherin Allah da ya ba ni dominku. 3Ina rubuto maku bisa ga wahayin da aka sanashe ni. Wannan ita ce boyayyar gaskiya da na rubuta a takaice a cikin wata wasikar. 4Sa'adda kuka karanta a kan wannan, za ku iya fahimtar basira ta cikin boyayyar gaskiya a kan Almasihu. 5Wanda a zamanun da ba a bayyana wa mutane ba. Amma yanzu an bayyana shi ga manzanni da annabawa kebabbu a cikin Ruhu. 6Wannan boyayyar bishara ita ce al'ummai ma abokan gado ne tare da mu, gabobi ne cikin jiki daya. Abokan tarayya ne kuma cikin alkawaran Almasihu Yesu ta wurin bishara. 7Domin wannan na zama bawa ta wurin baiwar alherin Allah da ya bani ta wurin karfin ikonsa. 8Allah ne ya ba ni wannan baiwa. Ko da shike nine mafi kankanta cikin kebabbun Allah, in yi shelar bishara ga al'ummai akan wadatar Almasihu marar matuka. 9In kuma fahimtar da dukan mutane a kan shirin Allah, wannan boyayyar gaskiya wadda tun zamanai da suka wuce Allah ya boye, shi da ke mahallicin dukan abubuwa. 10Saboda haka, ta wurin ikilisiya, masu iko da masu mulkin sararin sama za su san hikimar Allah ta fuskoki daban daban. 11Wannan ya kasance bisa ga dawwamammen nufi da ya zartar cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. 12Gama a cikin Almasihu muna da gabagadi, da dama, da amincewa sabili da gaskiyar mu a cikinsa. 13Saboda haka ina rokon ku kada ku karaya da wahalar da na sha domin ku wadda ta zama daukakar ku. 14Saboda haka nake durkusawa da gwiwa ta a gaban Uba, 15wanda ta wurinsa ake kiran kowanne iyali na sama da na kasa. 16Ina addu'a ya amince maku bisa ga yalwar wadatar daukakarsa, ku karfafa matuka da iko ta wurin Ruhunsa, da yake cikinku. 17Ina addu'a Almasihu ya zauna a cikin zuciyar ku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu'a ku kafu ku kuma ginu da zurfi kwarai cikin kaunarsa. 18Ku kasance cikin kaunarsa domin ku gane, tare da dukan masu bi, menene zurfi, da fadi, da tsawon kaunar Almasihu. 19Ina addu'a domin ku san mafificiyar kaunar Almasihu da ta wuce sani. Ku yi wannan domin a cika ku da dukan cikar Allah. 20Yanzu ga wanda yake da ikon aikata dukan abu fiye da abin da muke roko ko tunani, bisa ga ikonsa da ke aiki a cikinmu, 21daukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikilisiya ta wurin Almasihu Yesu har ya zuwa zamanun zamanai har abada abadin. Amin.

¿Sabías que…?
El misterio abierto a los gentiles
- En este capítulo, Pablo se llama prisionero de Cristo Jesús por causa de los gentiles y pide a sus lectores que no se desanimen por los sufrimientos que él padece por ellos, a los que llama gloria de ellos.Fuentes: el propio texto bíblico
- Describe un misterio que le fue dado a conocer por revelación y que durante siglos permaneció oculto en Dios, quien creó todas las cosas. Ese misterio es que, por medio del evangelio, los gentiles son coherederos, miembros del mismo cuerpo y participantes de la promesa en Cristo Jesús: algo que no se dio a conocer a las generaciones anteriores como ahora ha sido revelado por el Espíritu a los santos apóstoles y profetas de Dios.Fuentes: el propio texto bíblico
- El Easton's Bible Dictionary (1897) afirma que Pablo nació más o menos en la misma época que Jesús, que su nombre de circuncisión era Saulo y que el nombre Pablo probablemente se le dio en la infancia para usarlo en el mundo gentil, mientras Saulo sería su nombre hebreo de casa. Era natural de Tarso, capital de Cilicia, una provincia romana en el sureste de Asia Menor: una ciudad comercial próspera a orillas del río navegable Cidno y sede de una universidad famosa. Es este Pablo quien, en el capítulo, dice que se le confió la administración de la gracia de Dios en favor de los gentiles.Fuentes: Paul · el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org