2 Corintios 5
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Mun san cewa idan wannan gidan da muke zaune a ciki ya rushe, muna da wani ginin daga wurin Allah. Gida ne wanda ba hannuwan mutane suka gina ba, amma madawwamin gida ne a cikin sama. 2Domin a cikin wannan jiki muna gurnani, muna jira a suturta mu da wurin zaman mu na samaniya. 3Muna jiran wannan ne domin ta wurin suturtar da mu ba za a same mu tsirara ba. 4Gama babu shakka yayinda muke cikin wannan alfarwa, muna gurnani, muna nawaita. Ba mu so muyi zaman hutanci. Maimakon haka, muna so a suturtar da mu, domin rai ya hadiye abu mai mutuwa. 5Wanda kuwa yake shirya mu domin ainihin wannan abu Allah ne, wanda ya ba mu Ruhu a matsayin alkawarin abinda ke zuwa. 6Domin wannan mu zama da gabagadi koyaushe. Mu lura da cewa yayinda muka shagala cikin jiki, muna nesa da Ubangiji. 7Gama bisa ga bangaskiya muke tafiya, ba bisa ga ganin ido ba. 8Don haka muna da gabagadi. Mun gwammace mu rabu da jiki domin mu zauna tare da Ubangiji. 9Sai muka maishe shi burinmu, ko muna cikin jiki ko nesa, mu gamshe shi. 10Domin tilas dukanmu mu hallara a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, saboda kowa ya karbi sakamakon abubuwan da yayi cikin jiki, ko masu kyau ne ko marasa kyau. 11Don haka, domin mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane. Allah na ganin yadda muke a fili. Ina fatan hakan a fili take ga lamirinku. 12Ba muna kokarin mu rinjaye ku domin ku kalle mu a matsayin amintattun mutane ba. Maimakon haka, muna ba ku dalilin yin takama da mu, domin ku sami amsar da za ku bada ga wadanda ke fahariya da kasancewarsu amma ba game da abinda ke zuciya ba. 13Gama idan mun fita daga hankulanmu, saboda Allah ne. Kuma idan muna cikin hankalinmu, domin ku ne. 14Domin kaunar Almasihu ta tilas ta mu, domin mun tabbatar da wannan: cewa mutum daya ya mutu domin kowa, kuma domin wannan duka sun mutu. 15Kuma Almasihu ya mutu domin kowa, domin wadanda ke raye kada su sake rayuwa domin kansu. A maimakon haka, su yi rayuwa domin shi wanda ya mutu kuma aka tashe shi. 16Domin wannan dalili, daga yanzu ba za mu kara shar'anta kowa bisa ga ma'aunin 'yan'adam ba, ko da yake a baya mun taba duban Almasihu a haka. Amma yanzu mun daina shar'anta kowa ta haka. 17Saboda haka, duk wanda ke cikin Almasihu, sabon halitta ne. Tsofaffin al'amura sun shude. Duba, sun zama sababbi. 18Dukan wadannan abubuwa daga Allah ne. Ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu hidimar sulhu. 19Wato, cikin Almasihu, Allah na sulhunta duniya zuwa gare shi, ba tare da lissafin zunubansu a kansu ba. Yana damka mana sakon sulhu. 20Don haka an zabe mu a matsayin wakilan Almasihu, kamar dai Allah na kira ga mutane ta wurin mu. Muna rokon ku, saboda Almasihu: ''ku sulhuntu ga Allah!'' 21Shi ya maida Almasihu ya zama hadaya domin zunubinmu. Shine wanda bai taba zunubi ba. Ya yi haka ne don mu zama adalchin Allah a cikin sa.

¿Sabías que…?
La reconciliación y la esperanza de un hogar celestial
- Este capítulo compara la vida presente con una tienda terrenal que puede desarmarse y la contrapone a un edificio de Dios: una casa eterna en el cielo, no construida por manos humanas. En esa tienda gimen, anhelando ser vestidos con la morada celestial en vez de quedar desnudos, para que la mortalidad sea tragada por la vida.Fuentes: el propio texto bíblico
- El autor dice que Dios los preparó para esto y les dio el Espíritu como garantía de lo que ha de venir. Están confiados, pero mientras están en casa en el cuerpo están lejos del Señor, caminando por fe y no por vista; todos deben comparecer ante el tribunal de Cristo para recibir lo que les corresponde por lo hecho en el cuerpo, sea bueno o malo.Fuentes: el propio texto bíblico
- El amor de Cristo los impulsa, pues uno murió por todos, para que los que viven ya no vivan para sí mismos, sino para quien murió por ellos y resucitó. Quien está en Cristo es una nueva creación — lo viejo pasó y lo nuevo ha llegado — y son embajadores de Cristo, portadores de un mensaje de reconciliación: Dios hizo pecado, en favor de ellos, a quien no conoció pecado, para que en él llegaran a ser justicia de Dios.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org