1 Tesalonicenses 5
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Yanzu fa game da zancen lokatai da zamanai 'yan'uwa, ba ku da bukatar a rubuta maku wani abu. 2Domin ku da kanku kun sani kwarai cewa ranar zuwan Ubangiji kamar barawo take da dare. 3Da suna zancen “zaman lafiya da kwanciyar rai,” sai hallaka ta zo masu ba zato ba tsammani. Zai zama kamar nakudar haihuwa ce da ke kama mace mai ciki. Ba su kwa da wata hanyar kubuta. 4Amma ku, 'yan'uwa, ai ba cikin duhu kuke ba har da wannan rana zata mamaye ku kamar barawo. 5Domin dukkan ku 'ya'yan haske ne 'ya'yan rana kuwa. Mu ba 'ya'yan dare ba ne ko na duhu, 6Don haka, kada muyi barci kamar yadda sauran ke yi. Maimakon haka, bari mu kasance muna zaman tsaro kuma muna a fadake. 7Don masu yin barci da dare suke yin barci, haka kuma masu sha su bugu ma da dare suke yi. 8Tunda shike mu 'ya'yan rana ne, bari mu zauna a natse. Bari musa sulke na bangaskiya da kauna, mu kuma sa kwalkwali don ceton mu dake gaba. 9Domin Allah bai kaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijin mu Yesu Almasihu. 10Shi ne wanda ya mutu domin mu, don ko da muna raye ko muna mace, mu iya rayuwa tare da shi, 11Domin haka ku ta'azantar da juna ku kuma inganta juna, kamar yadda kuke yi. 12Muna rokon ku, 'yan'uwa, ku bada daraja ga wadanda suke aiki a tsakaninku wadanda kuma suke shugabanci a kan ku cikin Ubangiji, wadanda kuma suke horonku. 13Muna kuma rokon ku, da ku kula dasu ku kuma kaunacesu sabili da irin ayyukansu. Ku kuma yi zaman lafiya da junan ku. 14Muna yi maku gargadi 'yan'uwa; ku jawa marassa ji kunne, ku karfafa marassa karfin zuciya, ku taimaki gajiyayyu, kuyi zaman hakuri da kowa. 15Ku lura kada wani ya rama mugunta da mugunta, Maimakon haka ma, Ku cigaba da abinda ke mai kyau ga juna da kowa duka. 16Kuyi farin ciki koyaushe. 17Kuyi addu'a ba fasawa. 18A cikin kome kuyi godiya. Domin wannan ne nufin Allah a cikin Yesu Almasihu game daku. 19Kada ku hana Ruhun Allah aiki a cikin ku. 20Kada ku raina anabce anabce. 21Ku gwada komai. Ku rike abinda ke mai kyau. 22Ku kaucewa duk wani abinda yayi kama da mugunta. 23Bari Allah na salama ya mai da ku cikakun tsarkaka. Bari dukkan ruhun ku, da zuciyar ku, da jikin ku su zama adanannu marassa zargi domin zuwan Ubangijin mu Yesu Almasihu. 24Wanda ya kira ku mai aminci ne, wanda kuma zai aikata. 25Yan'uwa, kuyi addu'a domin mu. 26Ku gaida dukkan yan'uwa da tsattsarkar sumba. 27Ina rokon ku saboda Ubangiji ku karanta wasikar nan ga dukkan 'yan'uwa. 28Bari alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu shi kasance tareda ku.

¿Sabías que…?
Despiertos para el Día del Señor
- Este capítulo dice que el Día del Señor vendrá como ladrón en la noche y que la destrucción llegará de repente, como dolores de parto, mientras la gente dice: “Paz y seguridad”. Llama a los hermanos hijos de la luz e hijos del día, y los exhorta a no dormir como los demás, sino a permanecer despiertos y sobrios.Fuentes: el propio texto bíblico
- A quienes pertenecen al día se les pide que sean sobrios y se pongan la coraza de la fe y del amor y el casco de la esperanza de la salvación. El capítulo dice que Dios no los destinó a la ira, sino a obtener la salvación por medio del Señor Jesucristo, quien murió para que, despiertos o dormidos, vivan juntos con él.Fuentes: el propio texto bíblico
- Las palabras finales piden a los hermanos que reconozcan a quienes trabajan con diligencia entre ellos, presiden sobre ellos y los instruyen, teniéndolos en la más alta estima por su trabajo. Se les exhorta a amonestar a los indisciplinados, animar a los desalentados, ayudar a los débiles, ser pacientes con todos y no devolver mal por mal. También se les dice que no apaguen el Espíritu ni traten las profecías con desprecio, sino que prueben todas las cosas, saluden a todos los hermanos con un beso santo y hagan que esta carta sea leída a todos los hermanos.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org