1 Tesalonicenses 2
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Domin ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, cewa zuwan mu gareku, ba a banza yake ba. 2Kun kuma san yadda aka wulakantar damu, aka kuma kunyatar damu a Filibi, kamar yadda kuka sani. Muna nan kuwa da karfin zuciya cikin Allahnmu domin yi maku bisharar Allah cikin fama da yawa. 3Domin kuwa gargadinmu zuwa a gare ku ba gurbatacciya bace, ko cikin rashin tsarki, ba kuma ta yaudara bace. 4A maimako, kamar yadda Allah ya amince damu, ya kuma damka mana amanar bishararsa, haka kuma muke yin magana. Muna maganar ba domin mu gamshi mutane ba, amma domin mu gamshi Allah. Domin shi ne yake gwada zuciyarmu. 5Domin bamu taba yi maku dadin baki ba, ko sau daya, kamar yadda kuka sani, ko kwadayi a asirce, kamar yadda Allah shine shaidar mu. 6Bamu kuma nemi daukaka daga mutane ko daga gare ku ko kuma wadansu ba. Da mun so da mun mori ikonmu a matsayin manzannin Almasihu. 7A maimakon haka, mun kaskantar da kanmu a tsakanin ku kamar yadda uwa take ta'azantar da 'ya'yan ta. 8Don haka muna da kauna domin ku, ba bisharar Allahnmu kadai muke jin dadin yi maku ba, amma harda bada rayukan mu domin ku. Domin kun zama kaunatattu ne a garemu, 9Kufa tuna, 'yan'uwa, game da aikinmu da famarmu. Dare da rana muna aiki sosai domin kada mu nawaita wa kowane dayan ku. A lokacin da muke yi maku bisharar Allah. 10Ku shaidu ne, haka ma Allah, yadda muka yi rayuwar tsarki da kuma adalci da rashin abin zargi a wajenku wadanda kuka bada gaskiya. 11Don haka kun kuma sani yadda muka rika yi da kowannenku, kamar uba da 'ya'yansa, yadda muka yi ma ku garadi da kuma karfafa ku, mun kuma shaida. 12Domin ku yi tafiya a hanyar da ta dace ga Allah, wanda ya kira ku zuwa ga mulkinsa da kuma daukakarsa. 13Domin wannan dalili ne yasa muke yi wa Allah godiya a koyaushe. Domin a lokacin da kuka karbi maganar Allah daga wurinmu wadda kuka ji, kun karbeta da gaske ba kamar maganar mutum ba. A maimako, kuka karbeta da gaskiyarta, kamar yadda take, maganar Allah. Wannan kalma kuma ita ce ke aiki a cikin ku wadanda kuka yi bangaskiya. 14Domin ku 'yan'uwa, kun zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da ke Yahudiya cikin Almasihu Yesu. Domim kuma kun sha wahala irin tamu daga wurin mutanen kasarku kamar yadda suma suka sha a hannun Yahadawa. 15Yahudawane suka kashe Ubangiji Yesu da sauran Annabawa, kuma Yahudawane suka koro mu, Basu gamshi Allah ba. A maimako, suna hamayya da dukkan mutane. 16Sun kuma haramta mana yin magana da Al'ummai domin su sami ceto. Sakamakon haka kuwa kullum suna cika zunubansu. Fushi kuma ya afko kansu daga karshe. 17Mu kuma, 'yan'uwa, mun rabu daku na karamin lokaci, a zahiri, ba a zuciya ba, mun kuma yi iyakar kokarinmu da marmarin ganin fuskarku. 18Domin mun yi maramarin zuwa gareku. Ni, Bulus, ba sau daya ba, amma Shaidan ya hanamu. 19To menene begenmu a gaba, ko murnarmu ko rawanin alfahari, a gaban Ubangijinmu Yesu a ranar zuwansa? Ko ba ku bane, da kuma sauran jama'a? 20Don kuwa kune daukakarmu da kuma farin cikinmu.

¿Sabías que…?
Ministerio, sufrimiento y un regreso impedido
- Pablo recuerda a los lectores que él y sus compañeros ya habían soportado sufrimiento y un trato vergonzoso en Filipos y, aun así, tuvieron valor para anunciar el evangelio a pesar de una fuerte oposición. Filipos, antes llamada Crénides, era la capital de la provincia de Macedonia; Filipo de Macedonia fortificó la antigua ciudad tracia y le dio su propio nombre, y bajo el emperador Augusto se convirtió en una colonia romana, un asentamiento militar de soldados romanos establecido para controlar el distrito recién conquistado, descrita como una Roma en miniatura.Fuentes: el propio texto bíblico · Philippi
- Pablo dice que intentó volver una y otra vez, pero Satanás se lo impidió, aunque el deseo de ver a los lectores cara a cara se había vuelto aún más intenso. El nombre Satanás significa adversario o acusador, y en el Nuevo Testamento se usa de manera intercambiable con el diablo más de treinta veces.Fuentes: el propio texto bíblico · Satan
- Los lectores son descritos como imitadores de las iglesias de Dios en Judea que están en Cristo Jesús, y sufrieron de parte de sus propios compatriotas lo que aquellas iglesias sufrieron. Bajo los romanos, en el tiempo de Cristo, Judea era la más meridional de las tres divisiones de Palestina y parte de la provincia de Siria, e incluía los territorios de Judá, Benjamín, Dan, Simeón y parte de Efraín.Fuentes: el propio texto bíblico · Judea
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org