1 Juan 2
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1'Ya'yana, na rubuta ma ku wadannan abubuwa domin kada kuyi zunubi. Amma idan wani yayi zunubi muna da matsakanci a wurin Uba, Yesu Almasihu, mai adalci. 2Shine fansar zunubanmu, ba ma namu kadai ba amma na duniya dukka. 3Ta haka muka san cewa mun san shi, idan mun kiyaye dokokinsa. 4Duk wanda yace, “Na san Allah” amma bai kiyaye dokokinsa ba, makaryaci ne gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5Amma duk wanda ya kiyaye maganarsa, hakika kaunar Allah ta kammala a cikin wannan mutum. Ta wurin haka muka sani muna cikinsa. 6Duk wanda yace yana cikin Allah dole ne shi da kansa yayi tafiya kamar yadda Yesu Almasihu yayi. 7Kaunatattu, ba sabuwar doka nike rubuta maku ba, amma tsohuwar doka ce wadda kuka ji tun farko. Tsohuwar dokar kuwa itace maganar da kuka ji tun farko. 8Amma yanzu ina rubuta maku sabuwar doka wadda gaskiya ce a cikin Almasihu da cikinku, saboda duhu yana wucewa, haske na gaskiya yana haskakawa. 9Duk wanda yace yana cikin haske amma yana kin dan'uwansa, yana cikin duhu har yanzu. 10kuma wanda yake kaunar dan'uwansa yana cikin haske babu dalilin tuntube a wurinsa. 11Amma duk wanda yake kin dan'uwansa yana cikin duhu, yana kuma tafiya cikin duhu, bai san ma inda ya nufa ba, domin duhu ya makantar da shi. 12Na rubuta maku, ya ku kaunatun 'ya'yana, saboda an gafarta zunubanku domin sunansa. 13Na rubuta maku, ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku matasa saboda kun yi nasara da mugun. Na rubuta maku, yara kanana, saboda kun san Uban. 14Na rubuta maku, Ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku, matasa, saboda kuna da karfi, kuma maganar Allah tana zaune cikinku. Kuma kun yi nasara da mugun. 15Kada kuyi kaunar duniya ko abubuwan da suke cikin duniya. Idan wani yayi kaunar duniya, kaunar Uban bata cikinsa. 16Domin dukkan abubuwan da suke a cikin duniya, kwadayi na jiki, abin da idanu suke sha'wa, da rayuwar girman kai ta wofi, ba na Uban bane amma na duniya ne. 17Duniya tana wucewa tare da sha'awarta. Amma dukkan wanda ya aikata nufin Allah zaya kasance har abada. 18Yara kanana, sa'a ta karshe ce. Kamar dai yadda kuka ji magafcin Almasihu yana zuwa, ko yanzu ma magaftan Almasihu da yawa sun rigaya sun zo, ta haka muka san sa'a ta karshe ce. 19Sun fita daga cikinmu, dama su bana cikinmu bane. Gama idan da su namu ne da sun ci gaba tare damu. Amma da yake sun fita, ya nuna su ba na cikinmu bane. 20Amma ku kun karbi shafewa daga wurin Mai Tsarki, kuma dukkanku kun san gaskiya. 21Bana rubuta maku bane domin baku san gaskiya ba, amma saboda kun santa, kuma ba wata karya da ta fito daga gaskiya. 22Wanene makaryaci shine wanda yayi musu cewa Yesu ba Almasihu bane? Wannan mutumin shi ne magafcin Almasihu, tun da yayi musun Uba yayi musun Dan. 23Ba wanda yayi musun Dan kuma yake da Uban. Dukkan wanda ya amince da Dan yana da Uban ma. 24A game daku kuma, sai ku bari abinda kuka ji daga farko ya zauna a cikinku. Idan abin da kuka ji daga farko ya zauna a cikinku, kuma zaku kasance a cikin Dan da kuma Uban. 25Alkawarin da ya bamu kenan, rai na har abada. 26Na rubuta maku wadannan abubuwa ne game da wadanda zasu baudar daku. 27Game daku, shafewar daku ka samu daga wurinsa tana nan a cikinku, baku bukatar wani ya koyar daku. Amma kamar yadda shafewar da kuka karba a wurinsa ta koya maku dukkan abu, kuma gaskiya ne ba karya bane, tana nan a cikinku kamar yadda a ka koya maku, ku kasance a cikinsa. 28Yanzu fa, 'ya'ya na kaunatattu, ku kasance a cikinsa domin sa'adda zai baiyyana mu zama da gabagadi ba tare da kunya ba a gabansa sa'adda zai zo. 29Idan kun sani shi mai adalci ne, kun sani dukkan wanda ke aikata adalci haifaffe ne daga wurinsa.

¿Sabías que…?
Luz, amor y permanecer en Cristo
- El autor llama a los lectores “hijitos” y también se dirige, por turno, a los niños, a los padres y a los jóvenes. A los niños les dice que sus pecados han sido perdonados y que conocen al Padre; a los padres, que conocen al que es desde el principio; a los jóvenes, que son fuertes, que la palabra de Dios permanece en ellos y que han vencido al maligno.Fuentes: el propio texto bíblico
- El autor llama al mandamiento a la vez antiguo y nuevo: es el mensaje que tienen desde el principio, y también es nuevo porque es verdadero en Jesús y en ellos, mientras las tinieblas se disipan y la luz verdadera ya brilla. Odiar al hermano, dice el capítulo, deja a la persona caminando en tinieblas; amar al hermano es permanecer en la luz.Fuentes: el propio texto bíblico
- En este capítulo, “anticristo” no es solo la figura de cuya venida los lectores han oído hablar. El autor dice que ya han aparecido muchos anticristos, que salieron del grupo al que él llama “nosotros”, aunque no pertenecían a él, y que el anticristo es quien niega que Jesús es el Cristo y niega al Padre y al Hijo. Por esa aparición, escribe, se sabe que es la última hora.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org