Números 15
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Ƙarin hadayu
1Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Bayan kun shiga ƙasar da nake ba ku a matsayin gida, 3kuka yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji, daga cikin shanu, ko tumaki, abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa, ko hadayu don alkawura na musamman, ko hadayar yardar rai, ko kuma hadaya ta biki, 4sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai. 5Da kowane ɗan rago don hadaya ta ƙonawa, a shirya kwalaba ɗaya na ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha.
6“ ‘In da rago ne za a miƙa, to, sai a shirya hadaya ta gari mai laushi, garin yă zama kashi biyu bisa goma na efa. A kwaɓa shi da kashi ɗaya bisa uku na garwan mai, 7da kashi ɗaya bisa uku na garwan ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. A miƙa ta abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
8“ ‘Sa’ad da kuka shirya rago don hadaya ta ƙonawa saboda alkawari na musamman, ko hadaya ta salama ga Ubangiji, 9sai ku kawo hadaya ta gari tare da bijimi, kashi ɗaya bisa uku na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da rabin garwan mai. 10A kuma kawo rabin garwan ruwan inabi na hadaya ta sha. Za tă zama hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 11Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru. 12Haka za a yi da kowannensu bisa ga abin da aka shirya.
13“ ‘Duk wanda yake ɗan ƙasa, ta haka ne dole zai aikata waɗannan abubuwa sa’ad da ya kawo hadaya da akan yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 14Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi. 15Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji. 16Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’ ”
17Ubangiji ya ce wa Musa, 18“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da ina kai ku, 19kuka ci abincin ƙasar, ku miƙa wani sashe na amfanin ƙasar a matsayin hadaya ga Ubangiji. 20Ku kawo waina daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku, ku kuma miƙa shi a matsayin hadaya daga masussuka. 21A duk tsararraki masu zuwa, za ku miƙa wannan hadaya daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku ga Ubangiji.
Hadayu domin zunubai da ba na ganganci ba
22“ ‘To, in ku a matsayin jama’a, da gangan kuka ƙi kiyaye waɗannan ƙa’idodi da Ubangiji ya ba wa Musa ba, 23ko wani daga cikin umarnan da Ubangiji ya ba ku ta wurinsa, daga ranar da Ubangiji ya ba da su, har zuwa tsararraki masu zuwa, 24in kuwa aka yi haka ba da gangan ba, kuma da rashin sani, sai duk jama’a su miƙa ɗan bijimi don hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, tare da ƙayyadadden hadaya ta gari, da hadaya ta sha, da kuma bunsuru na hadaya don zunubi. 25Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama’ar Isra’ilawa, za a kuma gafarta musu, gama ba da gangan ba ne suka aikata, kuma sun kawo wa Ubangiji hadayar da akan yi da wuta da kuma hadaya don zunubi saboda laifinsu. 26Za a gafarta wa dukan jama’ar Isra’ilawa, da baƙin da suke zama a cikinsu, gama duk laifin da aka yi da rashin sani, yakan shafi dukan mutane.
27“ ‘Amma in mutum ɗaya ne kaɗai ya yi laifi ba da gangan ba, dole yă kawo akuya domin hadaya don zunubi. 28Firist zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin nan da ya aikata laifi ba da gangan ba, in kuwa an yi kafara saboda shi, za a gafarta masa. 29Ƙa’ida dai za tă zama ɗaya ga duk wanda ya yi laifi ba da gangan ba, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙon da yake zama a cikinku.
30“ ‘Amma duk wanda ya yi zunubi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko baƙo, ya saɓi Ubangiji, dole a ware wannan mutum daga mutanensa, 31gama ya rena maganar Ubangiji, ya kuma karya umarninsa. Tabbatacce za a kashe wannan mutum, alhakinsa laifinsa kuwa yana wuyansa.’ ”
An kashe mai karya ranar Asabbaci
32Yayinda Isra’ilawa suke ciki hamada, sai aka sami wani mutum yana tattara itace a ranar Asabbaci. 33Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro, 34sai suka sa shi a gidan waƙafi don ba su riga sun san abin da za a yi da shi ba tukuna. 35Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Dole mutumin yă mutu. Dole dukan taron su jajjefe shi a bayan sansani.” 36Saboda haka taron suka ɗauke shi zuwa bayan sansani, suka kuma jajjefe shi har ya mutu, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Tuntaye a riguna
37Ubangiji ya ce wa Musa, 38“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘A dukan tsararraki masu zuwa, za ku sa tuntaye a gefen rigunarku, su sa zare mai ruwan shuɗi a bisan kowane tuntu. 39Tuntayen za su zama muku abin dubawa don ku riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji, don kada ku bi son zuciyarku, da sha’awar idanunku yadda kuka taɓa yi. 40Sa’an nan za ku riƙa tuna, ku kuma aikata dukan umarnaina ku zama tsarkaka ga Allahnku. 41Ni ne Ubangiji Allahnku, da ya fitar da ku daga Masar, don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

¿Sabías que…?
Ofrendas, Obediencia y Recordatorios
- Las normas dadas para las ofrendas de cereal, las libaciones y los pecados involuntarios se aplicaban por igual a los israelitas nativos y a los extranjeros que residían entre ellos. La ley estableció expresamente un único estatuto permanente para ambos grupos ante el SEÑOR.Fuentes: el propio texto bíblico
- La ley hacía una clara distinción entre los pecados cometidos por error, para los cuales se proveía expiación mediante sacrificios, y los pecados desafiantes. Quien pecaba con rebeldía era considerado como blasfemo contra el SEÑOR y despreciador de Su palabra, quedando separado de la comunidad.Fuentes: el propio texto bíblico
- Para ayudar al pueblo a recordar todos los mandamientos divinos, se ordenó a los israelitas colocar borlas con un cordón azul en las esquinas de sus vestiduras. Mirar estas borlas tenía como fin evitar que se extraviaran siguiendo su propio corazón y sus propios ojos.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículo 41
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org