Nations Bible

Números 10

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

Kakakin azurfa

1Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Ka ƙera kakaki guda biyu na azurfa, ka kuma yi amfani da su don kira taron jama’a wuri ɗaya, don kuma ka riƙa sanar da su lokacin tashi daga sansani. 3Sa’ad da aka busa su biyu, dukan jama’a za su taru a gabanka a ƙofar Tentin Sujada. 4In ɗaya ne kaɗai aka busa, sai shugabannin kabilan Isra’ila, su taru a gabanka. 5Sa’ad da aka ji karar busar kakaki, sai sansanin da yake a gabashi, su kama hanya. 6A kara ta biyu, sansanin da yake a kudanci, su kama hanya. Busan kakaki zai zama alama ta kama hanya. 7In don a tara jama’a ne, sai a busa kakaki, amma ba da irin alama ɗaya ba.

8“’Ya’yan Haruna, firistoci ne, za su busa kakaki. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla gare ku da kuma tsararraki masu zuwa. 9Duk lokacin da za ku tafi yaƙi a ƙasarku, in akwai waɗansu da suke matsa muku, za ku yi amfani da waɗannan kakaki ta wurin hura su, alama ce, cewa za a je yaƙi. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, yă cece ku daga maƙiyanku. 10Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Isra’ilawa sun bar Sinai

11A rana ta ashirin ga wata na biyu, a shekara ta biyu, sai girgijen ya tashi daga tabanakul na Shaida. 12Sai Isra’ilawa suka tashi daki-daki daga Hamadar Sinai, suna tafiya daga wuri zuwa wuri, har sai da girgijen ya tsaya a Hamadar Faran. 13Suka kama hanya, a wannan lokaci, bisa umarnin Ubangiji, ta wurin Musa.

14Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba. 15Netanel ɗan Zuwar ne shugaban ɓangaren kabilar Issakar, 16Eliyab ɗan Helon kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Zebulun. 17Sa’an nan aka saukar da tabanakul ƙasa, Gershonawa da mutanen Merari da suke ɗauke da shi suka kama hanya.

18Sai ɓangarori sansanin Ruben suka biyo, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Elizur ɗan Shedeyur ne shugaba. 19Shelumiyel ɗan Zurishaddai ne shugaban ɓangaren kabilar Simeyon, 20Eliyasaf ɗan Deyuwel kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Gad. 21Sai Kohatawa suka kama hanya, ɗauke da kayayyaki masu tsarki, domin kafin su kai wurin da za a kafa sansani, a riga an kafa tabanakul.

22Biye da waɗannan kuma sai ɓangaren sansanin kabilar Efraim suka biyo bisa ga ƙa’ida da aka yi, aka kuma umarta. Elishama ɗan Ammihud ne shugaba. 23Gamaliyel ɗan Fedazur ne shugaban ɓangaren kabilar Manasse, 24Abidan ɗan Gideyoni kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Benyamin.

25A ƙarshe, a matsayi masu gadin bayan dukan ɓangarori, sai ɓangaren sansanin Dan suka tashi bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ne shugaba. 26Fagiyel ɗan Okran ne shugaban ɓangaren kabilan Asher, 27Ahira ɗan Enan kuma shi ne shugaban kabilar Naftali. 28Wannan shi ne tsarin tafiyar ɓangarorin Isra’ilawa, sa’ad da sukan kama hanya.

29Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamidiyane surukinsa, “Yanzu fa, muna shirin tashi ne daga nan, domin mu tafi inda Ubangiji ya ce, ‘Zan ba ku.’ Ka zo tare da mu, za mu kuwa yi maka alheri, gama Ubangiji ya yi wa Isra’ilawa alkawari abubuwa masu kyau.”

30Ya amsa, ya ce “A’a, ba zan tafi ba; zan koma ƙasata da kuma wurin mutanena.”

31Amma Musa ya ce, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu. Ka san inda ya kamata mu kafa sansani a hamada, za ka kuma zama idanunmu. 32In ka zo tare da mu, za mu raba duk abin alherin Ubangiji ya ba mu tare da kai.”

33Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don yă samo musu masauƙi. 34A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.

35Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce,

“Ka tashi, ya Ubangiji!

Ka sa maƙiyanka su warwatse;

masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.”

36Duk sa’ad da akwatin ya sauka kuma, sai Musa ya ce,

“Ka komo, ya Ubangiji,

a wurin dubban da ba a iya ƙidayawa na iyalan Isra’ila.”

Ilustración artística: una interpretación, no un registro histórico.

¿Sabías que…?

Las Trompetas de Plata y la Partida del Sinaí

  • Dos trompetas de plata labrada a martillo servían como sistema de comunicación de Israel en el desierto, tocadas exclusivamente por los sacerdotes hijos de Aarón con toques largos o cortos para reunir a la congregación, ordenar la marcha de los campamentos, dar la alarma en la guerra y anunciar los sacrificios festivos.Fuentes: el propio texto bíblico
  • El día veinte del segundo mes del segundo año tras salir de Egipto, la nube se alzó sobre el tabernáculo, marcando la partida de Israel del desierto de Sinaí tras haber acampado allí casi un año entero, dirigiéndose hacia el desierto de Parán.Fuentes: el propio texto bíblico · Sinai · Paran
  • Moisés rogó a Hobab, hijo de su suegro madianita Reuel, que los acompañara para servirles de ojos, aprovechando su familiaridad con el terreno desértico y los lugares para acampar a cambio de compartir los bienes prometidos a Israel.Fuentes: el propio texto bíblico · Jethro

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Egypt · 30.129, 31.308 · versículo 11
  • Paran · 30.303, 34.777 · versículo 12
  • Wilderness of Sinai · Hoy: about 50 km around Jebel Musa · 28.540, 33.973 · versículo 12

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.