Nehemías 3
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Masu ginin katanga
1Eliyashib babban firist da ’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel. 2Mutanen Yeriko kuwa suka kama ginin daga mahaɗin, Zakkur ɗan Imri kuma ya fara ginin biye da su.
3’Ya’yan Hassenaya ne suka gina Ƙofar Kifi. Suka kafa ginshiƙan, suka kuma sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. 4Kusa da su kuma, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz ne ya yi gyare-gyaren. Biye da shi kuma sai Meshullam ɗan Berekiya, ɗan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi Zadok ɗan Ba’ana shi ma ya yi gyare-gyare. 5Mutanen Tekowa ne suka yi gyare-gyare biye da shi, amma manyan garinsu suka ƙi su sa hannu cikin aikin da shugabanninsu suka bayar.
6Yohiyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodehiya ne suka gyara Ƙofar Yeshana. Suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. 7Biye da su, mutanen Gibeyon da Mizfa Melatiya na Gibeyon da Yadon Meronot waɗanda suke ƙarƙashin ikon gwamnan Kewayen Kogin Yuferites ne suka yi gyare-gyaren. 8Uzziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin masu ƙeran zinariya ne ya yi gyare-gyaren sashe na biye; sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyaren biye da wannan. Suka gyara Urushalima har zuwa Katanga Mai Faɗi. 9Refahiya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyaren sashe na biye. 10Kusa da Refahiya, Yedahiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyaren daga gaban gidansa, sai Hattush ɗan Hashabnehiya ya yi gyare-gyaren biye da shi. 11Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-Mowab ya yi gyare-gyaren wani sashe da kuma Hasumiyar Wurin Gashi. 12Shallum ɗan Hallohesh, mai mulkin ɗayan rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyaren sashe na biye tare da taimakon ’ya’yansa mata.
13Hanun da mazaunan Zanowa ne suka gyara Ƙofar Kwari. Suka sāke gina ta suka sa ƙofofinta, da sakatunta, da sandunan ƙarfenta a wurarensu. Suka kuma gyara yadi ɗari biyar na katangar har zuwa Ƙofar Juji.
14Malkiya ɗan Rekab mai mulkin yankin Bet-Hakkerem ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Juji. Ya sāke gina ta ya kuma sa sakatunta, da sanduna ƙarfenta a wurarensu.
15Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda. 16Gaba da shi, Nehemiya ɗan Azbuk, mai mulkin rabin yankin Bet-Zur ne ya yi gyare-gyaren har zuwa kusa da kaburburan Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da kuma Gidan Jarumawa.
17Biye da shi, Lawiyawa a ƙarƙashin Rehum ɗan Bani ne suka yi gyare-gyaren. Kusa da su, Hashabiya mai mulkin rabin yankin Keyila ne ya yi gyare-gyaren don yankinsa. 18Biye da shi, ’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren. 19Biye da su, Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya yi gyara wani sashe, daga inda yake fuskantar hawan gidan makamai har zuwa kusurwa. 20Biye da shi, Baruk ɗan Zakkai da ƙwazo ya gyara wani sashe, daga kusurwa zuwa mashigin gidan Eliyashib babban firist. 21Biye da shi, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya yi gyaran wani sashe, daga mashigin gidan Eliyashib zuwa ƙarshensa.
22Firistoci daga kewayen yankin ne suka yi gyare-gyaren biye da shi. 23Can gaba da su, Benyamin da Hasshub ne suka yi gyare-gyaren a gaban gidansu, biye da su kuwa, Azariya ɗan Ma’asehiya, ɗan Ananiya ne ya yi gyare-gyaren kusa da gidansa. 24Biye da shi, Binnuyi ɗan Henadad ya yi gyaran wani sashe, daga gidan Azariya zuwa kusurwa, 25sai Falal ɗan Uzai ya yi aiki ɗaura da kusurwa da kuma doguwar hasumiya daga fadar da take bisa kusa da shirayin masu tsaro. Biye da shi, Fedahiya ɗan Farosh 26da masu hidimar haikali da suke zama a tudun Ofel ne suka yi gyare-gyaren har zuwa wani wuri ɗaura da Ƙofar Ruwa wajen gabas da kuma doguwar hasumiya. 27Biye da su, mutanen Tekowa suka yi gyaran wani sashe, daga babbar doguwar hasumiya zuwa katangar Ofel.
28Daga Ƙofar Doki, firistoci ne suka yi gyare-gyaren, kowanne a gaban gidansa. 29Biye da su, Zadok ɗan Immer ya yi gyare-gyaren ɗaura da gidansa. Biye da shi, Shemahiya ɗan Shekaniya, mai tsaron Ƙofar Gabas ya yi gyare-gyare. 30Biye da shi, Hananiya ɗan Shelemiya, da Hanun, ɗa na shida na Zalaf, suka gyara wani sashe. Biye da su, Meshullam ɗan Berekiya ya yi gyare-gyaren ɗaura da wurin zamansa. 31Biye da shi, Malkiya, ɗaya daga cikin masu ƙera zinariya ya yi gyare-gyaren har zuwa gidan masu hidimar haikali da kuma ’yan kasuwa, ɗaura da Ƙofar Bincike, har zuwa ɗakin da yake bisa kusurwar. 32Maƙeran zinariya da ’yan kasuwa suka gyara wani sashi tsakanin ɗakin da yake bisa kusurwa da Ƙofar Tumaki.

¿Sabías que…?
La reconstrucción de las murallas de Jerusalén
- La reconstrucción de las defensas de Jerusalén se organizó en tramos consecutivos alrededor de todo el perímetro, comenzando y terminando en la Puerta de las Ovejas, en la muralla oriental. El sumo sacerdote Eliasib y los demás sacerdotes iniciaron la labor reconstruyendo y consagrando dicha puerta.Fuentes: el propio texto bíblico · Sheep Gate · Eliashib
- El proyecto congregó a diversos grupos de la región, entre ellos gobernantes de distritos como Mizpa y Keila, orfebres, perfumistas, comerciantes y sacerdotes. Muchos repararon los tramos situados frente a sus propias casas, y líderes como Salum trabajaron junto con sus hijas.Fuentes: el propio texto bíblico · Mizpah · Keilah
- Los trabajos abarcaron lugares emblemáticos de la antigua ciudad, como la Muralla Ancha, el estanque de Siloé junto al huerto del rey, las gradas de la Ciudad de David y el Ofel, una elevación en la ladera sur de la colina del templo donde habitaban los sirvientes del templo.Fuentes: el propio texto bíblico · Ophel · David
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Sheep Gate · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 1, 32
- Tower of Hananel · Hoy: Antonia Fortress · 31.780, 35.234 · versículo 1
- Tower of the Hundred · Hoy: within 500 m of the Antonia Fortress · 31.780, 35.234 · versículo 1
- Jericho · Hoy: Tell es Sultan · 31.872, 35.445 · versículo 2
- Fish Gate · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 3
- Tekoa · Hoy: Khirbet Teku’a · 31.632, 35.210 · versículos 5, 27
- Gate of Yeshanah · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 6
- Beyond the River · 31.777, 35.234 · versículo 7
- Gibeon · Hoy: El Jib · 31.847, 35.183 · versículo 7
- Broad Wall · 31.776, 35.232 · versículo 8
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 8, 9, 12
- Tower of the Ovens · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 11
- Dung Gate · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 13, 14
- City of David · 31.774, 35.236 · versículo 15
- Fountain Gate · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 15
- Siloam · Hoy: Pool of Siloam · 31.771, 35.235 · versículo 15
- Angle · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 19, 20, 24, 25
- Ophel · 31.775, 35.236 · versículos 26, 27
- Water Gate · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 26
- Horse Gate · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 28
- East Gate · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 29
- Muster Gate · Hoy: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 31
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org