Josué 21
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Garuruwa domin Lawiyawa
1To, a lokacin, sai shugabannin iyalan Lawiyawa suka je wurin Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin sauran iyalan kabilu na Isra’ila a 2Shilo cikin Kan’ana, suka ce musu, “ Ubangiji ya yi umarni ta wurin Musa cewa a ba mu garuruwan da za mu zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau don dabbobinmu.”
3Saboda haka kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.
4Ƙuri’a ta farko ta fāɗa a kan Kohatawa bisa ga iyalansu. Sai aka ba wa Lawiyawa waɗanda suke ’yan zuriyar Haruna, firist, garuruwa goma sha uku daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin.
5Sauran Kohatawan kuma aka ba su garuruwa goma daga iyalan kabilar Efraim, Dan da kuma rabi kabilar Manasse.
6Aka kuma ba wa zuriyar Gershon garuruwa goma sha uku daga iyalan kabilan Issakar, Asher, Naftali, da kuma rabin kabilar Manasse a Bashan.
7Aka ba wa zuriyar Merari bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.
8Haka Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo masu kyau, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.
9Daga kabilan Yahuda da Simeyon ne aka ba su waɗannan garuruwan da aka ambata, 10(ga garuruwan da aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga iyalan Kohatawa na Lawiyawa, domin ƙuri’a ta farko ta fāɗa a kansu),
11an ba su, Kiriyat Arba (wato, Hebron), da wurin kiwon da yake kewaye da ƙasar kan tudu ta Yahuda. (Arba shi ne kakan Anak.) 12Amma sai aka ba Kaleb ɗan Yefunne filayen da kuma ƙauyukan da suke kewaye da birnin, su zama nasa. 13Sai aka ba zuriyar Haruna firist, ƙasar Hebron (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Libna, 14da Yattir, da Eshtemowa, 15da Holon, da Debir, 16da Ayin, da Yutta, da kuma Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa tara ke nan daga kabilun nan biyu, Yahuda da Simeyon.
17Daga kabilar Benyamin kuwa aka ba su,
Gibeyon, Geba, 18Anatot da Almon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan. 19Duka-duka garuruwan firistoci, zuriyar Haruna, su goma sha uku ne tare da wuraren kiwonsu.
20Aka kuma ba wa sauran Kohatawa, iyalan Lawiyawa, garuruwa daga kabilar Efraim.
21A ƙasar kan tudu ta Efraim, aka ba su,
Shekem (garin masu neman mafaka don sun yi kisa) da Gezer, 22Kibzayim da Bet-Horon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.
23Haka kuma daga kabilar Dan, aka ba su,
Elteke, Gibbeton, 24Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.
25Daga rabin kabilar Manasse kuwa aka ba su,
Ta’anak da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan. 26Dukan garuruwan nan goma tare da wuraren kiwonsu ne aka ba sauran iyalan Kohatawa.
27Aka ba wa zuriyar Gershon, waɗanda suke Lawiyawa, rabo.
Daga rabin kabilar Manasse,
Golan a cikin Bashan (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Be’eshtera, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan;
28daga kabilar Issakar kuma aka ba su
Kishiyon, Daberat, 29Yarmut da En Gannim, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;
30daga kabilar Asher kuwa aka ba su,
Mishal, Abdon, 31Helkat da Rehob, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;
32daga kabilar Naftali kuma aka ba su,
Kedesh a cikin Galili (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Hammon-Dor da kuma Kartan, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa uku ke nan. 33Duka-duka, garuruwan iyalan Gershonawa goma sha uku ne, tare da wuraren kiwonsu.
34Aka ba wa iyalan Merari (sauran Lawiyawa) garuruwa,
daga kabilar Zebulun,
wato, Yokneyam, Karta, 35Dimna da kuma Nahalal, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;
36daga kabilar Ruben kuma aka ba su,
Bezer, Yahza, 37Kedemot da kuma Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;
38daga kabilar Gad kuwa aka ba su,
Ramot Gileyad (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Mahanayim, 39Heshbon da kuma Yazer, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan. 40Duka-duka garuruwan da aka ba iyalan mutanen Merari, waɗanda su ne sauran Lawiyawa, garuruwa goma sha biyu ne.
41Jimillar birane da wurarensu na kiwon da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama’ar Isra’ila guda arba’in da takwas ne. 42Dukan garuruwan nan kowannensu yana kewaye da wurin kiwo.
43Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa dukan ƙasar da ya yi wa kakanninsu alkawari, suka kuwa mallake ta, suka zauna a cikinta. 44Ubangiji ya ba su hutawa a kowane gefe kamar yadda ya yi wa kakanninsu alkawari, ba ko ɗaya daga cikin abokan gābansu da ya iya cinsu da yaƙi. 45Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alherin da ya yi wa mutanen Isra’ila.

¿Sabías que…?
Las Ciudades de los Levitas
- A diferencia de las otras tribos de Israel, la tribu de Leví no recibió un territorio regional continuo. En su lugar, se les asignaron cuarenta y ocho ciudades individuales con sus pastos circundantes, distribuidas entre las tierras de todas las demás tribus.Fuentes: el propio texto bíblico
- La distribución de estas ciudades se llevó a cabo en Silo, en Canaán, donde los jefes de las familias levíticas presentaron su petición al sacerdote Eleazar, a Josué y a los líderes tribales, conforme a lo ordenado previamente por medio de Moisés.Fuentes: el propio texto bíblico · Shiloh · Canaan
- Varias ciudades levíticas destacadas también sirvieron como ciudades de refugio para personas que buscaban protección tras una muerte involuntaria, entre ellas Hebrón en Judá, Siquem en Efraín y Golán en Basán.Fuentes: el propio texto bíblico · Hebron · Bashan
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Canaan · 32.767, 35.333 · versículo 2
- Shiloh · Hoy: Khirbet Seilun · 32.056, 35.290 · versículo 2
- Bashan · 32.781, 35.935 · versículos 6, 27
- Hebron · Hoy: Tel Rumeida · 31.525, 35.102 · versículos 11, 13
- Jattir · Hoy: Khirbet Attir · 31.352, 35.016 · versículo 14
- Gibeon · Hoy: El Jib · 31.847, 35.183 · versículo 17
- Gezer · Hoy: Tel Gezer · 31.859, 34.919 · versículo 21
- Shechem · Hoy: Tell Balatah · 32.214, 35.282 · versículo 21
- Beth-horon · Hoy: Beit Ur al Tahta · 31.895, 35.084 · versículo 22
- Taanach · Hoy: Tell Ta’anakh · 32.522, 35.219 · versículo 25
- Galilee · 32.760, 35.527 · versículo 32
- Jokneam · Hoy: Tel Yokneam · 32.664, 35.108 · versículo 34
- Gilead · Hoy: Gilead 1 · 32.187, 35.692 · versículo 38
- Ramoth · Hoy: Tall er Rumeith · 32.500, 36.015 · versículo 38
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org