Josué 19
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Rabon don kabilar Simeyon
1Ƙuri’a ta biyu ta fāɗa a kan kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu ta gādo tana cikin yankin Yahuda. 2Waɗannan su ne wuraren da suka gāda.
Beyersheba (ko Sheba), Molada, 3Hazar Shuwal, Bilha, Ezem, 4Eltolad, Betul, Horma, 5Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa, 6Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.
7Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu, 8da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). 9Daga cikin gādon mutanen Yahuda ne aka fitar da gādon kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu, domin rabon da kabilar Yahuda suka samu ya fi ƙarfin abin da suke bukata. Saboda haka kabilar gādon Simeyon yana cikin harabar Yahuda.
Rabon da kabilar Zebulun ta samu
10Ƙuri’a ta uku ta fāɗa a kan Zebulun bisa ga iyalansu.
Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kai har Sarid. 11Ta nufi yamma zuwa Marala, ta taɓa Dabbeshet, ta wuce zuwa rafin da yake kusa da Yokneyam. 12Daga Sarid, ta juya gabas zuwa harabar Kislot Tabor, ta kuma wuce zuwa Daberat har zuwa Yafiya. 13Sa’an nan ta ci gaba, ta yi gabas zuwa Gat-Hefer da Et Kazin; ta ɓulla a Rimmon, ta juya zuwa Neya. 14A can ne iyakar ta kewaya zuwa Hannaton, sa’an nan ta ƙarasa a Kwarin Ifta El.
15Zebulun ta ƙunshi garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu. Garuruwan sun haɗa da Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem. 16Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Zebulun ta samu, bisa ga iyalansu.
Rabon da kabilar Issakar ta samu
17Ƙuri’a ta huɗu ta fāɗa a kan kabilar Issakar, bisa ga iyalansu. 18Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da,
Yezireyel, Kessulot, Shunem, 19Hafarayim, Anaharat, 20Rabbat, Kishiyon, Ebez, 21Remet, En Gannim, En Hadda da Bet-Fazez.
22Iyakar ta taɓa Tabor Shahazuma da Bet-Shemesh ta kuma ƙarasa a Urdun.
Duka-duka garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu. 23Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Issakar ta samu, bisa ga iyalansu.
Rabon da kabilar Asher ta samu
24Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu. 25Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da,
Helkat, Hali, Beten, Akshaf, 26Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat. 27Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu, 28ta kai Abdon, Rehob, Hammon da Kana, har zuwa Sidon Babba. 29Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib, 30Umma, Afek da Rehob.
Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu. 31Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu.
Rabon da kabilar Naftali ta samu
32Ƙuri’a ta shida ta fāɗa a kan kabilar Naftali, bisa ga iyalansu.
33Iyakarsu ta kama daga Helef, daga babban itacen Mamre nan da yake a Za’anannim, ta wuce Adami Nekeb da Yabneyel zuwa Lakkum, ta kuma ƙarasa a Urdun. 34Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas.
35Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret, 36Adama, Rama, Hazor, 37Kedesh, Edireyi, En Hazor, 38Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh.
Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu. 39Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Naftali ta samu, bisa ga iyalansu.
Rabon da kabilar Dan ta samu
40Ƙuri’a ta bakwai ta fāɗa a kan kabilar Dan, bisa ga iyalansu. 41Ƙasarsu ta gādo ta haɗa da,
Zora, Eshtawol, Ir Shemesh, 42Shalim, Aiyalon, Itla, 43Elon, Timna, Ekron, 44Elteke, Gibbeton, Ba’alat, 45Yehud, Bene-Berak, Gat-Rimmon, 46Me Yarkon da Rakkon tare da sashen da yake fuskantar Yaffa. 47(Amma ya zama wa mutanen kabilar Dan da wahala su mallaki ƙasar da aka ba su gādo, saboda haka sai suka nufi Leshem suka ci su da yaƙi, suka karkashe mutanen wurin, suka mallake ta, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato, Dan.) 48Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan, bisa ga iyalansu.
Rabon da Yoshuwa ya samu
49Sa’ad da aka gama raba gādon ƙasar bisa ga ƙuri’a. Sai Isra’ilawa suka ba Yoshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikinsu, 50yadda Ubangiji ya umarta, suka ba shi garin da ya ce a ba shi, Timnat Serad a ƙasar tudu ta Efraim. Ya kuma gina garin ya zauna a can.
51Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin kabilan iyalan Isra’ila suka rarraba ta hanyar jefa ƙuri’a a Shilo a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Da haka suka yi suka gama rarraba ƙasar.

¿Sabías que…?
La repartición final de la tierra
- Simeón recibió una herencia ubicada por completo dentro del territorio mayor de Judá, debido a que la porción de Judá se consideraba demasiado extensa para ellos. Esto incluía asentamientos del sur como Berseba y Molada.Fuentes: el propio texto bíblico · Simeon · Beersheba · Moladah
- Dan fue la última tribu en recibir su asignación de tierra, situada en la frontera occidental hacia el mar. Cuando los danitas tuvieron dificultades para retener su territorio original, marcharon al norte, conquistaron la ciudad de Lesem y la rebautizaron Dan en honor a su antepasado.Fuentes: el propio texto bíblico · Dan
- Solo después de completarse la división de las tierras tribales, los líderes otorgaron a Josué hijo de Nun su herencia personal. Él solicitó y recibió la ciudad de Timnat-seraj en la región montañosa de Efraín, la cual reconstruyó y donde se estableció.Fuentes: el propio texto bíblico · Joshua
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Negeb · 31.245, 34.841 · versículo 8
- Jokneam · Hoy: Tel Yokneam · 32.664, 35.108 · versículo 11
- Bethlehem · Hoy: Beit Lahm · 32.735, 35.186 · versículo 15
- Shunem · Hoy: Sulam · 32.606, 35.334 · versículo 18
- Jordan · Hoy: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículos 22, 33, 34
- Mount Tabor · Hoy: Jebel et Tur · 32.686, 35.393 · versículo 22
- Mount Carmel · 32.672, 35.023 · versículo 26
- Sidon · Hoy: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · versículo 28
- Great Sea · Hoy: Mediterranean Sea · 31.805, 34.170 · versículo 29
- Tyre · 33.271, 35.196 · versículo 29
- Allon · Hoy: in Hanot Taggarim · 32.721, 35.411 · versículo 33
- Hazor · Hoy: Tel Hazor · 33.018, 35.569 · versículo 36
- Kedesh · Hoy: Tel Kedesh · 33.112, 35.530 · versículo 37
- Ir-shemesh · Hoy: Tel Bet Shemesh · 31.751, 34.975 · versículo 41
- Ekron · Hoy: Tel Miqne · 31.777, 34.852 · versículo 43
- Joppa · Hoy: Jaffa · 32.054, 34.753 · versículo 46
- Dan · Hoy: Tel Dan · 33.249, 35.652 · versículo 47
- Shiloh · Hoy: Khirbet Seilun · 32.056, 35.290 · versículo 51
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org