Josué 17
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Wannan shi ne gādon da aka ba wa kabilar Manasse, a matsayin ɗan farin Yusuf. Manasse yana da ɗan farin mai suna Makir. Makir shi ne mahaifin mutanen Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan gama Makiriyawa jarumai ne ƙwarai. 2Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manasse rabon gādonsu bisa ga iyalansu, wato, Abiyezer, Helek, Asriyel, Shekem, Hefer da Shemida. Waɗannan su ne ’ya’yan Manasse, maza, ɗan Yusuf bisa ga iyalansu.
3Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse ba shi da ’ya’ya maza, sai dai mata. Ga sunayensu, Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza. 4Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “ Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji. 5Dalilin ke nan Manasse ya sami kashi goma ban da ƙasar Gileyad da Bashan a gabashin Urdun, 6domin ’ya’ya mata na kabilar Manasse sun sami gādo tare da ’ya’ya maza. Aka ba wa sauran mutanen kabilar Manasse ƙasar Gileyad.
7Iyakar ƙasar Manasse ta tashi daga Asher zuwa Mikmetat a gabashin Shekem. Iyakar kuma ta miƙe har zuwa kudu wadda ta ƙunshi mutanen da suke zaune a En Taffuwa. 8(Manasse ne yake da ƙasar Taffuwa, amma garin Taffuwa kansa, a kan iyakar Manasse ta mutanen Efraim ce.) 9Sa’an nan iyakar ta ci gaba ta yi kudu zuwa Rafin Kana. Akwai garuruwan da suke kudancin rafin, waɗanda suke Efraim, ko da yake suna cikin yankin Manasse. Iyakar Manasse ta miƙe zuwa arewa ta bi gefen rafin ta kuma ƙarasa a Bahar Rum. 10Ƙasar a wajen kudu ta Efraim ce, ta wajen arewa kuma ta Manasse ce. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Asher yana wajen arewa, Issakar kuma a wajen gabas.
11A yanki tsakanin Issakar da Asher, Manasse yana da waɗannan wurare, Bet-Sheyan, Ibileyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan En Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta (Na uku cikin jerin shi ne Nafot).
12Duk da haka mutanen Manasse ba su iya mallakar garuruwan nan ba, domin Kan’aniyawa sun nace da zama a wannan yanki. 13Da Isra’ilawa suka yi ƙarfi, sai suka sa Kan’aniyawa suka zama masu yin musu aiki, amma ba su iya korarsu duka ba.
14Mutanen Yusuf kuwa suka ce wa Yoshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo ɗaya kawai? Ga shi muna da yawa kuma Ubangiji ya albarkace mu sosai.”
15Yoshuwa ya ce musu, “In kuna da yawa sosai, in kuma ƙasar kan tudu ta Efraim ba ta ishe ku ba, sai ku je cikin jeji, ku nema wa kanku ƙasa a ƙasar Ferizziyawa da Refahiyawa.”
16Mutanen Yusuf suka amsa suka ce, “Ƙasar kan tudu ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan’aniyawan da suke zama a filin, da waɗanda suke Bet-Sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke Kwarin Yezireyel, duk suna da keken yaƙin ƙarfe.”
17Amma Yoshuwa ya ce wa mutanen Yusuf, wa Efraim da Manasse, “Kuna da yawa, kuna kuma da ƙarfi sosai. Ba wuri ɗaya kaɗai za ku samu gādo ba, 18amma har da ƙasar kan tudu ma, ko da yake jeji ne, ku je ku gyara shi, duk yă zama naku. Ko da yake Kan’aniyawa suna da kekunan yaƙi na ƙarfe, suna kuma da ƙarfi, duk da haka za ku kore su.”

¿Sabías que…?
La heredad de Manasés y la casa de José
- La tribu de Manasés quedó dividida geográficamente a ambos lados del río Jordán. Debido a que el clan de Maquir era reconocido en la guerra, ya había recibido los territorios orientales de Galaad y Basán, mientras que el resto de los clanes recibió diez porciones al oeste del Jordán.Fuentes: el propio texto bíblico · Machir · Gilead · Bashan
- Las hijas de Zelofejad —Maala, Noa, Hogla, Milca y Tirsa— se presentaron ante Josué y el sacerdote Eleazar para reclamar el derecho de propiedad ordenado por el Señor a través de Moisés. Así, recibieron una herencia de tierras junto con los hermanos de su padre.Fuentes: el propio texto bíblico · Hepher · Machir
- Cuando las tribus de la casa de José se quejaron de que su territorio era insuficiente, Josué les ordenó desmontar y ocupar la zona boscosa de las colinas en lugar de temer a los cananeos de los valles, quienes contaban con carros de hierro en ciudades como Bet-sán.Fuentes: el propio texto bíblico · Joshua · Beth-shean
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Bashan · 32.781, 35.935 · versículos 1, 5
- Gilead · Hoy: Gilead 1 · 32.187, 35.692 · versículos 1, 5, 6
- Jordan · Hoy: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículos 1, 2, 5
- Shechem · Hoy: Tell Balatah · 32.214, 35.282 · versículo 7
- Great Sea · Hoy: Mediterranean Sea · 31.805, 34.170 · versículos 9, 10
- Megiddo · Hoy: Tel Megiddo · 32.585, 35.184 · versículo 11
- Taanach · Hoy: Tell Ta’anakh · 32.522, 35.219 · versículo 11
- Valley of Jezreel · Hoy: Jezreel Valley · 32.596, 35.242 · versículo 16
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org