Jeremías 46
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Saƙo game da Masar
1Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da al’ummai.
2Game da Masar.
Ga saƙo game da sojojin Fir’auna Neko sarkin Masar, wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ci da yaƙi a Karkemish a Kogin Yuferites a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda.
3“Ku shirya garkuwoyinku, manya da ƙanana,
ku kuma fito don yaƙi!
4Ku shirya dawakai,
ku sa musu sirdi!
Ku tsaya a wurarenku
saye da hulunan kwano a kai!
Ku wasa māsunku,
ku yafa kayan yaƙinku!
5Me nake gani?
Sun tsorata,
suna ja da baya,
an ci jarumawansu.
Suna gudu da sauri
ba waiwayawa,
akwai razana a kowane gefe,”
in ji Ubangiji.
6“Masu saurin gudu ba sa iya gudu
haka ma masu ƙarfi ba sa iya kuɓuta.
A arewa ta Kogin Yuferites
sun yi tuntuɓe sun fāɗi.
7“Wane ne wannan mai tashi kamar Nilu,
kamar koguna masu tafasar ruwaye?
8Masar tana tashi kamar Nilu,
kamar koguna masu tafasa.
Tana cewa, ‘Zan tashi in rufe duniya;
zan hallakar da birane da kuma mutanensu.’
9Ku yi sukuwar hauka, ya dawakai!
Ku tashi a guje, ya mahayan kekunan yaƙi!
Ku yi ta fitowa, ya jarumawa,
mutanen Kush da kuma Ludim masu riƙon garkuwoyi,
mutanen Lidiya, masu iya jan baka.
10Amma wannan rana ta Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki
ranar ɗaukar fansa, gama ɗaukar fansa a kan maƙiyansa.
Takobi zai yi ta ci sai ya gamsu,
sai ya kashe ƙishirwansa da jini.
Gama Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, zai miƙa hadaya
a ƙasar arewa kusa da Kogin Yuferites.
11“Ki haura Gileyad ki samo magani,
Ya Budurwa ’Yar Masar.
Amma kin riɓanya magani a banza;
ba magani dominki.
12Al’ummai za su ji game da kunyar da kika sha;
kukanki zai cika duniya.
Jarumi zai yi tuntuɓe a kan wani;
dukansu biyu za su fāɗi tare.”
13Ga saƙon da Ubangiji ya yi wa Irmiya annabi game da zuwan Nebukadnezzar sarkin Babilon don yă yaƙi Masar.
14“Ka yi shelar wannan a Masar, ka kuma furta shi a Migdol;
ka yi shelarsa kuma a Memfis da Tafanes.
‘Ku ɗauki matsayinku ku kuma shirya,
gama takobi na cin waɗanda suke kewaye da ku.’
15Me zai sa a wulaƙanta jarumawanka haka?
Ba za su iya tsayawa ba, gama Ubangiji zai ture su ƙasa.
16Za su yi ta tuntuɓe;
za su fāɗi akan juna.
Za su ce, ‘Mu tashi, mu koma
zuwa wurin mutanenmu da kuma ƙasashenmu,
daga takobin masu danniya.’
17A can za su tā da murya su ce,
‘Fir’auna sarkin Masar mai yawan surutu ne kawai;
ya bar zarafi ya wuce masa.’
18“Muddin ina raye,” in ji Sarki,
wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki,
“wani zai ɓullo wanda yake kamar Tabor a cikin duwatsu,
kamar Karmel kusa da teku.
19Ku tattara kayanku don shirin zuwa zaman bauta,
ku da kuke zama a Masar,
gama Memfis za tă zama kufai
ta zama kango, babu mazauna.
20“Masar kyakkyawar karsana ce,
amma bobuwa tana zuwa a kanta daga arewa.
21Sojojin da ta yi hayarsu a cikinta
suna kamar ’yan maruƙa masu kitse.
Su ma za su juya su kuma gudu gaba ɗaya,
ba za su iya tsayawa ba,
gama ranar masifa tana zuwa a kansu,
lokacin da za su sha hukunci.
22Masar za tă yi huci kamar macijin da yake gudu
yayinda abokin gāba yana matsowa da ƙarfi;
za su fāɗo mata gatura
kamar mutanen da suke saran itatuwa.
23Za su sari kurminta,” in ji Ubangiji,
“ko da yake yana maƙare da itatuwa.
Sun fi fāra yawa,
ba su ƙidayuwa.
24Za a kunyatar da Diyar Masar,
da aka bashe ga mutanen arewa.”
25Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ina gab da kawo hukunci a kan allahn Amon na Tebes, a kan Fir’auna, a kan Masar da allolinta da sarakunanta, da kuma a kan waɗanda suka dogara ga Fir’auna. 26Zan ba da su ga waɗanda suke neman ransu, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da fadawansa. Amma daga baya, Masar za tă kasance da mazauna kamar dā,” in ji Ubangiji.
27“Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana;
kada ka karai, ya Isra’ila.
Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nisa,
zuriyarka daga ƙasar bautarsu.
Yaƙub zai sāke kasance cikin salama, rai kwance,
babu kuma wanda zai sa ya ji tsoro.
28Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana,
gama ina tare da kai,” in ji Ubangiji.
“Ko da na hallaka dukan al’ummai sarai
inda na kora ka, ba zan hallaka ka sarai ba.
Zan hore ka amma da adalci kaɗai;
ba zan bar ka ba hukunci ba.”

¿Sabías que…?
El juicio sobre Egipto y la Batalla de Carquemis
- Jeremías fecha esta profecía en el cuarto año del rey Joacim de Judá, cuando Nabucodonosor de Babilonia derrotó al faraón Necao de Egipto en Carquemis, junto al río Éufrates. Este enfrentamiento decisivo marcó un cambio trascendental de poder en la región, poniendo fin al dominio egipcio sobre las tierras vecinas.Fuentes: el propio texto bíblico · Carchemish · Jehoiakim
- El capítulo utiliza la crecida anual del río Nilo como imagen del orgulloso avance militar de Egipto sobre la tierra. También advierte a destacadas ciudades egipcias como Menfis (llamada Nof en hebreo), la antigua capital del Bajo Egipto, sobre la devastación y el exilio venideros.Fuentes: el propio texto bíblico · Nile · Memphis
- La profecía predice una invasión babilónica directa contra Egipto bajo el mando de Nabucodonosor. El juicio anunciado se dirigía no solo contra el faraón y sus tropas, sino también contra Amón, la deidad principal de Tebas, y los demás dioses de Egipto.Fuentes: el propio texto bíblico · Nebuchadnezzar
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Babylon · 32.543, 44.422 · versículos 2, 13, 18, 26
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 2, 8, 9, 11, 13, 14, 17, 18, 19, 20, 21, 22, 23, 24, 25, 26
- Euphrates · Hoy: Euphrates River · 31.004, 47.442 · versículos 2, 6, 10
- Nile · Hoy: Nile River · 31.465, 30.367 · versículos 7, 8
- Cush · Hoy: Cush 1 · 16.935, 33.751 · versículo 9
- Gilead · Hoy: Gilead 1 · 32.187, 35.692 · versículo 11
- Memphis · 29.849, 31.253 · versículos 14, 19
- Tahpanhes · Hoy: Tell Defenneh · 30.861, 32.171 · versículo 14
- Mount Carmel · 32.672, 35.023 · versículo 18
- Mount Tabor · Hoy: Jebel et Tur · 32.686, 35.393 · versículo 18
- Thebes · 25.721, 32.610 · versículo 25
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org