Jeremías 22
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Hukunci a kan mugayen sarakunan Yahuda
1Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce, 2‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi. 3Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri. 4Gama in ka lura da bin waɗannan umarnai, to, sarakunan da suke zaune a gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan fada, suna hawan kekunan yaƙi da dawakai, fadawansu da mutanensu suna musu rakiya. 5Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’ ”
6Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da wannan fadar sarkin Yahuda,
“Ko da yake kina kamar Gileyad a gare ni,
kamar ƙwanƙolin Lebanon,
tabbatacce zan maishe ki hamada,
kamar garuruwan da ba mazauna.
7Zan aika da mai hallakarwa a kanki,
kowane mutum da makamansa,
za su kuma yayyanka gumaguman al’ul na ki masu kyau
su jefa su cikin wuta.
8“Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’ 9Amsar kuwa za tă zama, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada suka kuma bauta wa waɗansu alloli.’ ”
10Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa;
a maimako, ku yi kuka mai zafi saboda wanda aka kai zaman bauta,
domin ba zai ƙara dawowa ba
ko ya ƙara ganin ƙasarsa ta haihuwa.
11Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shallum ɗan Yosiya, wanda ya gāji mahaifinsa a matsayin sarkin Yahuda amma bai bar wurin nan ba, “Ba zai ƙara dawowa ba. 12Zai mutu a inda suka kai shi zaman bauta; ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.”
13“Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci,
ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya,
yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza
ba ya biyansu wahalarsu.
14Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada
da manyan ɗakuna.’
Ta haka sai ya yi musu manyan tagogi
ya manne musu al’ul
ya yi musu ado kuma da ruwan ja.
15“Wannan zai mai da kai sarki ne
in kana da al’ul a kai a kai?
Mahaifinka bai kasance da abinci da abin sha ba?
Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai
saboda haka kome ya kasance da lafiya da shi.
16Ya kāre muradin matalauta da mabukata,
ta haka kome ya tafi masa daidai.
Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?”
In ji Ubangiji.
17“Amma idanunka da zuciyarka
sun kahu kawai a kan ƙazamar riba,
da a kan zub da jinin marar laifi
da kuma a kan danniya da zalunci.”
18Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda,
“Ba za su yi kuka dominsa ba,
‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’
Ba za su yi kuka dominsa ba,
‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’
19Za a binne shi kamar jaki
za a ja shi a ƙasa a jefar
a bayan ƙofofin Urushalima.”
20“Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka,
bari a ji muryarka a Bashan,
yi kuka daga Abarim,
gama an murƙushe dukan abokanka.
21Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya,
amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’
Wannan halinka ne tun kana matashi;
ba ka yi mini biyayya ba.
22Iska za tă koro dukan makiyayanka
abokanka kuma za su tafi zaman bauta.
Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka
saboda dukan muguntarka.
23Kai da kake zama a ‘Lebanon,’
kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul
za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka,
zafi kamar na mace mai naƙuda!
24“Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka. 25Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa. 26Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu. 27Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.”
28Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya,
abin da babu wanda yake so?
Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa
a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba?
29Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa,
ki ji maganar Ubangiji!
30Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya,
mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba,
gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara
babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda
ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.”

¿Sabías que…?
Juicios sobre los reyes de Judá
- Salum, también conocido como Joacaz, fue elegido por el pueblo para suceder a su padre Josías, pero fue depuesto y llevado cautivo a Egipto por el faraón Necao tras reinar solo unos meses, convirtiéndose en el primer rey de Judá en morir en el exilio.Fuentes: el propio texto bíblico · Jehoahaz · Jehoiakim
- El profeta contrasta marcadamente al rey Josías con su hijo Joacim. Mientras Josías defendió la justicia y la causa de los pobres, Joacim recurrió al trabajo forzado no remunerado para edificar un suntuoso palacio recubierto de cedro y pintado de bermellón.Fuentes: el propio texto bíblico · Josiah · Jehoiakim
- Conías, otro nombre para el rey Joaquín o Jeconías, fue deportado a Babilonia por el rey Nabucodonosor, cumpliendo la profecía de Jeremías de que moriría en tierra extranjera y que ninguno de sus descendientes volvería a reinar en el trono de David en Judá.Fuentes: el propio texto bíblico · Jehoiachin · Nebuchadnezzar
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 4, 19, 20
- Gilead · Hoy: Gilead 1 · 32.187, 35.692 · versículo 6
- Lebanon · 33.540, 35.584 · versículos 6, 20, 23
- Abarim · 31.754, 35.715 · versículo 20
- Bashan · 32.781, 35.935 · versículo 20
- Babylon · 32.543, 44.422 · versículo 25
- Chaldea · 30.962, 46.104 · versículo 25
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org