Jeremías 18
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
A gidan mai ginin tukwane
1Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji. 2“Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.” 3Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen. 4Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.
5Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 6“Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila. 7A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki, 8in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata. 9In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta, 10in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.
11“Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’ 12Amma za su amsa su ce, ‘Ba amfani. Za mu ci gaba da shirye-shiryenmu; kowannenmu zai bi taurin muguwar zuciyarsa.’ ”
13Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ku tattambaya a cikin al’ummai.
Wa ya taɓa jin irin wannan abu?
Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu
mafi banƙyama.
14Dusar ƙanƙarar Lebanon
ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon?
Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa
sun taɓa daina gudu?
15Duk da haka mutanena sun manta da ni;
sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani,
waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu
a hanyoyin dā.
Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi
a hanyoyin da ba a gina ba.
16Ƙasarsu za tă zama kufai,
abin reni har abada;
dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki
su kaɗa kai.
17Kamar iska daga gabas
zan warwatsa su a gaban abokan gābansu;
zan juya musu bayana, ba zan nuna musu fuskata ba
a ranar masifarsu.”
18Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.”
Addu’ar Irmiya
19Ka saurare ni, ya Ubangiji
ka ji abin da masu zargina suke cewa!
20Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta?
Duk da haka sun haƙa mini rami.
Ka tuna cewa na tsaya a gabanka
na kuma yi magana a madadinsu
don ka janye fushinka daga gare su.
21Saboda haka ka kawo wa ’ya’yansu yunwa;
ka miƙa su ga ikon takobi.
Bari matansu su zama marasa ’ya’ya da gwauraye;
bari a kashe mazansu,
a kuma kashe samarinsu da takobi a yaƙi.
22Bari a ji kuka daga gidajensu
sa’ad da ka kawo masu hari a kansu farat ɗaya,
gama sun haƙa rami don su kama ni
suka kuma kafa tarko wa ƙafafuna.
23Amma Ya Ubangiji,
ka san duk maƙarƙashiyarsu, na neman su kashe ni.
Kada ka gafarta musu laifofinsu
ko ka shafe zunubansu daga gabanka.
Bari a tumɓuke su a gabanka;
ka yi da su sa’ad da kake fushi.

¿Sabías que…?
El Alfarero y el Barro
- En la casa del alfarero, Jeremías observa a un artesano remodelar en el torno una vasija estropeada para hacer otra vasija. El pasaje utiliza este oficio para ilustrar la autoridad divina y el juicio condicional: si una nación advertida se aparta del mal, el castigo se detiene, pero si obra mal, la bendición prevista se retira.Fuentes: el propio texto bíblico
- La profecía contrasta el abandono de Dios por parte de Israel con la constancia de la naturaleza, preguntando si la nieve del Líbano alguna vez abandona sus riscos rocosos. La cordillera del Líbano, cuyo nombre significa blanco, era célebre por sus elevadas cumbres y sus corrientes de aguas frescas.Fuentes: Lebanon · el propio texto bíblico
- La conspiración contra Jeremías surgió de opositores que presumían tener seguridad religiosa, alegando que la ley nunca faltaría al sacerdote, ni el consejo al sabio, ni la palabra al profeta. El mensaje de juicio de Jeremías desafiaba directamente esa confianza institucional.Fuentes: Jeremiah · el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 11
- Lebanon · 33.540, 35.584 · versículo 14
- Mount Hermon · 33.400, 35.850 · versículo 14
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org