Nations Bible

Isaías 37

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

An yi faɗin ceton Urushalima

1Sa’ad da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakkece rigunansa ya kuma sanya tsummoki ya tafi ya shiga haikalin Ubangiji. 2Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz. 3Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da ’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu. 4Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.”

5Sa’ad da shugabannin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya, 6sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo. 7Ka saurara! Zan sa ruhuna a cikinsa saboda sa’ad da ya ji wani labari, zai koma zuwa ƙasarsa, a can kuwa zan sa a kashe shi da takobi.’ ”

8Sa’ad da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye ya kuma sami sarki yana yaƙi da Libna.

9To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana. 10“Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda cewa kada ka bar allahn da ka dogara a kai ya ruɗe ka sa’ad da ya ce, ‘Ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba.’ 11Tabbatacce ka ji abin da sarakunan Assuriya suka aikata ga dukan ƙasashe, suna hallaka su tas. Kai kuwa za ka tsira ne? 12Allolin al’umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne, allolin Gozan, Haran, Rezef da kuma na mutanen Eden waɗanda suke zama a Tel Assar? 13Ina sarkin Hamat yake, sarkin Arfad fa, sarkin Sefarfayim, ko na Hena ko na Iffa?”

Addu’ar Hezekiya

14Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji. 15Sai Hezekiya ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, 16“Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya. 17Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.

18“Gaskiya ce, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriyawa sun mai da dukan waɗannan mutane da ƙasashensu kango. 19Sun jefar da gumakansu cikin wuta suka kuma hallaka su, gama su ba alloli ba ne itace ne kawai da dutse, da hannuwan mutane suka sarrafa. 20Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, saboda masarautai a duniya su san cewa kai kaɗai ne, ya Ubangiji, Allah.”

Fāɗuwar Sennakerib

21Sa’an nan Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Saboda ka yi addu’a gare ni game da Sennakerib sarkin Assuriya, 22ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa,

“Budurwa Diyar Sihiyona

ta rena tana kuma maka ba’a.

Diyar Urushalima

tana kada kai yayinda kake gudu.

23Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo?

A kan wa ka tā da muryarka

ka kuma daga idanu cikin fariya?

A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!

24Ta wurin jakadunka

ka jibge zage-zage a kan Ubangiji.

Ka kuma ce,

‘Da kekunan yaƙina masu yawa

na hau ƙwanƙolin duwatsu,

ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon.

Na sassare al’ul mafi tsayi

fir mafi kyau.

Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.

25Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa

na kuma sha ruwa a can.

Da tafin ƙafafuna

na busar da dukan rafuffukan Masar.’

26“Ba ka ji ba cewa

tun dā can na shirya ya zama haka?

A kwanakin dā na kafa shi;

yanzu na sa ya faru,

cewa ka mai da birane masu mafaka

zuwa tsibin ɓuraguzai.

27Mutanensu, suka rasa ƙarfi,

sun firgita suka kuma sha kunya.

Suka zama kamar tsire-tsire a gona,

kamar tsire-tsiren ta suka tohu,

kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi,

wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.

28“Amma na san inda kake zama

da sa’ad da kakan fita ka kuma koma

da yadda ka harzuƙa gāba da ni.

29Saboda ka harzuƙa gāba da ni

kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana,

zan sa ƙugiya a hancinka

linzamina a bakinka,

zan kuma sa ka koma

ta hanyar da ka zo.

30“Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya,

“Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa,

shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan.

Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba,

za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci ’ya’yansu.

31Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa

za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da ’ya’ya a bisa.

32Gama daga Urushalima raguwa za tă fito,

kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira.

Himmar Ubangiji Maɗaukaki

zai cika wannan.

33“Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya,

“Ba zai shiga wannan birni ba

ya harbe kibiya a nan.

Ba zai zo gabansa da garkuwa ba

ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba.

34Ta hanyar da ya zo da ita zai koma;

ba zai shiga wannan birni ba,”

in ji Ubangiji.

35“Zan kāre wannan birni in kuma cece shi,

saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!”

36Sai mala’ikan Ubangiji ya fita ya kuma karkashe mutane dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar a sansanin Assuriya. Sa’ad da mutane suka farka kashegari, sai ga gawawwaki duk a kwance! 37Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya janye. Ya koma zuwa Ninebe ya zauna a can.

38Wata rana, yayinda yake yin sujada a haikalin allahnsa Nisrok, ’ya’yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka kuma gudu zuwa ƙasar Ararat. Esar-Haddon ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.

Ilustración artística: una interpretación, no un registro histórico.

¿Sabías que…?

La oración de Ezequías y la liberación de Jerusalén

  • Cuando el rey Ezequías recibió la carta amenazante del rey asirio Senaquerib, subió al templo en Jerusalén y extendió el documento ante Dios en oración. En su plegaria señaló que los dioses de las naciones conquistadas habían caído por ser solo obras humanas de madera y piedra, a diferencia del Dios vivo.Fuentes: el propio texto bíblico · Hezekiah
  • El relato menciona a Tirhaca, rey de Cus, quien marchó para combatir a Senaquerib. En aquel periodo, Cus y Egipto se encontraban unificados bajo gobernantes etíopes, lo que constituía una fuerza militar en el sur que se oponía a la expansión asiria.Fuentes: Tirhakah · Cush · el propio texto bíblico
  • Tras el desastre que diezmó a su ejército frente a Jerusalén, Senaquerib se retiró a su capital en Nínive. Mientras adoraba en el templo de su dios Nisroc, sus propios hijos, Adramelec y Sarezer, lo asesinaron.Fuentes: el propio texto bíblico · Sennacherib · Adrammelech

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Assyria · 36.359, 43.153 · versículos 4, 6, 8, 10, 11, 18, 21, 33, 37, 38
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 8, 9, 10, 22, 32, 33
  • Lachish · Hoy: Tell ed Duweir · 31.565, 34.849 · versículo 8
  • Cush · Hoy: Cush 1 · 16.935, 33.751 · versículo 9
  • Eden · Hoy: Beth-eden · 36.701, 38.087 · versículo 12
  • Haran · Hoy: Harran · 36.864, 39.033 · versículo 12
  • Hamath · Hoy: Hama · 35.136, 36.750 · versículo 13
  • Zion · Hoy: Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 22
  • Lebanon · 33.540, 35.584 · versículo 24
  • Mount Carmel · 32.672, 35.023 · versículo 24
  • Egypt · 30.129, 31.308 · versículo 25
  • Mount Zion · 31.772, 35.229 · versículo 32
  • Nineveh · 36.359, 43.153 · versículo 37
  • Ararat · Hoy: Urartu · 39.703, 44.300 · versículo 38

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.