Nations Bible

Isaías 30

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

Kaiton al’umma mai tayarwa

1“Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,”

in ji Ubangiji,

“ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba,

suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba,

suna jibga zunubi a kan zunubi;

2waɗanda suka gangara zuwa Masar

ba tare da sun nemi shawarata;

waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna,

don neman inuwar mafakar Masar.

3Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya,

inuwar Masar za tă jawo muku kunya.

4Ko da yake suna da shugabanni a Zowan

kuma jakadunsu sun iso Hanes,

5kowa zai sha kunya

saboda mutanen da ba su da amfani gare su,

waɗanda ba sa taimako ko amfani,

sai dai jawo kunya da da-na-sani.”

6Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa,

Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari

inda zakoki da zakanya,

inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke,

jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna,

dukiyarsu a kan raƙuma,

zuwa ƙasan nan marar riba,

7zuwa Masar, wadda taimakonta marar amfani ne.

Saboda haka na yi mata laƙabi

Rahab Marar Yin Kome.

8Tafi yanzu, ka rubuta musu a kan allo,

ka rubuta shi a kan littafi,

cewa kwanaki suna zuwa

zai zama madawwamin shaida.

9Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu,

’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.

10Sukan ce wa masu gani,

“Kada ku ƙara ganin wahayi!”

Ga annabawa kuwa sukan ce,

“Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai!

Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai,

ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.

11Ku bar wannan hanya,

ku tashi daga wannan hanya,

ku kuma daina kalubalantarmu

da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!”

12Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa,

“Saboda haka kun ƙi wannan saƙo,

kuka dogara ga aikin kama-karya

kuka kuma dogara ga yin ruɗu,

13wannan zunubi zai zama muku

kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa,

da zai rushe nan da nan, ba tsammani.

14Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu,

ya ragargaje ƙaf

har cikin gutsattsarinsa ba za a sami ko ɗan katanga

don ɗiba garwashin wuta

ko a ɗiba ruwa daga tanki ba.”

15Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa,

“Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake,

cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku,

amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.

16Kun ce, ‘A’a, za mu gudu a kan dawakai.’

Saboda haka za ku gudu!

Kun ce, ‘Za mu hau dawakai masu sauri mu gudu.’

Saboda haka masu fafararku za su fi ku gudu!

17Dubu za su gudu

don barazanar mutum guda;

da jin barazanar mutane biyar

dukanku za ku yi ta gudu

sai an bar ku

kamar sandar tuta a kan dutse,

kamar tuta a kan tudu.”

18Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;

ya tashi don yă nuna muku jinƙai.

Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.

Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!

19Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku. 20Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su. 21Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.” 22Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!”

23Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya. 24Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali. 25A ranar babban kisa, sa’ad da hasumiyoyi za su fāɗi, rafuffukan ruwa za su malalo a kan kowane dutse da kowane tudu mai tsawo. 26Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.

27Duba, Sunan Ubangiji yana zuwa daga nesa,

tare da fushi mai ƙuna da kuma baƙin hayaƙi;

leɓunansa sun cika da fushi,

harshensa kuma wuta ce mai cinyewa.

28Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu

yana tashi har zuwa wuya.

Yakan tankaɗe al’ummai cikin lariyar hallaka;

yakan sa a muƙamuƙan mutane

linzamin da zai jagorance su su kauce.

29Za ku kuma rera

kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki;

zukatanku za su yi farin ciki

kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa

zuwa dutsen Ubangiji,

zuwa Dutse na Isra’ila.

30Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja

ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa

tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa,

gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara.

31Muryar Ubangiji za tă firgita Assuriya

da sandar mulkinsa zai kashe su.

32Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu

da bulalarsa na hukunci

zai zama kiɗi ga ganguna da garaya,

yayinda yake yaƙi da su da naushin hannunsa.

33An riga an shirya wurin ƙonawa;

an shirya shi saboda sarki.

An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi,

da isashen wuta da itacen wuta;

numfashin Ubangiji,

yana kamar kibiritu mai ƙuna,

da aka sa masa wuta.

¿Sabías que…?

Una alianza inútil con Egipto

  • Isaías condenó a los líderes de Judá por enviar embajadores a ciudades egipcias como Zoán (Tanis) y Hanes sin consultar a Dios. Judá buscaba la protección militar del faraón frente a la amenaza asiria, pero el profeta advirtió que esa alianza solo traería vergüenza y desilusión.Fuentes: el propio texto bíblico · Zoan · Hanes · Pharaoh
  • El capítulo resalta la peligrosa travesía por el Néguev, la región árida al sur de Judá por donde transitaban las caravanas hacia Egipto. Los emisarios cargaron asnos y camellos con tesoros para comprar auxilio militar, cruzando un desierto inhóspito a cambio de una ayuda que resultaría inútil.Fuentes: el propio texto bíblico · Negeb

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 2, 3, 6, 7, 16
  • Zoan · Hoy: Tanis · 30.977, 31.880 · versículo 4
  • Negeb · 31.245, 34.841 · versículo 6
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 19, 29
  • Zion · Hoy: Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 19
  • Assyria · 36.359, 43.153 · versículo 31
  • Topheth · Hoy: in the Hinnom Valley · 31.769, 35.228 · versículo 33

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.