Isaías 19
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Annabci a kan Masar
1Abin da Allah ya faɗa game da Masar,
Duba, Ubangiji yana a kan girgije a sukwane
yana kuwa zuwa Masar.
Gumakan Masar sun firgita a gabansa,
zukatan Masarawa sun karai.
2“Zan tā da hargitsi tsakanin mutumin Masar da mutumin Masar,
ɗan’uwa zai yi gāba da ɗan’uwa
maƙwabci ya yi gāba da maƙwabci,
birni ya yi gāba da birni,
mulki ya yi gāba da mulki.
3Masarawa za su karai,
zan kuma sa shirye-shiryensu su zama banza;
za su nemi shawarar gumaka da kuma ruhohin matattu,
za su nemi shawarar mabiya da na masu duba.
4Zan ba da Masarawa
ga ikon azzalumi shugaba,
mugun sarki kuma zai yi mulki a kansu,”
in ji mai girma, Ubangiji Maɗaukaki.
5Ruwayen kogi za su ƙafe,
bakin kogi zai shanye yă kuma bushe.
6Wuriyoyi za su yi wari;
rafuffukan Masar za su yi ta raguwa har su ƙafe.
Iwa da jema za su bushe,
7haka ma tsire-tsire kusa da Nilu,
a bakin kogi.
Kowane abin da aka shuka a gefen Nilu
zai bushe, iska ta kwashe su ƙaf.
8Masu kamun kifi za su yi nishi su kuma yi makoki,
dukan waɗanda suke jefan ƙugiyoyi a Nilu;
waɗanda suke jefan abin kamun kifi a ruwa
abin kamun kifin za su zama marasa amfani.
9Waɗanda suke aiki da kaɗin auduga za su karai,
masu yin lilin mai kyau za su fid da zuciya.
10Masu aikin tufafi ransu zai ɓace,
kuma dukan masu samun albashi za su damu.
11Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai;
mashawarta masu hikima na Fir’auna suna ba da shawarwari marasa amfani.
Yaya za ka ce wa Fir’auna,
“Ni ɗaya ne cikin masu hikima,
almajirin sarakuna na dā can”?
12Ina masu hikima suke yanzu?
Bari su nuna maka su kuma sanar
da abin da Ubangiji Maɗaukaki
ya shirya a kan Masar.
13Shugabannin Zowan sun zama wawaye,
an ruɗe shugabannin Memfis
dutsen kan kusurwa na mutanenta
su sa Masar ta kauce.
14Ubangiji ya sa zuba musu
ruhun jiri;
suka sa Masar ta yi tangaɗi cikin kome da take yi,
kamar yadda mutumin da ya bugu yake tangaɗi cikin amansa.
15Babu abin da Masar za tă yi,
kai ko wutsiya, reshen dabino ko iwa.
16A wannan rana Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki lokacin da Ubangiji Maɗaukaki ya ɗaga hannu a kansu. 17Ƙasar Yahuda kuma za kawo fargaba ga Masarawa; kowanne da Yahuda ya ambace zai firgita, saboda abin da Ubangiji Maɗaukaki yake shiri a kansu.
18A wannan rana birane biyar a Masar za su yi yaren Kan’ana su kuma miƙa kai cikin yarjejjeniya ga Ubangiji Maɗaukaki. Za a ce da ɗayansu Birnin Hallaka.
19A wannan rana za a kasance da bagade ga Ubangiji a tsakiyar Masar, da kuma ginshiƙin dutse Ubangiji a iyakarta. 20Zai zama alama da kuma shaida ga Ubangiji Maɗaukaki a ƙasar Masar. Sa’ad da suka yi kuka ga Ubangiji saboda masu zaluntarsu, zai aiko musu mai ceto da mai kāriya, zai kuma cece su. 21Saboda haka Ubangiji zai sanar da kansa ga Masarawa, kuma a wannan rana za su yarda da Ubangiji. Za su yi masa sujada da hadayu da hadayun hatsi; za su yi alkawura ga Ubangiji su kuma kiyaye su. 22Ubangiji zai bugi Masar da annoba; zai buge su ya kuma warkar da su. Za su juyo wurin Ubangiji, zai amsa roƙonsu ya kuma warkar da su.
23A wannan rana za a kasance da babban hanya daga Masar zuwa Assuriya. Assuriyawa za su tafi Masar, Masarawa kuma za su tafi Assuriya. Masarawa da Assuriyawa za su yi sujada tare. 24A wannan rana Isra’ila za tă zama na uku, tare da Masar da Assuriya, abin albarka ga duniya. 25Ubangiji Maɗaukaki zai albarkace su, yana cewa, “Albarka ta tabbata ga Masar, mutanena, Assuriya aikin hannuna, da kuma Isra’ila gādona.”

¿Sabías que…?
La profecía sobre Egipto
- Zoán (conocida por los griegos como Tanis), en el delta del Nilo, y Menfis (llamada Nof en hebreo) fueron capitales administrativas y centros de liderazgo en el antiguo Egipto. Isaías señala a los consejeros de estas ciudades reales para resaltar el fracaso de la sabiduría egipcia.Fuentes: Zoan · Memphis · el propio texto bíblico
- El juicio económico descrito en el capítulo apunta directamente al Nilo, el río esencial para la supervivencia de Egipto. La sequía de sus aguas y canales amenazaba la agricultura, la pesca y oficios fundamentales como el cultivo de lino y el tejido fino.Fuentes: Nile · el propio texto bíblico
- El oráculo concluye vislumbrando una calzada que uniría a los grandes rivales imperiales, Egipto y Asiria, junto a Israel. En lugar de una guerra perpetua, estos antiguos imperios aparecen rindiendo culto juntos y compartiendo la bendición divina.Fuentes: Assyria · Egypt · el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 1, 2, 3, 4, 6, 10, 11, 12, 13, 14, 15, 16, 17, 18, 19, 20, 21, 22, 23, 24, 25
- Nile · Hoy: Nile River · 31.465, 30.367 · versículos 5, 6, 7, 8
- Zoan · Hoy: Tanis · 30.977, 31.880 · versículos 11, 13
- Memphis · 29.849, 31.253 · versículo 13
- Canaan · 32.767, 35.333 · versículo 18
- Assyria · 36.359, 43.153 · versículos 23, 24, 25
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org