Esdras 6
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Umarnin Dariyus
1Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincika a duba cikin littattafan tarihin da suke a ajiye a wurin ajiyarsu a Babilon. 2Sai aka sami takarda a Ekbatana a yankin Mediya, ga kuma abin da yake rubuce a ciki.
Abin tunawa.
3A shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus, sarki ya ba da umarni game da haikalin Allah a Urushalima, ya ce,
Bari a sāke gina haikalin yă zama wurin miƙa hadayu, a kuma aza harsashin ginin haikalin. Tsayinsa zai zama ƙafa tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tasa’in. 4Za a jera manyan duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katako. Daga asusun sarki kuma za a biya kuɗin aikin. 5Kwanonin zinariya da na azurfan gidan Allah waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga haikali a Urushalima ya kawo Babilon, a mayar da su wurinsu a haikali a Urushalima; a sa su cikin gidan Allah.
6Saboda haka Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai, da ku masu muƙami na yankin, ku bar wurin. 7Kada ku hana wannan aiki na haikalin Allah. Bari gwamnan Yahudawa, da dattawan Yahudawa su sāke gina wannan gidan Allah a wurin da yake a dā.
8Na kuma ba da umarni game da abin da za ku yi wa dattawan Yahudawa cikin aikin ginin wannan gidan Allah.
Daga asusun sarki a kuɗin da yake shigo wa Kewayen Kogin Yuferites za a biya mutanen nan duka, domin kada aikin yă tsaya. 9A tanada musu duk abin da suke bukata. A ba su ’yan bijimai, da raguna, da ’yan tumaki domin miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na sama, haka kuma dole a tanada wa firistoci alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da mai, kullum ba fasawa yadda firistoci suke yi a Urushalima 10domin su miƙa hadayu masu daɗi ga Allah na Sama, su kuma yi addu’a domin lafiyar sarki da ’ya’yansa.
11Na kuma yi umarni cewa duk wanda ya karya wannan doka sai a fitar da itace daga cikin gidansa, a fiƙe kan itacen, a tsire mutumin, sa’an nan a mai da gidansa juji. 12Bari Allah yă sa sunansa yă kasance, yă hamɓarar da duka wani sarki ko mutanen da za su sa hannu don a sāke wannan doka, ko kuma don su rushe haikalin nan a Urushalima.
Ni Dariyus na ba da wannan umarni, bari a yi biyayya babu wasa.
Gamawa da kuma keɓewar haikali
13Saboda umarnin da sarki Dariyus ya aika, sai Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites da Shetar-Bozenai da abokansu suka yi biyayya da umarnin babu wasa. 14Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa. 15An gama ginin haikalin a rana ta uku na watan Adar a shekara ta shida ta mulkin Sarki Dariyus.
16Sai mutanen Isra’ila, firistoci, Lawiyawa da kuma sauran waɗanda suka dawo daga bauta suka yi bikin keɓe gidan Allah, cike da farin ciki. 17Suka miƙa bijimai guda ɗari, da raguna ɗari biyu, da ’yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra’ila, suka kuma miƙa bunsurai guda goma sha biyu don hadaya ta zunubi, kowane bunsuru ɗaya don kowace kabila ta Isra’ila. 18Suka kuma naɗa firistoci a gundumominsu da kuma Lawiyawa a ƙungiyoyinsu don hidimar Allah a Urushalima, bisa ga abin da aka rubuta a Littafin Musa.
Bikin Ƙetarewa
19A rana ta goma sha huɗu ga watan farko, sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi Bikin Ƙetarewa. 20Firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka zama da tsabta. Lawiyawa suka yanka ragon Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda suka dawo daga bauta, da kuma domin ’yan’uwansu firistoci, da kuma domin kansu. 21Sai Isra’ilawa waɗanda suka dawo daga bauta suka ci tare da duk waɗanda suka keɓe kansu daga halin ƙazanta na Al’ummai maƙwabtansu, don su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila. 22Suka yi kwana bakwai suna Bikin Burodi Marar Yisti, suna cike da farin ciki, gama Ubangiji ya cika su da farin ciki don ya sa sarkin Assuriya ya canja tunaninsa, ya taimake su cikin aikin gidan Allah, Allah na Isra’ila.

¿Sabías que…?
Terminación y dedicación del Templo
- Aunque el rey Darío ordenó una búsqueda en los archivos de Babilonia, el decreto original de Ciro que autorizaba la reconstrucción del templo fue hallado en la fortaleza de Ecbatana, en la provincia de Media, donde Ciro mantenía una residencia real.Fuentes: el propio texto bíblico · Ecbatana
- Tatnai, el gobernador persa de la región al oeste del Éufrates que había investigado la obra, recibió órdenes de Darío de costear por completo la construcción y proveer animales para los sacrificios diarios con los impuestos recaudados en su provincia.Fuentes: el propio texto bíblico · Tatnai
- El templo se terminó en el sexto año de Darío mediante el ministerio profético de Hageo y Zacarías, y su dedicación se celebró con gozosos sacrificios, incluidos doce machos cabríos que representaban a todas las tribus de Israel.Fuentes: el propio texto bíblico · Haggai · Zechariah
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Babylonia · 32.543, 44.422 · versículo 1
- Ecbatana · Hoy: Tell Hagmatana · 34.806, 48.516 · versículo 2
- Media · 34.806, 48.516 · versículo 2
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 3, 5, 9, 12, 18
- Babylon · 32.543, 44.422 · versículo 5
- Beyond the River · 31.777, 35.234 · versículos 6, 8, 13
- Euphrates · Hoy: Euphrates River · 31.004, 47.442 · versículo 6
- Persia · 34.806, 48.516 · versículo 14
- Assyria · 36.359, 43.153 · versículo 22
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org