Nations Bible

Ezequiel 40

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

Wurin sabon haikali

1A shekara ta ashirin da biyar ta zaman bauta, a farkon shekara, a rana ta goma ga wata, a shekara ta goma sha huɗu bayan fāɗuwar birnin Urushalima, a wannan rana ikon Ubangiji ya sauko a kaina ya kuma iza ni. 2Cikin wahayin, Allah ya kai ni ƙasar Isra’ila ya sa ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda a gefen kudunsa akwai gine-ginen da suka yi kamar birni. 3A cikin wahayin ya kai ni can, na kuma ga mutum wanda kamanninsa ya yi kamar tagulla; yana tsaye a hanyar shiga yana riƙe da igiyar lilin da kuma karan awo a hannunsa. 4Mutumin ya ce mini, “Ɗan mutum, duba da idanunka, ka ji da kunnuwanka ka kuma lura da kowane abin da zan nuna maka, gama abin da ya sa na kawo ka nan ke nan. Ka faɗa wa gidan Isra’ila duk abin da ka gani.”

Ƙofar shiga ta gabas zuwa filin waje

5Na ga katanga da ya kewaye filin haikali gaba ɗaya. Tsawon karan awon da yake a hannun mutumin kamu shida ne, sai ya auna kaurin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.

6Sa’an nan ya tafi ƙofar da take fuskantar gabas. Ya hau matakanta ya auna madogarar ƙofa; zurfinta kamu shida ne. 7Tsawon kowane ɗakin matsara kamu shida ne, fāɗinsa kuma kamu shida, kaurin bangayen da suka raba ɗaki da ɗaki kamu biyar ne. Zurfin madogarar ƙofar da yake dab da shirayin da yake fuskantar haikalin kamu shida ne.

8Sa’an nan ya auna shirayin hanyar shiga; 9zurfinsa kamu takwas ne, kaurin kowane madogarar ƙofarsa kuwa kamu biyu ne. Shirayi hanyar shiga yana fuskantar haikalin.

10A cikin ƙofar gabas akwai ɗakuna uku a kowane gefe na hanyar shiga; dukan ukun girmansu ɗaya, bangayen da suke tsakani a kowane gefe girmansu ɗaya ne. 11Sa’an nan ya auna bakin hanyar shiga ya sami fāɗinsa kamu goma, tsawonsa kuma kamu goma sha uku. 12A gaban kowane ɗakin akwai bango mai tsayi kamu ɗaya, ɗakunan kuma kamu shida-shida ne a kowane gefe. 13Sa’an nan ya auna hanyar shiga daga saman bangon ɗaki a baya zuwa saman ɗakin da yake ɗaura da shi; nisansu kamu ashirin da biyar ne daga bango zuwa bango. 14Ya auna ɗakin bakin ƙofa na can ƙarshen hanyar shiga ya sami kamu sittin. Awon ya kai har zuwa shirayin da yake fuskantar filin. 15Nisan da take daga mashigin hanyar shiga zuwa can ƙarshen shirayin, kamu hamsin ne. 16Akwai ƙananan tagogi a ɗakunan da kuma a bangayen hanyar shiga, yadda suke a shirayin; tagogi a kewaye duka suna fuskantar ciki. An yi wa bangayen da suke waje ƙofar shiga ado da zāne-zāne siffofin itatuwan dabino.

Filin waje

17Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar shiga zuwa filin waje, inda na ga ɗakuna talatin da aka gina kewaye a filin waje na filin. An gina waɗannan ɗakunan gefe a jikin bangon waje, a gabansu kuwa akwai daɓe kewaye da filin. 18Daɓen ya bi ta daidai gefen hanyoyin shiga, kuma faɗinsa ya yi daidai da tsawon ƙofofin shiga; wannan shi ne daɓen da yake ƙasa-ƙasa.

19Sa’an nan ya auna nisan da take daga hanyar shiga da take ƙasa-ƙasa daga ciki zuwa waje na filin ciki; ya kai kamu ɗari a gefen gabas haka ma yake a gefen arewa.

Ƙofar arewa

20Sa’an nan mutumin ya auna tsawo da fāɗin ƙofar da take fuskantar arewa, wadda take bi zuwa filin waje. 21Ƙofar shigar ma tana da ɗakuna uku-uku a kowane gefe. Girman bangayen da suka miƙe, da kuma shirayinta daidai suke da na ƙofa ta fari. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuwa kamu ashirin da biyar. 22Tagoginta, shirayinta da siffofin itatuwan dabinon da aka yi zāne-zānen adonta duk girmansu ɗaya ne da na ƙofar da take fuskantar gabas. Ɗakin shiga shi ma ya fuskanci filin yana kuma da matakai bakwai waɗanda suka bi zuwa ƙofar shiga, da shirayinta ɗaura da su. 23Akwai ƙofa zuwa filin ciki wadda take fuskantar ƙofar arewa, kamar dai yadda take a gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofar da take ɗaura ta ita; ya sami kamu ɗari.

Ƙofar kudu

24Sa’an nan ya kai ni gefen kudu, na kuma ga ƙofa tana fuskantar kudu. Ya auna madogaranta da shirayinta, dukansu girmansu ɗaya ne kamar sauran ƙofofi biyun. 25Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye, kamar tagogin sauran. Tsawonta kamu hamsin ne fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne. 26Matakai bakwai sun haura zuwa ƙofar, da shirayi ɗaura da matakan; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a bangayen a kowane gefe. 27Filin cikin ma yana da ƙofar da ta fuskanci kudu, sai ya auna daga wannan ƙofa zuwa ƙofar waje a gefen kudu; ya sami kamu ɗari.

Ƙofofin zuwa filin ciki

28Sai ya kawo ni cikin filin ciki ta ƙofar kudu, ya kuma auna ƙofar kudu; ita ma tana da girma ɗaya da sauran ƙofofin shiga. 29Ɗakunanta na matsara, bangayenta duk suna da girma ɗaya da sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne. 30(Fāɗin shirayun hanyoyin shiga kewaye da filin ciki kamu ashirin da biyar ne, fāɗinsu kuma kamu biyar.) 31Shirayin ƙofar yana fuskantar filin waje; an yi zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogarar bangayen hanyar shiga. Yana kuma da matakai takwas.

32Sai ya kai ni filin da yake ciki a gefen gabas, ya kuma auna hanyar shiga; girmanta iri ɗaya ne kamar sauran. 33Ɗakunanta, bangayenta da shirayinta duk girmansu iri ɗaya ne kamar sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawon hanyar shiga kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar. 34Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogararta. Tana kuma da matakai takwas.

35Sa’an nan ya kawo ni ƙofar arewa ya kuma auna ta. Girmanta ɗaya ne da sauran, 36Haka ma ɗakunanta, bangayenta da shirayinta, ƙofar tana da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar. 37Shirayin ƙofar ta fuskanci filin waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogaranta, matakai takwas kuwa sun haura zuwa wajenta.

Ɗakuna don shirya hadayu

38Ɗakin da hanya ta ratsa ciki yana kusa da shirayin a kowane hanyoyin shiga na ciki, inda a kan wanke hadayun ƙonawa. 39A shirayin hanyar shiga akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yankan hadayun ƙonawa, hadayun zunubi da kuma hadayun laifi. 40Ta bangon waje na shirayin hanyar shiga, kusa da matakai a mashigin zuwa hanyar shiga da take arewa akwai tebur biyu, akwai kuma tebur biyu a gefe ɗaya na matakan. 41Duka dai akwai tebur huɗu a gefe ɗaya na hanyar shiga, huɗu kuma a ɗaya gefen, tebur takwas ke nan gaba ɗaya, inda a kan yanka hadayu a kai. 42Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu don hadayun ƙonawa, tsawon kowanne kuwa kamu ɗaya da rabi ne, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya. A kansu ne a kan ajiye kayan yanka hadayun ƙonawa da kuma sauran hadayu. 43Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye a bangon, tsawon kowanne ya yi fāɗin tafin hannu. An yi amfani da teburin don a riƙa ajiye naman hadayu.

Ɗakuna domin firistoci

44Waje da ƙofar ciki, a cikin filin ciki, akwai ɗakuna biyu, ɗaya a gefen ƙofar arewa yana kuma fuskantar kudu, wani kuma a gefen ƙofar kudu yana fuskantar arewa. 45Sai mutumin ya ce mini, “Ɗakin da yake fuskantar kudu ne na firistocin da suke lura da haikali, 46ɗaya ɗakin kuma da yake fuskantar arewa ne na firistocin da suke lura da bagade. Waɗannan su ne ’ya’yan Zadok maza, waɗanda su ne kaɗai Lawiyawan da za su iya yin kusa da Ubangiji don su yi hidima a gabansa.”

47Sa’an nan ya auna filin, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu ɗari. Bagaden kuwa yana a gaba a cikin haikalin.

Haikalin

48Sai ya kawo ni shirayin haikalin ya kuma auna madogaran shirayin; fāɗinsu a kowane gefe kamu biyar-biyar ne. Fāɗin mashigin kamu goma sha huɗu ne, bangayenta kuma kamu uku-uku ne a kowane gefe. 49Fāɗin shirayin kamu ashirin ne, kamu goma sha biyu kuma daga gaba zuwa baya. A kan kai samansa ta wurin hawan matakai, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe na madogaran.

Ilustración artística: una interpretación, no un registro histórico.

¿Sabías que…?

La visión del templo restaurado

  • Ezequiel recibió esta visión en el vigésimo quinto año del exilio babilónico, catorce años después de la caída de Jerusalén. Llevado en visión divina a un monte muy alto en la tierra de Israel, se le encomendó observar y registrar con precisión las medidas de un templo restaurado.Fuentes: el propio texto bíblico
  • La caña de medir que sostenía el guía con apariencia de bronce medía seis codos largos, donde cada codo largo equivalía a un codo común más un palmo menor. Esta unidad fijó las proporciones de cada muro, pórtico y cámara del santuario.Fuentes: el propio texto bíblico
  • La visión asigna el servicio del altar exclusivamente a los hijos de Sadoc entre los levitas. Sadoc ejerció como sumo sacerdote en tiempos de David y Salomón, habiendo permanecido fiel a la dinastía real cuando otros se rebelaron.Fuentes: el propio texto bíblico · Zadok

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 1

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.