Deuteronomio 7
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Korin al’ummai
1Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku ƙasar da kuke shiga don ku mallaka, ya kuma kori al’ummai masu yawa a gabanku; wato, Hittiyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, al’ummai bakwai masu girma da ƙarfi fiye da ku. 2Sa’ad da kuma Ubangiji Allahnku ya ba da su gare ku, kuka kuma ci su da yaƙi, sai ku hallaka su ƙaƙaf. Kada ku yi yarjejjeniya da su, kada kuma ku nuna musu jinƙai. 3Kada ku yi auratayya da su. Kada ku ba da ’ya’yanku mata wa ’ya’yansu maza, ko ku ɗauko ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza. 4Gama za su juye ’ya’yanku maza daga bina, su bauta waɗansu alloli, fushin Ubangiji kuma zai ƙuna a kanku da sauri, zai kuma hallaka ku. 5Ga abin da za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza keɓaɓɓun duwatsunsu, ku farfashe ginshiƙan Asheransu, ku kuma ƙona gumakansu da wuta. 6Gama ku mutane masu tsarki ne ga Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga dukan mutane a fuskar duniya, don ku zama mutanensa, kayan gādonsa.
7Ba don kun fi sauran al’ummai yawa ne ya sa Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma zaɓe ku ba, gama ku ne mafi ƙanƙanta cikin dukan al’ummai. 8Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar. 9Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa. 10Amma
waɗanda suke ƙinsa, a fili yakan sāka musu da hallaka;
ba zai yi jinkiri yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili.
11Saboda haka, sai ku lura, ku bi umarnai, ƙa’idodi, da dokokin nan da nake ba ku a yau.
12In kuka mai da hankali ga waɗannan dokoki, kuka kuma yi hankali ga bin su, to, Ubangiji Allahnku zai kiyaye alkawarinsa na ƙauna gare ku, kamar yadda ya rantse wa kakanninku. 13Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku. 14Za a albarkace ku fiye da waɗansu mutane; babu wani cikin maza ko matanku da zai kasance babu haihuwa, ba kuwa wata dabbarku da za tă kasance babu haihuwa. 15Ubangiji zai kiyaye ku daga kowace cuta. Ba zai wahalshe ku da mugayen cututtukan da kuka sani a Masar ba, amma zai aukar wa dukan maƙiyanku. 16Dole ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su gare ku. Kada ku ji tausayinsu, kada kuma ku bauta wa allolinsu, gama wannan zai zama tarko gare ku.
17Wataƙila ku ce wa kanku, “Waɗannan al’ummai sun fi mu ƙarfi. Yaya za mu kore su?” 18Amma kada ku ji tsoronsu; ku tuna da kyau abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Fir’auna da kuma dukan Masar. 19Kun ga da idanunku, manyan gwaje-gwaje, alamu masu banmamaki da al’ajabai, hannu mai ƙarfi da kuma mai ikon da Ubangiji Allahnku ya fitar da ku. Ubangiji Allahnku zai yi haka ga dukan mutanen da yanzu kuke tsoro. 20Ban da haka ma, Ubangiji Allahnku zai aika da rina a cikinsu, har sai sun hallaka sauran mutanen da suka ragu, waɗanda suka ɓuya daga gare ku. 21Kada ku tsorata saboda su, gama Ubangiji Allahnku, wanda yake a cikinku, Allah ne mai girma da kuma mai banrazana. 22Da kaɗan da kaɗan Ubangiji Allahnku zai kore waɗannan al’ummai a gabanku. Ba a bari ku hallaka su duka gaba ɗaya ba, in ba haka namun jeji za su yaɗu kewaye da ku. 23Amma Ubangiji Allahnku zai ba da su gare ku, yana jefa su cikin rikicewa mai girma, har sai an hallaka su. 24Zai ba da sarakunsu a hannunku, za ku kuwa shafe sunayensu daga duniya. Babu wani da zai yi tsayayya da ku, za ku hallaka su. 25Ku ƙone siffar allolinsu da wuta. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da aka rufe allolin da ita, Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku. 26Kada ku kawo abin ƙyama cikin gidajenku, domin kada ku zama kamar su. Gaba ɗaya ku yi ƙyamarsu, ku ƙi su, gama an ware su, sun zama domin a hallaka.

¿Sabías que…?
Un Pueblo Elegido y la Conquista de Canaán
- Deuteronomio menciona siete naciones en Canaán más grandes y fuertes que Israel: hititas, gergeseos, amorreos, cananeos, ferezeos, heveos y jebuseos. Se ordenó a Israel no pactar ni emparentar con ellos para no caer en la idolatría.Fuentes: el propio texto bíblico
- La elección de Israel no dependió de su número o poder, pues eran el más pequeño de todos los pueblos. Su liberación del faraón, rey de Egipto, se basó en el amor de Dios y en el juramento hecho a sus antepasados.Fuentes: el propio texto bíblico · Pharaoh (of the Exodus) · Egypt
- La conquista debía llevarse a cabo poco a poco y no de golpe. Una rápida despoblación de la tierra habría provocado que las fieras del campo se multiplicaran en contra de los israelitas.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org