Deuteronomio 19
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Biranen Mafaka
1Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya hallakar da al’ummai waɗanda yake ba ku ƙasarsu, sa’ad da kuka kore su, kuka kuma zauna a birane da gidajensu, 2sai ku keɓe wa kanku birane uku waɗanda suke a tsakiyar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka. 3Ku gina hanyoyi zuwa cikinsu, ku kuma raba ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo kashi uku, saboda duk wani da ya yi kisankai yă iya gudu zuwa can.
4Ga doka game da mutumin da ya kashe wani, ya kuma gudu don yă cece ransa, wani wanda ya kashe maƙwabcinsa ba da gangan ba, ba kuwa da wata ƙiyayya a tsakaninsu a dā ba. 5Misali, in mutum ya je jeji da maƙwabcinsa domin yankan itace, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe daga ƙotar yayinda yake saran itacen, ya sari maƙwabcin har ya mutu. Mutumin nan zai iya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane don yă ceci ransa. 6In ba haka ba mai neman ɗaukan fansa jini, zai iya binsa cikin fushi, yă cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da yake ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā. 7Wannan ne ya sa na umarce ku ku keɓe wa kanku birane uku.
8In Ubangiji Allahnku ya fadada yankinku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa wa kakanninku, ya kuma ba ku ƙasar gaba ɗaya kamar yadda ya yi musu alkawari, 9idan dai kun lura, kuka kiyaye umarnin da nake ba ku a yau, wato, ta wurin ƙaunar Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya kullum cikin hanyoyinsa, to, sai ku keɓe ƙarin birane uku. 10Ku yi haka don kada a zub da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, don kada ku kuma zama masu laifin zub da jini.
11Amma idan wani mutum yana ƙin maƙwabcinsa, ya kuma yi kwanto yana fakonsa, ya yi masa rauni, har ya kashe shi, sa’an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane, 12dattawan garinsa za su aika a kawo shi, a dawo da shi daga birnin, a miƙa shi ga mai neman fansar jini don yă kashe shi. 13Kada ku ji tausayinsa. Dole ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga Isra’ila, don ku sami zaman lafiya.
14Kada ka gusar da dutsen nuna shaidar iyakar maƙwabcinka wanda kakanni suka sa, a gādon da ka samu a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka mallaka.
Shaidu
15Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku.
16In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi, 17dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin. 18Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne, 19to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku. 20Sauran mutane za su ji wannan su kuma ji tsoro, ba kuwa za a ƙara yin irin wannan mugun abu a cikinku ba. 21Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa.

¿Sabías que…?
Ciudades de refugio, linderos y justicia imparcial
- La ley ordenaba a Israel apartar tres ciudades de refugio y construir caminos de acceso a través de tres regiones de la tierra. Estas ciudades permitían que alguien que matara a su prójimo por accidente, como cuando la hoja de un hacha se desprende del mango, huyera a salvo del vengador de la sangre.Fuentes: el propio texto bíblico
- Estaba estrictamente prohibido mover los linderos antiguos colocados por los antepasados. Estas marcas delimitaban las tierras heredadas por cada familia, y moverlas equivalía a apoderarse injustamente de la propiedad del prójimo.Fuentes: el propio texto bíblico
- Para evitar acusaciones falsas, un solo testigo no bastaba para condenar a nadie por un delito; se requería el testimonio de dos o tres testigos. Si los sacerdotes y jueces comprobaban que un testigo había mentido con malicia, se le imponía exactamente el mismo castigo que él pretendía para el acusado.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org