Deuteronomio 15
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Shekara ta yafe bashi
1A ƙarshen kowace shekara ta bakwai, dole ku yafe basusuwan da kuke bi. 2Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi. 3Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa. 4Amma bai kamata a sami matalauci a cikinku ba, gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku, ku mallaka a matsayin gādo, 5in dai kun yi cikakken biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuna kiyaye dukan waɗannan umarnan da nake ba ku yau. 6Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku kamar yadda ya yi alkawari, za ku kuma ba al’ummai masu yawa bashi, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. Za ku yi mulkin al’ummai masu yawa, babu wata kuwa da za tă yi mulkinku.
7In akwai matalauci a cikin ’yan’uwanku, a duk wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku taurara zuciya, ko ku ƙi saki hannu ga ɗan’uwanku matalauci. 8A maimakon haka ku bayar hannu sake, ku kuma ba shi bashi gwargwadon abin da yake bukata a sauƙaƙe. 9Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku. 10Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai. 11Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga ’yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku.
Ba da ’yanci ga bayi
12In ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa, namiji ko ta mace, ya sayar da kansa gare ka, ya kuma bauta maka shekaru shida, a shekara ta bakwai dole ka ’yantar da shi. 13Sa’ad da kuka sake shi, kada ku bar shi yă tafi hannu wofi. 14Ku ba shi kyautai hannu sake daga tumakinku, daga masussukarku, da kuma daga wurin matsewar inabinku. Ku ba shi yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace ku. 15Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuma ya fisshe ku. Shi ya sa nake ba ku wannan umarni a yau.
16Amma in bawanka ya ce maka, “Ba na so in bar ka,” saboda yana ƙaunarka da iyalinka, ya kuma fiye masa yă zauna da kai, 17sai ka ɗauki basilla ka huda kunnensa a bakin ƙofa, zai kuwa zama bawanka dukan rayuwarsa. Ka yi haka ma wa baiwarka.
18Sa’ad da kuka ’yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a kome da kuke yi.
’Ya’yan fari na dabbobi
19Ku keɓe wa Ubangiji Allahnku kowane ɗan fari na garkenku na shanu, da na tumaki. Kada ku sa ɗan fari na shanunku aiki, kada kuma ku aske gashin ɗan fari na tumakinku. 20Kowace shekara, kai da iyalinka za ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa. 21In dabbar tana da lahani, gurguntaka ko makantaka, ko kuwa tana da wani mugun lahani, kada ku miƙa ta ga Ubangiji Allahnku. 22Sai ku ci a cikin biranenku. Mutum marar tsabta da mai tsabta zai iya ci kamar yadda ake yi da barewa ko mariri. 23Amma kada fa ku ci jinin, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
¿Sabías que…?
Deudas, Siervos y Ofrendas de Primogénitos
- Cada siete años, los israelitas debían condonar las deudas contraídas por sus compatriotas. Se advertía expresamente a los acreedores que no negaran préstamos por el solo hecho de que se acercaba el séptimo año de remisión.Fuentes: el propio texto bíblico
- Los siervos hebreos que habían servido seis años debían quedar libres en el séptimo año y recibir provisiones generosas de ganado, grano y vino. Si un siervo decidía quedarse por afecto a la casa, el amo perforaba su oreja contra la puerta con una lezna como señal de servicio permanente.Fuentes: el propio texto bíblico
- Los machos primogénitos del ganado vacuno y lanar eran consagrados a Dios y no podían ser puestos a trabajar ni trasquilados. Los animales sin defecto se comían anualmente en el lugar de culto designado, mientras que los animales defectuosos podían comerse en casa por cualquier persona.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículo 15
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org