Nations Bible

2 Samuel 10

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

Dawuda ya ci Ammonawa da yaƙi

1Ana nan sai sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa Hanun kuwa ya gāje shi a matsayin sarki. 2Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan yi wa Hanun ɗan Nahash alheri kamar yadda mahaifinsa ya yi mini.” Saboda haka sai Dawuda ya aiki jakadu su yi masa ta’aziyyar mutuwar mahaifinsa.

Sa’ad da mutanen Dawuda suka isa ƙasar Ammonawa, 3sai manyan mutanen Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aiko da jakadu su kawo maka ta’aziyya? Ai, wayo ya yi don yă ga asirin birninmu, yă san ƙarfinmu, yă kuma ci mu da yaƙi.” 4Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda ya aske rabin gemun kowannensu, ya yayyage rigunarsu daidai ɗuwawu, sa’an nan ya sallame su.

5Sa’ad da aka gaya wa Dawuda game da wannan, sai ya aiki manzanni su taryi waɗannan mutanen da aka ci mutuncinsu, gama an wulaƙanta su ƙwarai. Sai sarki ya ce musu, “Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya sāke girma, sa’an nan ku dawo.”

6Da Ammonawa suka gane cewa Dawuda ya ji fushi da su sosai saboda abin da suka yi, sai suka yi hayar sojojin ƙasar Arameyawa dubu ashirin daga Bet Rehob da Aram-Zoba, suka kuma yi hayar sarkin Ma’aka tare da mutum dubu ɗaya, suka kuma yi hayar maza dubu goma sha biyu daga Tob.

7Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi. 8Ammonawa suka fita suka ja dāgār yaƙi a ƙofar shiga birninsu, yayinda Aram-Zoba, da na Rehob, da mutane Tob, da kuma na Ma’aka, suka ja tasu dāgār a karkara.

9Yowab ya ga cewa an ja masa dāgār yaƙi gaba da baya; saboda haka sai ya zaɓi waɗansu shahararrun sojoji cikin Isra’ila, ya sa su gabza da Arameyawa. 10Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin Abishai ɗan’uwansa, ya sa su gabza da Ammonawa. 11Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ƙarfina, sai ku kawo mini gudummawa; amma in Ammonawa suka fi ƙarfinku, sai mu kawo muku gudummawa. 12Ku yi ƙarfin hali, mu kuma yi yaƙi da ƙarfin zuciya saboda mutanenmu da kuma birane Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da yake da kyau a idanunsa.”

13Sa’an nan Yowab da rundunar da take tare da shi suka ci gaba don su gabza da Arameyawa, Arameyawa kuwa suka gudu a gabansa. 14Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka ruga da gudu a gaban Abishai, suka shiga cikin birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙin da ya yi da Ammonawa.

15Bayan Arameyawa suka ga Isra’ila ta ci su da yaƙi, sai suka sāke tattara kansu. 16Hadadezer sarkin Zoba ya aika a kawo Arameyawan da suke ƙetaren Kogin Yuferites. Suka iso Helam a ƙarƙashin shugabancin Shobak, shugaban dukan sojojin Hadadezer.

17Da aka gaya wa Dawuda wannan, sai ya tattara dukan Isra’ila, ya ƙetare Urdun, ya je Helam. Arameyawa suka ja dāgār yaƙinsu, suka kara da Dawuda. 18Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, Dawuda kuwa ya kashe mahayan keken yaƙinsu ɗari bakwai, da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya bugi Shobak, shugaban ƙungiyar sojansu ya kuwa mutu a can. 19Sa’ad da dukan sarakuna waɗanda suke abokan tarayya na Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa, suka kuma zama bayinsu.

Wannan ya sa Arameyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudummawa.

Ilustración artística: una interpretación, no un registro histórico.

¿Sabías que…?

La guerra contra los amonitas y arameos

  • Cuando el rey Janún de Amón sospechó que los emisarios de David eran espías, los humilló rapándoles la mitad de la barba y cortándoles la ropa a la altura de las caderas. Debido a su gran vergüenza, David les ordenó quedarse en Jericó hasta que les creciera la barba de nuevo.Fuentes: el propio texto bíblico · Hanun · Jericho
  • Al darse cuenta de que se habían hecho odiosos para David, los amonitas contrataron a miles de soldados mercenarios arameos de reinos vecinos como Bet-rejob, Soba y Maaca para luchar contra Israel.Fuentes: el propio texto bíblico · Zobah · Maacah
  • Al verse atrapado entre dos frentes—los amonitas junto a las puertas de la ciudad y los arameos en campo abierto—, Joab dividió las fuerzas de Israel, liderando él mismo las tropas escogidas contra los arameos y dejando el resto a su hermano Abisay.Fuentes: el propio texto bíblico · Joab · Abishai

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Ammon · 31.955, 35.934 · versículos 1, 2, 3, 6, 8, 10, 11, 14, 19
  • Jericho · Hoy: Tell es Sultan · 31.872, 35.445 · versículo 5
  • Maacah · 33.258, 35.581 · versículos 6, 8
  • Zobah · 33.935, 36.151 · versículos 6, 8
  • Syria · Hoy: Aram · 33.511, 36.306 · versículos 9, 11, 13, 14, 17, 18, 19
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 14
  • Euphrates · Hoy: Euphrates River · 31.004, 47.442 · versículo 16
  • Jordan · Hoy: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículo 17

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.