1 Reyes 1
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

Acerca de este libro
Sobre 1 Reyes
- El Easton's Bible Dictionary (1897) considera incierta la autoría de los libros de Reyes. Una tradición según la cual Jeremías los escribió queda, a juicio de Easton, respaldada por pasajes casi idénticos a partes de Jeremías y por sucesos que Jeremías conocía personalmente; sin embargo, Easton estima más probable que Esdras, después del cautiverio, compilara los libros a partir de documentos anteriores, quizá escritos por David, Salomón, Natán, Gad e Iddo. Easton sitúa la composición entre el 561 a. C., cuando Evil-merodac liberó a Joaquín del cautiverio, y el 538 a. C., el decreto de Ciro.Fuentes: Easton: Kings, The Books of
- Easton afirma que estos libros contienen los anales del reino desde la subida de Salomón al trono hasta que Nabucodonosor y los babilonios lo sometieron, un período que estima en unos 453 años. 1 Reyes comienza mientras David está muriendo: Adonías, su cuarto hijo, que había pasado a ser el heredero presunto del trono tras la muerte de Amnón y Absalón, se hace proclamar rey, pero Natán y Betsabé persuaden a David de que entronice a Salomón de inmediato. Salomón, hijo de David y Betsabé, cuya historia se registra en 1 Reyes 1-11, llegó al trono, sugiere Easton, hacia los dieciséis o dieciocho años.Fuentes: Easton: Kings, The Books of · Adonijah · Solomon
- En las Escrituras hebreas, los dos libros de Reyes formaban originalmente un solo libro; la Septuaginta fue la primera en dividirlos y, con la Vulgata, los numera como el tercer y el cuarto libros de Reyes, siendo los libros de Samuel el primero y el segundo. Easton observa que Crónicas da mayor relieve al oficio sacerdotal o levítico, mientras que Reyes da mayor relieve al oficio real, y que en la división de las Escrituras en tres partes hecha por los judíos estos libros se cuentan entre los Profetas. La narración remite a fuentes anteriores: el libro de los hechos de Salomón y las crónicas de los reyes de Judá y de Israel.Fuentes: Easton: Kings, The Books of
- Tras la muerte de Salomón, las diez tribus se rebelaron e invitaron a Jeroboam, hijo de Nebat, a ser su rey; Easton lo llama el primer rey de esas tribus y sitúa su reinado entre 976 y 945 a. C. Había huido a Egipto bajo la protección de Sisac I y luego trasladó su residencia de Siquem, su primera capital, a Tirsa, que siguió siendo la residencia principal de los reyes de Israel hasta que Omri compró a Semer el monte de Shomeron por dos talentos de plata y edificó Samaria. La narración posterior incluye a Acab, hijo de Omri y séptimo rey de Israel, cuya esposa era Jezabel: al culto del becerro introducido por Jeroboam añadió el culto de Baal, y fue severamente amonestado por el profeta Elías.Fuentes: Jeroboam · Tirzah · Samaria · Ahab
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Adoniya ya naɗa kansa Sarki
1Sa’ad da Sarki Dawuda ya tsufa ya kuma ƙara shekaru, ba ya iya jin ɗumi ko an rufe shi da abin rufuwa. 2Saboda haka bayinsa suka ce masa, “Bari mu nemi wata budurwa wadda za tă yi wa ranka yă daɗe, sarki hidima, tă kuma kula da shi. Za tă dinga kwanta kusa da ranka yă daɗe, yă ji ɗumi.”
3Suka nemi kyakkyawar yarinya cikin fāɗin Isra’ila, sai suka sami Abishag, mutuniyar Shunam, suka kawo ta wa sarki. 4Yarinyar kuwa kyakkyawa ce ƙwarai; ta kuwa lura da sarki, ta kuma yi masa hidima, amma sarki bai yi jima’i da ita ba.
5Adoniya, wanda mahaifiyarsa ce Haggit, ya fito ya ce, “Zan zama sarki.” Saboda haka ya nemi kekunan yaƙi, ya kuma shirya dawakai, tare da mutane hamsin da za su sha gabansa. 6(A duk rayuwarsa mahaifinsa bai taɓa tsawata masa yă ce, “Me ya sa kake yin haka ba?” Shi kuwa mai kyan gani ne ƙwarai, shi ne aka haifa bayan Absalom.)
7Adoniya ya haɗa baƙi da Yowab ɗan Zeruhiya da kuma Abiyatar firist, suka kuma ba shi goyon baya. 8Amma Zadok firist, Benahiya ɗan Yehohiyada, annabi Natan, Shimeyi, Reyi da kuma matsara na musamman na Dawuda ba su bi Adoniya ba.
9Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda, 10amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benahiya, ko wani daga matsara na musamman, ko kuwa ɗan’uwansa Solomon ba.
11Sai Natan ya ce wa Batsheba, mahaifiyar Solomon, “Ki san cewa Adoniya, ɗan Haggit, ya zama sarki ba tare da sanin ranka yă daɗe, sarkinmu Dawuda ba? 12Yanzu bari in ba ki shawara yadda za ki cece ranki da kuma ran ɗanki Solomon. 13Ki shiga wurin Sarki Dawuda ki ce masa, ‘Ranka yă daɗe sarki, ba ka rantse mini ni baiwarka cewa, “Tabbatacce Solomon ɗanka ne zai zama sarki bayana, yă kuma zauna a kujerar sarautar ba”? To, me ya sa Adoniya ya zama sarki?’ 14Yayinda kike can kina magana da sarki, zan shiga in kuma tabbatar da abin da kika faɗa.”
15Saboda haka Batsheba ta je don tă ga sarki. A yanzu dai sarki ya tsufa, yana nan kuma a cikin ɗakinsa, inda Abishag mutuniya Shunam take masa hidima. 16Batsheba ta rusuna ta kuma durƙusa a gaban sarki.
Sai sarki ya tambaye ta ya ce, “Me kike so?”
17Ta ce masa, “Ranka yă daɗe, kai kanka ka rantse mini ni baiwarka da sunan Ubangiji Allahnka cewa, ‘Solomon ɗanka zai zama sarki bayana, zai kuma zauna a kujerar sarautata.’ 18Amma yanzu Adoniya ya zama sarki, kai kuwa ranka yă daɗe sarki, ba ka san wani abu game da shi ba. 19Ya miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa, ya kuma gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da Abiyatar firist, da Yowab shugaban mayaƙa, amma bai gayyaci Solomon bawanka ba. 20Ranka yă daɗe sarki, idanun dukan Isra’ila suna a kanka, domin su san wa zai zauna a kujerar ranka yă daɗe sarkina, a bayanka. 21In ba haka, bayan an binne ranka yă daɗe sarki, tare da kakanninsa, za a wulaƙance ni da Solomon ɗana, kamar masu laifi.”
22Yayinda take cikin magana tare da sarki, sai annabi Natan ya iso. 23Sai aka faɗa wa sarki, “Ga annabi Natan.” Da Natan ya je gaban sarki, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.
24Natan ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki, ko ka furta cewa Adoniya ne zai zama sarki a bayanka, yă kuma zauna a kujerar sarautarka? 25Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’ 26Amma bai gayyace ni bawanka, da Zadok firist, da Benahiya ɗan Yehohiyada, da kuma bawanka Solomon ba. 27Ranka yă daɗe, sarki, ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fadawanka, cewa ga wanda zai gāje Ranka yă daɗe, sarki ba?”
Dawuda ya naɗa Solomon Sarki
28Sai Dawuda ya ce, “Kira Batsheba tă shiga.” Sai ta zo gaban sarki ta kuma tsaya a gabansa.
29Sai sarki ya yi rantsuwa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya cece ni daga kowace damuwa, 30tabbatacce a yau zan aikata abin da na yi miki rantsuwa da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila; Solomon ɗanki zai zama sarki bayana, kuma shi zai zauna a kan kujerar sarautata a maimakona.”
31Sai Batsheba ta rusuna da fuskarta har ƙasa, ta kuma durƙusa a gaban sarki ta ce, “Bari ran Sarkina Dawuda yă daɗe, har abada!”
32Sarki Dawuda ya ce, “Ku kira mini Zadok firist, annabi Natan, da Benahiya ɗan Yehohiyada.” Da suka zo gaban sarki, 33sai ya ce musu, “Ku ɗauki bayin sarki tare da ku, ku kuma sa ɗana Solomon a kan dokina, ku gangara da shi zuwa Gihon. 34A can ku sa Zadok firist, da annabi Natan su shafe shi sarki a bisa Isra’ila. Ku busa ƙaho, ku kuma yi ihu, kuna cewa, ‘Ran Sarki Solomon yă daɗe!’ 35Sa’an nan ku haura tare da shi, zai kuwa zo yă zauna a kujera sarautata, yă yi mulki a maimakona. Na naɗa shi mai mulki a bisa Isra’ila da Yahuda.”
36Benahiya ɗan Yehohiyada ya amsa wa sarki, ya ce, “Amin! Bari Ubangiji Allah na ranka yă daɗe sarkina, yă tabbatar da haka. 37Kamar yadda Ubangiji ya kasance da ranka yă daɗe, sarki, haka ma bari yă kasance da Solomon, yă kuma mai da kujerar sarautarsa tă fi kujerar sarautar ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, girma!”
38Sai Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa suka gangara, suka sa Solomon a kan dokin Sarki Dawuda, suka raka shi zuwa Gihon. 39Zadok firist ya ɗauki ƙahon mai daga tenti mai tsarki, ya shafe Solomon. Sa’an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka yi ihu, suna cewa “Ran Sarki Solomon yă daɗe!” 40Dukan mutane kuwa suka haura suka bi shi, suna busan sarewa, suna farin ciki sosai, har ƙasa ta girgiza saboda sowa.
41Adoniya tare da dukan baƙin da suke tare da shi kuwa suka ji wannan sa’ad da suke gama bikinsu. Da jin busan ƙaho, sai Yowab ya yi tambaya, ya ce, “Me ya jawo surutu haka a birni?”
42Tun yana cikin magana, sai Yonatan ɗan Abiyatar ya iso. Adoniya ya ce, “Shigo! Ai, mutumin kirki irinka, lalle ka kawo labari mai daɗi ne.”
43Yonatan ya ce wa Adoniya, “A ina! Ranka yă daɗe, Sarkinmu Dawuda ya naɗa Solomon sarki. 44Sarki ya aika shi tare da Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa, suka sa shi a kan dokin sarki, 45Zadok firist kuwa da annabi Natan sun shafe shi sarki a Gihon. Daga can suka haura suna kirari, birni kuwa ta ɓarke da sowa. Surutun da kake ji ke nan. 46Ban da haka ma, Solomon ne sarki yanzu. 47Yanzu haka, fadawa sun zo suna wa ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, sam barka, suna cewa, ‘Bari Allahnka yă sa sunan Solomon yă zama sananne fiye da naka, bari kuma sarautarsa tă fi taka girma!’ Sarki kuwa ya rusuna, ya yi sujada a kan gadonsa 48ya ce, ‘Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bar idanuna suka ga magāji a kan kujerar sarautata a yau.’ ”
49A nan fa, dukan baƙin Adoniya suka taso da rawar jiki suka watse. 50Amma Adoniya, don tsoron Solomon, ya je ya kama ƙahon bagade ya riƙe. 51Sa’ad da aka faɗa wa Solomon cewa, “Adoniya yana tsoron Sarki Solomon, kuma ya manne wa ƙahonin bagade. Yana cewa, ‘Bari Sarki Solomon yă rantse mini a yau cewa ba zai kashe bawansa da takobi ba.’ ”
52Solomon ya amsa ya ce, “In ya nuna kansa mai biyayya, ba gashin kansa da zai fāɗi ƙasa; amma in aka same mugunta a cikinsa, zai mutu.” 53Sai Sarki Solomon ya aiki mutane, suka kuma sauko da shi daga bagade. Adoniya kuwa ya zo, ya rusuna wa Sarki Solomon, sai Solomon ya ce, “Tafi gidanka.”

¿Sabías que…?
La sucesión al trono de David
- Siendo el hijo mayor sobreviviente de David tras la muerte de Amnón y Absalón, Adonías reclamó la sucesión real respaldado por el comandante militar Joab y el sacerdote Abiatar. Sin embargo, David eligió a su hijo menor Salomón, quien contaba con el apoyo del profeta Natán, el sacerdote Sadoc y Benaía.Fuentes: Adonijah · Solomon · el propio texto bíblico
- Montar en la propia mula del rey constituía una proclamación pública decisiva de autoridad real. Por orden expresa de David, Salomón fue llevado al manantial de Gijón, donde Sadoc lo ungió como rey con aceite sagrado del tabernáculo en medio del sonido de cuernos y la aclamación popular.Fuentes: Gihon · Zadok · el propio texto bíblico
- Al enterarse de la coronación pública de Salomón, Adonías huyó aterrorizado y buscó asilo sujetándose a los cuernos del altar de los sacrificios. Salomón le otorgó clemencia condicional, perdonándole la vida siempre que demostrara ser un hombre digno.Fuentes: Adonijah · el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Shunem · Hoy: Sulam · 32.606, 35.334 · versículo 3
- Serpent’s Stone · Hoy: within 100 m of Bir Ayub · 31.767, 35.236 · versículo 9
- Gihon · Hoy: Gihon Spring · 31.773, 35.236 · versículos 33, 38, 44, 45
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 40
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org